Sabon Rikici: An kashe dan shekara 13 da wasu 3 a Filato
Published: 7th, June 2025 GMT
Akalla mutane hudu ne, ciki har da wani matashi dan shekara 13, an ce an harbe su tare da fille kawunansu a ranar Alhamis a yankin Gangaran Kwata da ke karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Mazauna yankin sun ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe biyu na tsakar daren ya haifar da tashin hankali a yankin na Mangu.
Abdullahi Maicibi, shugaban addini a yankin Kwata, ya tabbatarwa da wakilin Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce an dauki gawarwakin wadanda aka kashe zuwa babban masallacin Mangu da ke garin Mangu domin yin sallar jana’iza.
Shagari Madaki, another resident, said apart from the murders, many houses were burned during the incident, explaining that “We don’t know why the attackers invaded our area,” he added.
Wani mazaunin garin Shagari Madaki ya ce baya ga kashe-kashen da aka yi, an kona gidaje da dama a lokacin da lamarin ya faru, yana mai bayanin cewa “ba mu san dalilin da ya sa maharan suka mamaye yankinmu ba.”
A cewar shugaban addinin, wasu mutane dauke da makamai da ake zargin ‘yan kungiyar Mwaghavul ne suka mamaye yankin, inda suka yi ta harbe-harbe inda kashe mutum hudu.
Malamin addinin ya jaddada bukatar jami’an tsaro su dauki kwakkwaran mataki domin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika, yana mai cewa barin wadanda ba gwamnati ba su dauki makami a kan daidaikun mutane zai haifar da rashin bin doka.
Musa Ibrahim, kawun daya daga cikin mamatan, ya bayyana cewa suna tare da dan uwansa ne a lokacin da suka ji karar harbe-harbe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 4 Da Manoma A Katsina
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa gwamnatin Jihar Katsina na ƙoƙarin sasantawa da wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar.
Wasu daga cikin ‘yan bindigar da ke Jibia, Batsari da DanMusa sun amince da zaman lafiya tare da miƙa makamansu.
Sai dai wannan hari na baya-bayan nan ya sa al’umma sun fara shakkar ko zaman lafiyar zai ɗore.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp