2025-06-05@05:29:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 512
«Kayan miya»:
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata al’ada da ta zama gama gari a tsakanin matasa, ita ce yankewa da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan bukukuwan Sallah. A da, ana da wurare na musamman da ake yin irin wannan abu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa NAJERIYA A YAU:...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas. Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar. Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Fubara, ya samu saɓani...
ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu a Karamar Hukumar Kaduna Sout Shirin Dawo da Yara Makaranta na Gwamnatin Jihar Kaduna Mai suna ROOSC ya kaddamar da rabon kayan koyon karatu ga dalibai a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Makarantar Firamare ta LEA da ke...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda...
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in...
Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata. Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya...
Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa...
Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki. Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa....
Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni. Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau. Malam Gusau ya...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa,...
Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai...
Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah. Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon...
Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin...
A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin...
Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup...
“Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da...
A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun...
A jawabinsa a wajen rabbata hannun yarjejeniyar, jami’in shirin na jihar ta Gwambe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya danganta wannan aiki a matsayin wani babban ci gaba a jihar. Ya kara da cewa, aikin ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, akwai kuma batun zuba hannun jari ga ci gaban kiwon su kansu dabbobin. A...
Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin abinci ga Falasdinawa da ke fama da yunwa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama laifin yaki. “Muna ganin abinci dake jibge a kan iyakoki kuma ba a ba da izinin...
Wani mutum mai suna Adamu Muhammed Tenimu ya suma bayan da samu labarin cewa matarsa ta haifi jarirai ’yan uku a asibitin koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lokoja babban birnin Jihar Kogi ranar Juma’a. Shaidu sun ce, mutumin da ya ji cewa matarsa ta haifi ‘ya’ya mata uku, sai ya faɗi ya suma a harabar...
MDD ta yi gargadi akan yunuwar da mutanen Gaza suke fama da ita, sannan ta kara da cewa: Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji, kuma rabin cibiyoyin kiwon lafiya na yankin sun daina aiki saboda rashin isar da kayan agaji daga waje.” Ofishin MDD wanda yake kula da ayyukan agaji ne ya yi wannan...
A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan...
PUNCH Metro ta tuna cewa a kwanakin baya jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a cikin hadaka a Kananan Hukumomin Ilorin da Ifelodun na jihar. Oyewale ya ce an tare wadanda ake zargin ne a madatsar ruwa ta Asa da yankin Jami’ar Al-Hikmah da...
Wasu mutum 12 ’yan gida daya da almajirai sama da 50 na cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwan da ta afka wa yankin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a ranar Laraba. Ambaliyar, wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a daren na...
Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya A yayin ganawarsa da sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil ya sanar da cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da makamashin...
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau shekara biyu ke nan cif tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na 16 tun bayan samun ‘yancin kai. Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya fara yi yayin jawabin karbar mulkin shi ne sanar da...
A ci gaba da tafka laifukan yakin da HKI take yi a Gaza,Fiye da Falasdinawa 60 ne su ka yi shahada a jiya Laraba. A wani harin da sojojin mamayar su ka kai a yankin Jabaliya, Falasdinawa 5 sun yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa su ka jikkata. Wani jirgin sama maras matuki...
Daya daga cikin maniyyata Aikin Hajjin bana daga jihar Filato mai suna Hajiya Zainab ta mayar wa da wani dan kasar Rasha kudinsa da ta tsinta a birnin Makka na kasar Saudiyya, har kimanin Naira miliyan takwas da dubu 200. Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a...
Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin...
Dakarun sojojin Najeriya sun dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno, inda suka kashe wasu da dama daga cikin maharan. Majiyar leken asirin hedikwatar sojan Najeriya ta tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:35 na wayewar safiyar...
Gwamnatin kasar Ireland ta yi doka a jiya Talata wacce ta hana a shigar da duk wasu kaya da aka kera a matsugunan ‘yan share wuri zauna da a karkashin dokokin kasa da kasa ake daukarsu a matsayin haramtattu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Ireland ya fada wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa;...
Sun kara da cewa, kasashen Afirka za su kafe kai da fata wajen mutunta ka’idar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan duk kokarin da kasar Sin ta yi na kare ikon ’yancinta da cimma burin sake hadewar kasar, da yin adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana suka ce,...
Tabbas a halin yanzu, wasu kasashe ba su ba da’a muhimmanci ba, kana suna ta daukar matakan kashin kai yadda suka ga dama, lamarin da ya sa al’amuran kasa da kasa suka shiga rudani. Dangane da wannan batu, dole ne Sin da kasashen Afirka masu da’a su karfafa hadin kai, su yi adawa da...
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa,...
Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu. An...
’Yan sanda sun tsare wata matar aure kan zargin ta da kashe kishiyarta a Ƙaramar Hukumar Daura da ke Jihar Katsina. Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa matar ta yi wa uwargidarta kisan gilla ne bayan wata hatsaniya da aka samu a tsakaninsu, wanda ya ƙazance...
Rundunar ‘yansanda ta fara gudanar da bincike kan fashewar wani abu a mashigar babban birnin tarayya Abuja a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya a ranar Litinin. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu rahoton kiran gaggawa a ranar 26 ga...

Shugaban Kasar Kenya: FOCAC Ya Samar Da Damammaki Ga Sin Da Afirka Wajen Inganta Hadin Kansu Da Samun Moriya Tare
Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya ziyarci kasar Sin daga ran 22 zuwa 26 ga watan Afrilun da ya gabata, bisa gayyatar da takwaransa na Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin ziyararsa, shugabannin biyu sun kai ga matsaya daya kan daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa hulda mai makoma ta bai daya a...
Ya ce: “Ya kamata ku nazarci Shugaban Ƙasa sosai. Za ku iya faɗin ra’ayoyin ku; zai saurare ku, amma a ƙarshe shawarar da zai yanke tasa ce. Ina ganin ya dace mu gane hakan.” Yayin da yake bayani kan taken taron, ministan ya ce Shugaba Tinubu na da cikakkiyar niyya wajen aiwatar da Shirin...
Kwamishinan ‘yansanda na jihar, CP Bello Shehu, ya ja hankalin al’umma da su guji tashin hankali a cikin gida, yana mai jaddada muhimmancin neman hanyoyin zaman lafiya da bin doka wajen warware matsaloli. Ya gargaɗi jama’a da kada su ɗauki doka a hannunsu domin hakan yana ƙara taɓarɓarewa da tauye adalci. Daga kanmu, magana...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikn Na’im Kassim ya bayyana cewa; Idan har gwamnatin kasar ta gajiya wajen yin abinda ya rataya a wuyanta na aiki da tsagaita wutar yaki, to gwgawarmaya tana da wata hanyar da za ta yi aiki da ita akan ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da...
Adadin “nau’i uku na manyan kamfanoni 500” da suka halarci bikin baje kolin a bana ya kai 114, wanda ya kai kashi 55.6 bisa dari. Daga cikin su, akwai kamfanoni 61 dake cikin manyan kamfanoni 500 na duniya, adadin da ya karu da kashi 74.3 bisa dari kan na baje kolin da ya gabata. (Bello...
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an yi garkuwa da Ilya ne daga kauyen Gatawa tare da mahaifinsa. Iliya da mahaifinsa dukkansu daga karamar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto. An yi garkuwa da su ne a cikin watan Afrilu, yayin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyensu, suna ta harbe-harbe, inda daga nan ne ‘yan...
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa bai wa ’yan Arewa mutum 12 manyan muƙamai a hukumomin gwamnati. Ya ce wannan matakin ya gyara rashin daidaito da ake gani a naɗin muƙaman da shugaban ya yi a baya, wanda ya janyo damuwa a...
Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki. Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da...
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda...
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe. Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da...