Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta ce kasar ta samu ingantuwa a banagren amfani da ruwa a shekarar 2024.

Sanarwar da ma’aikatar kan fitar kan albarkatun ruwa a duk shekara, ta ce a bara, ruwan da kasar ta yi amfani da shi da na kwatankwacin yuan 10,000 ko dala 1,391.5 na alkaluman GDP ya ragu da kaso 4.

4 bisa dari. Haka kuma idan aka kwatanta da yuan 10,000 na darajar bangaren masana’antu, adadin ya ragu da kaso 5.3 bisa dari.

A cewar sanarwar, saukar ruwa da albarkatun ruwa sun wuce matsakaicin matakin na shekaru da dama. Matsakaicin adadin ruwan da ya zuba a kasar a shekarar 2024 shi ne milimita 717.7, wanda ya haura na shekarun baya da kaso 11.4 cikin dari. Jimilar albarkatun ruwa kuma ya tsaya kan kubik mita 3.11, karuwar kaso 12.7 cikin dari idan aka kwatanta da na matsakaicin na shekarun baya. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: albarkatun ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa da tsaki a Jihar Kano.

Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71

A cewarsam Tinubu ya yi watsi da halin da yankin arewacin ƙasar ke ciki wajen gina Kudancin Najeriya da kuma samar musu da kayan more rayuwa.

“Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan,” in ji Kwankwaso.

Kwankwaso wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023, ya zargi jam’iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Nijeriya.

Ya ce: “Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi,” in ji Kwankwaso.

Ya ce wannan ya sa ake fama da rashin tsaro da talauci da sauransu.

Kwankwaso ya ce yawancin hanyoyi da ke Arewacin suna cikin mawuyacin hali, wasu ma sun lalace, yayin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware maƙudan kuɗaɗe wa ɓangaren ayyukan more rayuwa a Kudancin ƙasar.

Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sauya alƙibla domin tafiya da kowa da kuma tabbatar da cewa an raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin ci gaban dukkan sassan ƙasar.

“Yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnati ta kawo sauyi, domin mu san cewa ba gwamnati ce kaɗai ta wani ɓangare guda ba,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso
  • Gwamantin Kasar Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga BirninSiweida Na Kasar Saboda Ci Gaba Da Bullar Rikici
  • Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
  • Zan Ci Gaba da Taka Leda A Kano Pillars Duk da Matsayin Da Na Samu — Ahmed Musa
  • Aikin Zirga-Zirgar Jiragen Sama Ta Fasinja Ta Sin Ya Bunkasa Zuwa Sabon Matsayi
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Uranium A Cikin Kasarta
  • Eritrea ta gargadi Habasha game da yunkurin kafa tashar jiragen ruwa a cikin yankinta
  • Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana
  • Shirin Ba Da Horo A Kasar Sin Ya Taimaka Wa Inganta Masana’antar Gyadar Senegal
  • Magudnar Ruwa Ta Yi Ajalin Rayuka Hudu A Zangon Kaya, Kano