Sin Na Kokarin Gina Yanayin Zaman Lafiya Da Hadin Gwiwa Da Kawance A Tekun Kudancin Kasar
Published: 8th, June 2025 GMT
Wani rahoto na gungun kwararru da aka fitar a Lahadin nan, ya nuna yadda kasar Sin ke ta kokarin samar da kyakkyawan yanayin zaman lafiya, da kawance, da hadin gwiwa a yankunan tekun kudancin kasar.
Rahoton na kwararrun cibiyar Xinhua, mai alaka da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua, na da lakabin “Mayar da tekun kudancin Sin wuri mai cike da zaman lafiya, kawance da hadin gwiwa: matakan da Sin ke dauka”, ya ce har kullum Sin na nacewa matakan wanzar da zaman lafiya, da daidaito a yankunan tekun kudancin kasar, kuma nasarar hakan na da alaka da matakan hadin gwiwa da ake aiwatarwa tsakanin Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN.
Rahoton ya kara da cewa, ta hanyar zurfafa amincewa da juna, da hadin gwiwa mai game da dukkanin sassan siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, wannan hadaka ta samar da wani yanayi na cimma moriya mai dorewa ta bai daya. Sakamakon hakan, Sin ta zamo karfi abun dogaro dake wanzar da zaman lafiya da daidaito a shiyyarta, yayin da take ta ingiza hadin gwiwa da ci gaban yankin tekun kudancin kasar.
Har ila yau, Sin ta yi aiki tukuru wajen gina zaman lafiyar shiyya, ta hanyar amincewa da juna ta fuskar siyasa, da bunkasa cin moriyar tattalin arziki na bai daya, domin tabbatar da walwala a shiyyarta, da inganta dinkewar al’ummu, ta yadda za a cimma makomar bai daya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tekun kudancin kasar da hadin gwiwa zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
A ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi a kasar labanon a jiya ma ta kai hari a kudancin kasar kuma ta yi sanadiyar mutuwar mauta 4 tare da jikkata wasu guda 3,
Isra’ila ta kai hari da jirgin sama mara matuki kan wata mota a kauyen kafr rumman , kana kuma ta sake kai wani harin a garin kafr sir kamar yadda rahotanni suka bayyana, kuma wadannan hare haren suna zuwa ne kwanaki 3 bayan da sojojin israila suka kai samame ta kasa a kudancin labanon a yankin Nabatiya inda suka kai hari a jiya,
A ranar jumaa da ta gabata ne shugaban kasar ta labanon joseph Aun ya nuna damuwarsa game da ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Isra’ila ke yi, inda yayi tir da tel aviv game da irin mataken da take dauka na karya yarjejeniyar.
A yan kwanankin nan sakatare janar din kungiyar hizbullah na kasar labanon shaikh Naim Qassem ya jaddada cewa tsayin daka ne karfin labanon, don haka Amurka na matsin lamba ne don ganin an danneta an tauye mata yanci da raunata ta don biyan muradun gwamnati.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci