Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Zata mayar da martani mai gauni kan yadda ake siyasantar da batun nukiliya a cikin kwamitin gwamnonin cibiyar IAEA

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya jaddada cewa: Idan aka mayar da batun Iran na nukiliya siyasa a taron kwamitin gwamnonin cibiyar IAEA, bai kamata daya bangaren ya sa ran Iran za ta ci gaba da yin aiki da cikakken kamun kai ba tare da mayar da martani ba.

Maimakon haka, Iran za ta gudanar da mu’amalarta da siyasarta daidai da halayensu da manufofinsu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta gidan talabijin na Iran a yammacin jiya Talata, dangane da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan rahoton baya-bayan nan da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafa’el Grossi ya gabatar, wanda ya haifar da cece-kuce game da wani kuduri mai tsauri kan Iran a taron kwamitin gwamnonin da za a yi a mako mai zuwa, Gharibabadi ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran mamba ce ta yarjejeniyar hana kera makamin nukiliya da yaduwarta, kuma tana yin riko da dokokin da yarjejeniyar ta cimma tare da karewa.

Ya kara da cewa: “Iran ta aiwatar da alkawuran da ta dauka tare da sauke nauyin da ya rataya a wuyarta. Ko da yake ya kamata hukumar ta IAEA ta kasance kungiya ce ta fasaha da doka, amma ra’ayoyin siyasa suna yin tasiri kanta.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

2027: Obi zai iya takara ba tare da ni ba — Datti Baba-Ahmed

Datti Baba-Ahmed, wanda ya yi wa Peter Obi, takarar mataimaki a zaɓen 2023, ya ce yana goyon bayan Obi idan yana so ya sake yin takara a 2027, ko da ba tare da shi ba.

Peter Obi da Datti sun tsaya takara tare a 2023 sai dai sun ƙare a na uku.

NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido

Shugaba Bola Tinubu ne ya lashe zaɓen.

Datti, ya ce Obi yana da ’yancin sake tsayawa takara a ƙarƙashin LP.

Ya kuma ce ba dole ne sai Obi ya yi haɗin gwiwa da shi ba.

“Peter Obi mutum ne da nake girmamawa ƙwarai. Yana da damar sake fitowa takara a 2027, ko da ba tare da ni ba,” in ji Datti a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.

Datti, wa ds tsohon Sanata ne, ya ce Najeriya na buƙatar shugabanni masu gaskiya da za su iya kawo ci gaba, ba masu alƙawuran ƙarya ba.

“Muna cikin wani yanayi mai muhimmanci. ’Yan Najeriya na buƙatar aiki ba uzuri ba. Muna buƙatar shugabanni masu cika alƙawari da gyara ƙasa,” in ji shi.

Game da shigar Peter Obi a wata haɗakar siyasa a jam’iyyar ADC, Datti ya ce hakan ba laifi ba ne.

“Haɗin gwiwa a siyasa ba cin amanar jam’iyya ba ne. Hakan al’ada ce a siyasa, inda mutane da jam’iyyu ke haɗuwa don cimma buri ɗaya.

“Ni ma na halarci wasu daga cikin tarukan. Ba wani abu ba ne da ya saɓa wa doka ko tsarin jam’iyya,” in ji shi.

Ya ce wannan haɗin gwiwar na da nufin samar wa ’yan Najeriya zaɓi mai kyau duba da halin da ake ciki.

Game da batun karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, Datti, ya ce kamata ya yi shugabancin ƙasa ya koma Kudu a 2027.

Ya ce wannan ba lissafin siyasa ba ne, amma manufar adalci da haɗin kai a ƙasa mai yawan ƙabilu kamar Najeriya ne.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
  • Tinubu Ya Tattauna da Gwamnonin APC Kafin Muhimmin Taron NEC
  • 2027: Obi zai iya takara ba tare da ni ba — Datti Baba-Ahmed
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Uranium A Cikin Kasarta
  • Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa
  • Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa
  • Kwankwaso  Ne Kaɗai Ɗan Siyasar Da Zai Iya Maye Gurbin Buhari — Jigo A NNPP
  • Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukumar Hisba Ta Jihar Jigawa
  • Gwamna Namadi Ya Jinjinawa Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Bisa Ayyukan Raya Kasa
  • Birgediya Janar Sabahi Fard Ya Jaddada Cewa: Duk Wani Sabon Hari Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Gauni