Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta
Published: 8th, June 2025 GMT
Ministan Bunƙasa Harkokin Ƙarafa, Shuaibu Abubakar Audu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na samun ci gaba wajen farfaɗo da tsohon kamfanin ƙarafa na Ajaokuta da ke Jihar Kogi.
Ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na Jihar Kogi a garinsu Ogbonicha da ke Ƙaramar Hukumar Ofu.
Ministan, ya ce Gwamnatin Tarayya ta riga ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanonin da za su samar da kayan aikinkamfanin.
Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙara neman masu saka hannun jari daga ƙasar China domin su zuba jari a kamfanin.
“Muna yin aiki babba. Mun fara tafiya, kuma muna da tabbacin cewa za mu dawo da aikin Ajaokuta cikin sauri,” in ji Audu.
Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu saboda tsare-tsarensa na gyara da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan ta hanyar inganta harkar sarrafa ƙarafa.
Ya ce Shugaban Ƙasa na ƙoƙarin warware matsalolin da ke addabar ƙasar nan da kuma inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
Audu, ya ce shirin “Sabunta Fata” da Shugaban Ƙasa ke jagoranta ya riga ya fara haifar da ɗa mai ido.
Ya bayyana saukar farashin wasu kayan abinci a matsayin misali.
Haka kuma ya bayyana cewa kuɗin da jihohi ke samu daga Asusun Gwamnatin Tarayya (FAAC) sun ƙaru, lamarin da ya taimaka wa Jihar Kogi.
A nasa jawabin, Sakataren APC na Jihar Kogi, Joshua Onoja, ya yaba wa Ministan bisa shirya taron, sannan ya tabbatar da cikakken goyon bayan jam’iyyar wajen sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar daga sassa daban-daban na Jihar Kogi, ciki har da shugabannin ƙananan hukumomi, ’yan majalisa na yanzu da na baya, ƙungioyi da sauransu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Kamfanin Ƙarafa Gwamnatin Tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyya
Jagororin jam’iyyun adawa na Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman yin rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita don tunkarar Jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
NNCG ta riga ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar Zaɓe mai zaman kanta INEC a hukumance don babban zaɓe na gaba.
Jami’an tsaro sun ƙwato makamai da kama mutane 398 a Kaduna Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa IbomTakardar wadda suka aika zuwa ga shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, wanda shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa tare a ranar Juma’a 20 ga Yunin.
A takardar an rubuta cewa, “muna neman INEC ta amince da buƙatarmu ta yi wa ƙungiyarmu ta All Democratic Alliance (ADA) ta zama jam’iyyar siyasa.”
Ta ƙara da cewa, taken jam’iyyar dai shi ne ‘Adalci ga kowa’ sannan masara ce tambarinta.