Ma’aikatar Harkokin Waje: Kasar Sin Ta Kasance Gwarzuwa Wajen Samar Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
Published: 6th, June 2025 GMT
Yau ce ranar muhalli ta duniya. An yi sharhi a baya cewa, a cikin ’yan shekarun nan, kasar Sin ta jagoranci ayyukan samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a duniya, da samun gagaruman nasarori a fannin raya makamashin da ake sabuntawa da sauran fannoni, da taimaka wa sauran kasashe masu tasowa wajen aiwatar da ayyukan sauyin makamashi.
Yayin da yake amsa tambayoyi a wurin taron manema labaru da ya gudana a yau, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance mai fafutukar neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a ko da yaushe, kana mai taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi ta wannan fuskar a duniya, inda aka mayar da makomar dan’adam ta bai-daya.
Kasar Sin tana mai da hankali kan ba da fifiko ga kyautata muhallin halittu da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, kuma tana son ci gaba da gudanar da ayyuka na bai-daya amma kuma ta bambanta hakkokin hakan tare da dukkan bangarori a matsayin “karfin da zai ba da dama” don inganta gina duniya mai tsabta, kyakkyawa da za ta zama mai dorewa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ci gaba ba tare da
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma October 30, 2025
Daga Birnin Sin Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC October 30, 2025
Daga Birnin Sin Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya October 30, 2025