Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka
Published: 7th, June 2025 GMT
’Yan Sanda sun kama wani mutum mai suna Mohammed Sani mai shekara 31 da duniya, bisa zargin dukan matarsa Hauwa mai ɗauke da juna biyu, wanda ya zama ajalinta.
Lamarin ya faru ne a gidansu da ke unguwar Banin Hashim da ke Minna, a Jihar Neja.
Sojojin Isra’ila sun kashe mutum 13 a wajen rabon tallafi a Gaza 2027: Makomar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na janyo cece-kuceHauwa mai shekara 24 a duniya wadda ke ɗauke da cikin wata tara, an same ta a mace a ɗakinsu kwance cikin jini.
Rundunar ’yan sandan ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar 3 ga watan Yuni, 2025.
Jami’an ‘yan sanda daga sashen A Division a Minna sun garzaya gidan.
Sun garzaya da Hauwa asibitin gwamnati da ke Minna, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Haka kuma, likitoci sun tabbatar cewa tana da juna biyu.
Maƙwabtansu sun shaida wa ‘yan sanda cewa ma’auratan suna yawan samun saɓani, kuma suna zargin mijin ne ya yi wa matar dukan tsiya.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce an kama Mohammed Sani kuma an miƙa shi zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Minna.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA