Cikin kwanaki uku na hutun bikin Dragon Boat na kasar Sin, an samu karuwar tafiye-tafiye zuwa ketare da suka kusa miliyan 5.91. Masu tafiye-tafiye sun karu matuka tun daga Asabar har jiya Litinin, inda aka samu karuwar kaso 2.7 bisa dari kan adadin da aka samu a bara.

Alkaluman da hukumar lura da shige da ficen al’umma ta kasar Sin ta fitar a Talatar nan, sun nuna karuwar baki masu shigowa kasar Sin daga ketare, musamman wadanda suka ci gajiyar manufar nan ta kawar da bukatar biza.

Albarkacin wannan manufa, adadin baki daga ketare da suka shigo kasar Sin yayin ranaku uku na bikin ya kai 231,000, adadin da ya karu da kaso 59.4 bisa dari kan na shekarar bara.

A bana an gudanar da bikin Dragon Boat ne tun daga ranar Asabar 31 ga watan Mayu zuwa jiya Litinin 2 ga watan Yuni. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, da shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Huning, sun gana da shugaban majalisar dattijan kasar Madagascar Richard Ravalomanana.

Yayin ganawar, Zhao Leji ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin kokari tare da Madagascar, don sa kaimi ga raya hadin gwiwa, da sada zumunta a tsakaninsu, da samar da gudummawa ga raya kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamani. Kana yana fatan hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu, za su kara yin mu’amala, da hadin gwiwa da juna, don taimakawa wajen raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Madagascar a dukkan fannoni.

Yayin ganawar tsakanin Wang Huning da Ravalomanana, Wang ya bayyana cewa, Sin da Madagascar hakikanin abokan juna ne, yayin da ake zamanintar da kasashen. Kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, na fatan yin mu’amala tare da majalisar dattijai ta kasar Madagascar, wajen taimakawa raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, Ravalomanana ya bayyana cewa, majalisar dattijan kasar Madagascar, na fatan yin kokari tare da kasar Sin, wajen inganta mu’amala a tsakanin hukumomin kafa dokokin kasashen biyu, don sa kaimi ga raya hadin gwiwar kasashen biyu, a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, da harkokin kananan hukumomi kasar da sauransu. Kana yana fatan kara yin mu’amala da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, a fannin sarrafa harkokin kasa, da kuma sa kaimi ga daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kaddamar Da Bikin BIRTV2025 A Beijing
  • Zan Ci Gaba da Taka Leda A Kano Pillars Duk da Matsayin Da Na Samu — Ahmed Musa
  • Aikin Zirga-Zirgar Jiragen Sama Ta Fasinja Ta Sin Ya Bunkasa Zuwa Sabon Matsayi
  • DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta
  • Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
  • Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
  • Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Libya Ta Tasa Keyar Baƙin Haure Yan Kasar Sudan 700 Zuwa Kasarsu