Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Yi Watsi Da Amfani Da Batun Tsaron Kasa Barkatai
Published: 6th, June 2025 GMT
A yau Alhamis, ma’aikatar ciniki ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci kasar Amurka da ta yi watsi da amfani da batun tsaron kasa barkatai wadda ta mayar da shi mai gamewa gaba daya da kuma wuce gona da iri, kana ta hada kai da dukkan bangarori wajen kiyaye tsarin cinikayya tsakanin sassa daban-daban.
A wani taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai, mai magana da yawun ma’aikatar, He Yongqian, ta bayyana hakan a lokacin da aka bukaci ta tofa albarkacin bakinta game da matakin da Amurka ta dauka na kara haraji kan karafa da holoko da kayayyakin da ake sarrafawa da su wadanda ake kaiwa kasar, daga kashi 25 zuwa 50 cikin dari. Ya ce irin wannan yunkuri na Amurka ba wai yana cutar da wasu da ita kadai ba ne, har ma zai kawo cikas ga sha’anin tafiyar da masana’antu cikin lumana da samar da kayayyaki a duniya.
Lokacin da take tsokaci kan sabbin takunkumai da Amurka ta sanya ga kasar Sin bayan tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da aka yi a Geneva cikin watan Mayu, mai magana da yawun ma’aikatar ta ce, kasar Sin ta sauke hakkokinta, tare da tabbatar da aiki da matsayar da aka cimma a tattaunawar.
Sai dai kuma, duk da haka, Amurka ta kakaba wasu sabbin takunkumai kan kasar Sin, tare da yin watsi da matsayar da aka cimma, kuma ta yi mugun tauye hakkoki da muradun kasar Sin. Ta kara da cewa, kasar Sin tana matukar nuna rashin gamsuwa da kuma adawa da hakan, inda ta bukaci Amurka da ta dakatar lamarin nan take. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Sin ta
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa
Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran.
Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a kasar Iran nan gaba bisa tsarin dokokin kasa da kasa.
Wannan yunkuri yasa an ga bangarorin biyu na Amurka da Isra’ila suna matsa lamba a kan sauran bangarori na duniya, tare da bayyana Shirin na Iran a matsayin mai matukar hadari ga duniya, da nufin samun goyon bayan kasashen duniya kan bakaken manufofisu a kan kasar ta Iran.
Dangane da zargin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan Shirin Iran da kuma neman samoma kansa hujjoji na kaiwa Iran hari, da kuma bayyana cewa harin Amurka ya kawo karshen Shirin Iran na nukiliya, Pezeshkian ya ce, “Da’awar cewa shirinmu na nukiliya ya kawo karshe, batu ne na yaudara.”
“Ilimin nukiliya yana a cikin kwakwalen masananmu ne na kimiyyarmu, ba a cikin wurarenmu ba.” In ji Pezeshkian.
Haka nan kuma shugaban na Iran ya sake nanata matakin kin amincewa da zargin kasarsa da hakoron kera makaman kare dangi, da kuma kara jaddada matsayin kasar na ci gaba da daukar matakan da take yi wajen kara inganta shirinta na makamashin nukiliya domin ayyukan farar hula.
Pezeshkian ya kuma sake nanata shirye-shiryen Iran na yin shawarwarin da ba su ginu a kan haramtawa Iran hakkinta na inganta na tace sanadarin Uranium ba, amma ya ce “duk wata tattaunawa da za a yi a nan gaba dole ne ta dogara a kan batutuwa na masu tabbatar da hakkokin Iran.