NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suka Fara Bacewa Yayin Bukukuwan Sallah
Published: 6th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin.
Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a yanzu matasa sukayi watsi da su wadanda kuma na da muhimmanci yayin bukukuwan sallah a da can baya wanda kuma suke ganin ba a yin su a yanzu.
Ko wadanne irin al’adu kenan na bukuwan sallah da dattawa ke ganin anyi watsi dasu.
NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin SallahShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda aladun bukukuwan Sallah ke canzawa a wannan zamani.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya.
Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya.
Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriya ta taso daga mataki na 8 zuwa na 6 a batun ta’addanci a duniya.
Kazalika a kwanakin nan wani hari da aka kai a wasu yankunan jihar Binuwe yayi sanadiyyar halakar mutane da dama, wadda hakan ya jawo cece ku ce da ya kai har wasu na kiran mutane su tashi don kare kan su.
Irin wannan kira dai an dade ana yi, sai dai gwamnati na ganin ba daidai ne mutane su kare kan su daga hare haren ‘yan ta’adda ba.
NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Ganyayyaki Ke Yi Wa ‘Yan Najeriya Wahala DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon LafiyaShirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan shin ko kare kai daga hare haren ‘yan ta’adda zai kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya?
Domin sauke shirin, latsa nan