Sheikh Naim Qassem Da Aragchi Sun Tabbatar Da Kara Karfin Zumunci Tsakanin Iran Da Lebanon
Published: 4th, June 2025 GMT
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Nain Qasim da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi sun gana a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran siyasa da yankin kudancin Asiya tare da kasar Lebanon.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto aragchi yana cewa dangantaka tsakanin Iran da kungiyar Hizbullah dangane ce wacce ta shafi yankin kudancin Asiya gaba daya.
A nashi bangaren shugaban kungiyar Hizbullah sheikh Naem Kassem ya godewa JMI ta irin tallafin da take bayarwa ga kungiyoyi da kasashen kawancen masu gwagwarmaya a yankin wadanda suka hada da Falasdinawa da Lebanon da sauransu.
Aragchi ya kara da cewa Iran a shirye take ta taimakawa kasar Lebanon a harkokin siyasa tattalin arziki da zamantakewa. Ya kuma yabawa kungiyar Hizbullah kan rawan da take takawa wajen tabbatar da tsaro da kuam zaman lafiya a kasar Lebanon, musamman da HKI wacce take mamaye da wasu yankunan na kasar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Za’ayi tattaunawa ta gaba tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi a Oman
Iran ta ce za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a Muscat, babban birnin kasar Oman.
Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya ce “An shirya zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a birnin Muscat.”
Tun a watan Afrilu, Tehran da Washington ke gudanar da shawarwarin kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
An yi shawarwari guda uku a tsakanin kasashen biyu a birnin Muscat, yayin da sauran biyun suka gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya.
Tehran da Washington sun gudanar da wadannan zagaye biyar na shawarwarin a shiga tsakanin kasar Oman, kan batun maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar 2015, wadda Amurka ta fice daga cikinta a shekarar 2018.
Sai dai shawarwarin na fuskantar cikas sakamakon bukatar da Amurka ta yi na cewa Iran ta daina tace sinadarin Uranium a matsayin wani bangare na sabuwar yarjejeniyar.
Iran dai ta jaddada cewa, ba za ta yi watsi da hakkinta na inganta sinadarin Uranium ba, wanda yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) ta tanada.