Amurka Ta Sake Dorawa Iran Karin Takunkuman Tattalin Arziki Duk Tare Da Tattaunawa A Tsakaninsu
Published: 7th, June 2025 GMT
Gwamnatin kasar Amurka ta kara yawan takunkuman tattalin arzikin da take dorawa JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon takunkuman sun shafi mutane 10 da kuma kamfanoni 27. Wadansu daga cikin kamfanonin suna kasar hadaddiyar daular Larabawa wasu kuma a Hong kong.
Ofichin Baitul malin Amurka ya bayyana cewa Kamfanin Ace Petrochem FZE da kuma Moderate General Trading LLC duk suna da rijister a UAE kuma kwace dukkan kadarorinsu da suke Amurka saboda wadannan takunkuman.
Labarin ya kara da cewa wadannan kamfanoni suna da dangantaka da kamfanin OFAC na kasar Iran, kamfanin tankunan jigilar man fetur.
Iran da Amurka dai sun gudanar da zagaye na 5 na tattaunawa a tsakanin kasashen biyu. Tun bayan ficewa Amurka daga yarjeniyar JCPOA a shekara ta 2018 ne Amurka take dorawa Iran takunkuman tattalin arziki.
A halin yanzu dai sabani ya shiga tsakanin kasashen biyu bayan da Amurka ta bukaci Iran ta kawo karshen tache Uranium a cikin gida wanda Iran tace ba zai yu ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
“Ana kiransa da suna dokar binciken tntanet ta tsoratarwa, wadda kasashen da suka ci gaba da dama suka dade da yin watsi da ita. A karni na 21, ba za a iya tunanin cewa gwamnatin Nijeriya za ta tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda shi ne ginshikin mulkin dimokuradiyya.”
Atiku ya ce duk wata doka da ke take ‘yancin ‘yan kasa na yin tsokaci mai muhimmanci game da shugabanninsu ko a hanyoyin sadarwar zamani ko ta hanyar magana ba dimokuradiyya ba ce kuma kai tsaye take hakkokin Dan’adam ne.
“A cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara daukan matakan da ke janyo kuncin tattalin arziki da yunwa da bakin ciki ga mutanen Nijeriya, mun shaida zanga-zanga da koke-koke daga ‘yan kasa da ba za su iya daukar mulkin rashin gaskiya ba. Duk da haka, maimakon sauraron ‘yan kasa sai gwamnatin ta zabi hanyar amfani da karfin hukumo da tsoratarwa wadda ta juya lamarin zuwa wani abu daban.
“Lallai abin bakin ciki ne na ganin ana take hakkin ‘yan kasa da kundin tsarin mulki ya tabbatar a lokacin da ya kamata dimokuradiyyarmu ta kasance mai bin tsari. Dole ne mu tunatar da gwamnatin Tinubu cewa babu gwamnati a lokacin da ta kasa kare ‘yancin ‘yan kasarta, komai karfinta kuwa. Yin haka abun ta da hankali ne kuma hakan yana nuna gazawar gwamnati a fili.”
Atiku ya ce tabbas gwamnati na da alhakin kula da doka da oda, babu ingantacciyar gwamnati da za ta harbi masu zanga-zangar lumana da harsashi mai rai ko ta boye a bayan dokoki tana musguna wa ‘yan kasa.
Ya ce rashin kulawar gwamnati Tinubu ga dokar kasa da kuma ci gaba da kin bin umarnin kotu sun zama shahararrun siffofinta mafiya suna a kasar nan a halin yanzu.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kara da cewa tun farkon wannan gwamnati, kungiyar kare hakkin Dan’ada ta Amnesty ta soke wannan gwamnatin da take hakkin Dan’adam.
Ya ce haka ma wasu kungiyoyi masu muhimmanci kamar irinsu kungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya da kungiyar kare ajandar kafafen yada labarai sun yi korafi kan cin zarafin ‘yan jarida da ‘yan kasa ta hannun jami’an gwamnati.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA