Shugaban Kasar Iran Ya Tattauna Ta Wayar Tarko Da Tokwaransa Na Masar Da Saudiya
Published: 5th, June 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiyan ya zanta ta wayar tarko tare da shugaban kasar Masar abdulfatta Assisi, inda suka taya juna murnar tahowar sallar Babba. Shugaban ya bayyana cewa kasar Iran tana da tsari ta makobta farko, don haka ne take, kara kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma musamman kasar ta Masar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a wata wayar tarho ta daban shugaban ya zanta da Yarima mai jiran gadon sarautan saudiya kuma Firay ministan kasar Muhammad bin Salman inda ya taya shi murnar zagayowar ranar Sallah babba sannan suka yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu. Duk tare da bambancin ra’ayin da kasashen biyu suke da shi dangane da yadda za’a warware matsalar falasdinawa kasashen biyu sun bukaci a kawo karshen kissan kiyashi a gaza a kuma isar da kayakin agaji da gaggawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta yi matukar Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kasar Iran, tare da jefa bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar kasar, dake karkashin kulawar hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA a takaice.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, lokacin da yake tsokaci kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyi uku na nukiliyar kasar Iran. Jami’in ya ce matakin Amurka ya yi matukar keta makasudi, da ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa, ya kuma ruruta yanayin rashin tabbas da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Daga nan sai jami’in ya ce Sin na kira ga sassa masu ruwa da tsaki a tashin hankalin dake wakana, musamman ma Isra’ila, da su gaggauta cimma matsayar dakatar da bude wuta, tare da tabbatar da tsaron rayukan fararen hula, da fara tattaunawa da shawarwari. Ya ce Sin a shirye take, ta yi aiki da sauran kasashe wajen aiwatar da matakan tabbatar da adalci, da aiki tukuru wajen dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp