Sin Ta Amince Da Bukatar Fitar Da Wasu Nau’o’in Ma’adinai Na “Rare Earth”
Published: 8th, June 2025 GMT
Ma’aikatar cinikayya ta Sin, ta ce kasar ta amince da bukatar samar da lasisin rika fitar da wasu nau’o’in ma’adinai na “rare earth”, da abubuwan da ake sarrafawa da su zuwa ketare, duba da karin bukatar su da masana’antun sarrafa mutum-mutumin inji, da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi ke yi.
Kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ya ce abubuwan da ake sarrafawa da ma’adinan “rare earth”, na da amfani a sassa biyu, wato ko dai na ayyukan soji, ko na amfani a abubuwan bukatu na fararen hula, don haka kayyade fitar da su ya dace da matakan da aka amince da su tsakanin sassan kasa da kasa.
Kazalika, jami’in ya jaddada cewa, kayyadewar na da nufin kyautata matakan tsaron kasa da moriyarta, da sauke nauyin dake wuyan kasar a matakin kasa da kasa, da dakile bazuwar makamai, daidai da manufar Sin ta wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya.
Ya ce, Sin za ta ci gaba da karfafa lura da yadda ake kiyaye neman izni a fannin, kuma a shirye take ta inganta tattaunawa, da shawarwari kan kayyade fitar da ma’adinan tare da kasashe masu ruwa da tsaki, ta yadda za a wanzar da kiyaye bin ka’idojin cinikayya a fannin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom
Ya ce ya dinga ƙorafi ne domin gwamnatin Buhari ba ta ɗauki matakin da ya dace ba game da kashe-kashen da ake yi a Benuwe.
“Ba zan iya zama na yi shiru ina ci gaba da binne mutane ba. Dole ne na faɗi gaskiya,” in ji shi.
“Amma ban tsaya a magana kawai ba, gwamnatina ta kawo hanyoyin magance matsalar da muka ga za su taimaka.”
Ortom ya ƙara da cewa da gwamnatin Buhari ta karɓi shawararsa kuma ta yi aiki da ita, da matsalar tsaro a Benuwe ta ƙare.
Ya ce ya sha kokawa a lokacin, kuma shirye-shiryen da gwamnati ta kawo kamar Ruga ba su da amfani.
Ya ce ba wai rikici ne tsakanin makiyaya da manoma kawai ba, wasu daga cikin makiyaya suna kai wa ƙauyuka hari, suna kashe mutane, lalata gonaki, yi wa mata fyaɗe da aikata wasu laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp