2025-07-25@15:31:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4825
«da ya lashe»:
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, ya karɓi ’yan APC zuwa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano. Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta shafinsa na X, inda ya ce waɗanda suka sauya sheƙar ’yan jam’iyyar APC ne. An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo An kashe mata da yara a sabon harin Filato “Jiya rana ce mai muhimmanci,” in ji shi. “Na karɓi dubban mutane da suka bar jam’iyyar APC suka dawo NNPP.” Ya ce taron ya gudana ne a gidansa da ke Kano, inda ya yi wa sabbin mambobin maraba da kuma alƙawarin adalci da haɗin kai a cikin jam’iyyar. An wallafa hotunan taron a shafukan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Juma’a wasu ’yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka uku na Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie a garin Arondizogu, a Ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a Jihar Imo, inda suka kashe aƙalla mutane bakwai. An samu rahoton cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sun yi ta harbin mutanen yankin a ƙauyukan Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama. An kashe mata da yara a sabon harin Filato Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Waɗanda harin ya rutsa da su, masu shaguna ne da kwastomominsu da kuma masu wucewa. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa majiyarr PUNCH cewa, waɗanda lamarin ya...
Sai dai Sanatoci sun yi watsi da bayanin, inda suka zargi Ojulari da yin watsi da Majalisar. Kwamitin yana binciken tambayoyin tantancewa daga shekarar 2017 zuwa 2023, wanda ya nuna sabanin da ya kai Naira tiriliyan 210, ciki har da bashin da ba a tabbatar da shi ba na Naira tiriliyan 103. ‘Yan majalisar sun firgita cewa Naira tiriliyan 3 zuwa 5 ne kawai aka rubuta a cikin asusun ribar da kamfanin ya samu a cikin shekaru shida. “Wannan gayyatar ba tilas bace,” in ji Wadada. Ya kara da cewa kwamitin ba yana zargin hukumar ta NNPC da laifin sata bane amma ya jaddada cewa girman sabanin ya bukaci a yi karin haske kai tsaye. Ya bayyana rashin bayyanar Ojulari...
Aƙalla mutum 14; ciki har da mata da ƙananan yara ƙanana ne, suka rasu a wani sabon hari da aka kai a Jihar Filato. Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a Gundumar Mangor da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos. Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu Waɗanda aka kashe suna kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako-mako da ke garin Bokkos, lokacin da wasu ’yan bindiga suka buɗe musu wuta. Wannan hari na zuwa ne wata guda bayan wani hari da aka kai wa wasu ‘yan ɗaurin aure daga Zariya a Jihar Filato, inda aka kashe su. Ƙungiyar Bokkos Cultural Development Forum (BCDF), ta tabbatar da faruwar...
Koda ya ke dai, a lokacin ‘yansanda sun yi nisa ban gudanar bincike, amma babu wanda suka iya kamawa, kuma ba a kara shigar da wata sabuwar kara a gaban kotu ba, duk tsawon wadannan shekarun. Wannan bukatar da Muyiwa ya biro da ita, tamkar bude wani sabon babi ne, kan batun hallaka manyan mutane a kasar, wadda za a iya cewa, tun daga 1999, har zuwa yau, amma shiru ake ji, kan daukar wani kwakwaran mataki. A wani taro a kwanan baya, babban Lauya SAN Cif Kanu Agabi, ya bijiro da zargin yadda ake gaza hukunta masu aikata manyan laifuka a kasar, inda kuma ake samun dogon jan kafa, kan shari’ar da ta shafi, marasa karfi a kasar. Wannan...
“Sauran su ne Lawan Haruna, Opurum Patrick, Agbo James da Georgewill Onwubiko da sauransu. “Shugaban PSC ya ce su tuna cewa su abokai ne ga kowa, kuma ya kamata a kowane lokaci su yi daidai da abin da ‘yan Nijeriya ke bukata. Ya kuma ba su tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yin iya kokarinta don ganin an inganta yanayin aikinsu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa. Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya. Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi da kashe yara 2 a Bauchi Marigayin, wanda shi ne Sarkin Gusau na 16, ya ɗare kan karaga ne a shekara ta 2015, bayan rasuwar mahaifinsa. Gogaggen ma’aikacin gwamnati, Dr Ibrahim ya taɓa zama Babban Sakatare a tsohuwar jihar Sakkwato da ma jihar Zamfara. Ya yi mulkin ne na tsawon shekara 10 da ’yan watanni kafin rasuwar tasa. Da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin Gwamna...
Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon hawa gwamnatin APC ake yinsa.” Kwankwaso ya kara da cewa ana gudanar da manyan ayyuka a Kudu cikin hanzari, amma an bar ayyuka masu mahimmanci a Arewa babu kulawa. “Muna jin ana gina titi daga Kudu zuwa Gabas. Muna maraba da ci gaba a ko’ina a Nijeriya. Amma gwamnati tana ɗaukar duk arzikin ƙasa ta zuba a ɓangare ɗaya kaɗai, ba ta yin aiki da...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Aref ya jaddada cewa: Dole ne a kawo karshen kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankin Zirin Gaza cikin gaggawa ta hanyar daukar matakai na zahiri da kuma dauri daga kasashen duniya. Aref ya rubuta a shafinsa na X a jiya Alhamis cewa: “Mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba saboda yunwa sakamakon hana isar da abinci ga al’ummar Gaza da aka zalunta ya kasance tare da yin shiru na kunya daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.” Ya kara da cewa: “Dole...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Babu shakka Iran za ta ci gaba da inganta sinadarn Uranium Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a jiya Alhamis dangane da tattaunawar da Iran za ta yi da kungiyar kasashen Turai da za a yi a yau Juma’a a birnin Istanbul na Turkiyya cewa; Za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a cikin kasar Iran, kuma kasar ba za ta yi watsi da wannan hakkin na al’ummar Iran ba. A cikin bayanin da ya yi a gefen ziyarar da ya kai ga iyalan shahidan Laftanar Janar Baqiri, Araqchi ya kara da cewa; Ko da yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da shirinta...
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su. Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci. Kakakin Rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya shaida wa manema labarai haka a Bauchi ranar Alhamis. NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso Wakil Ya bayyana cewa an samu rahoton faruwar lamarin ne a ranar 22 ga watan Yulin 2025, da misalin karfe 3:00 na rana. Ya...
Ya ce, nan da shekarar 2030 za a bukaci hekta miliyan 300 domin samar da bukatar abinci. Don haka ne ya ce taken taron ranar yaki da kwararowar hamada na 2025 na da matukar tasiri domin tabbatar da daukan matakan da suka dace wajen kiyaye hamada da gurbacewar muhalli. A cewarsa, yunkurin zai tunkari manyan kalubale kamar matsalar tattalin arziki da karancin abinci, karancin ruwa, da sauyin yanayi. Lawal ya jaddada cewa cimma muradun ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya ba zai yuwu ba idan ba tare da kare muhalli da kuma kula da filaye da albarkatun kasa ba. Ya kara da cewa gwamnati na ba da fifiko ga al’amuran muhalli kuma ta samar da cibiyoyi, manufofi, tsare-tsaren ayyuka,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati. Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala. NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan irin damar da masu yi wa kasa hidima suke da ita a garuruwan...
Kashe- Kashen 2025 Ya Fi Na 2024 Alkaluman bincike sun bayyana cewar ‘yan ta’adda sun dauki rayukan mutane a rabin wannan shekarar fiye da na shekarar 2024 da ta gabata kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yancin Dan- Adam ta kasa ta bayyana a wannan watan. Kamar yadda alkaluman suka nuna, akalla mutane 2, 266 ne suka bakunci lahira a hannun ‘yan ta’adda a rabin shekarar 2025, idan aka kwatanta da mutane 1, 083 a rabin farko na shekarar 2024 da kuma mutane 2, 194 a bakidaya shekarar. Rundunar sojojin Nijeriya na fafatawar yaki da mayakan Boko- Haram da sauran ‘yan ta’adda a Arewa Maso- Gabas, ta’addanci da garkuwa da mutane a Arewa Maso- Yamma, hare- haren makiyaya da manoma...
Kasashen Iran da Bangaladesh sun yi kakkausar suka ga cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga al’ummar musulmi da su dauki matakin gaggawa na dakatar da yakin kisan kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi wa al’ummar Palasdinu. A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Bangladesh Md. Touhid Hossain sun yi musayar ra’ayi kan halin da ake ciki a yankin. Araghchi ya yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila take tabkawa, musamman manufofinta na hana Falasdinawa abinci da Ruwan sha. Ya kuma jaddada muhimmancin kiran taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kuma samar...
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fada a wannan alhamis cewa yana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Senegal a cikin watan Augusta domin tattauna yadda aza magance matsalar basussukan da ke kan kasar da kuma fara tattaunawa kan tsarin sabon shirin lamuni. Kasar Senegal na fama da bashin biliyoyin daloli da gwamnatin da ta shude ta karba, lamarin da ya sanya asusun lamuni na duniya IMF ya dakatar da shirin ba da lamuni ga kasar. A nasa bangaren kuma, wani mai magana da yawun IMF ya ce, “Asusun na bukatar karin bayanai kafin ya karfafa kimanta halin da ake ciki na basussukan kasar Senegal, sannan yana bukatar yarjejeniya kan muhimman matakan gyara.” Ya kara da cewa, “Da...

Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
Da yammacin yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya shugabanci taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da EU karo na 25, tare da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen a nan birnin Beijing. A yayin taron, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da EU suna da moriya iri daya wadda babu rikici a cikinta. Bisa yanayin sauyi da ake ciki a halin yanzu, ya kamata Sin da EU su kara yin hadin gwiwa. Kuma kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da bangaren EU a fannonin cinikayya, da zuba jari, da kiyaye muhalli, da kimiyya da fasaha da sauransu, don tabbatar da samar da kayayyaki a tsakaninsu yadda ya kamata, da...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba bayan nadin sabon shugaban karamar hukumar Gumel. A wajen bikin da aka gudanar a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa rayuwa na da kurarran lokaci, don haka ya kamata shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma sanin nauyin da ke kansu. “Rayuwa ba ta da tabbas, hakazalika shugabanci ba wasa ba ne”....
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar. Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa da tsaki a Jihar Kano. Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71 A cewarsam Tinubu ya yi watsi da halin da yankin arewacin ƙasar ke ciki wajen gina Kudancin Najeriya da kuma samar musu da kayan more rayuwa. “Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa...
Gwamnatin Jihar Yobe ta raba tallafin kuɗi ga iyalan ’yan banga da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka a bakin aiki. Kuɗaɗen wanda Daraktan ayyuka na musamman, Muhammad Alhaji Baba ya miƙa a madadin sakataren gwamnatin jihar sakamakon umarnin da Gwamna Mai Mala Buni ya bayar na a yi hakan. Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71 An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Wannan shiri dai wani ɓangare ne na shirin jin daɗin jama’a na jaha ga jami’an tsaro domin tabbatar da cewa, iyalan ’yan banga da abin ya shafa sun samu tallafi. A ƙarƙashin shirin, kowane dangin ɗan banga da ya rasu ya karɓi Naira dubu ɗari ₦500, yayin da waɗanda suka jikkata...

Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar
A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, bisa hadarin jirgin saman fasinja da ya auku a kasar, wanda ya haddasa rasa rayuka da dama. Kafar dillancin labarai ta “The Russia Today”, ta hakaito kwamitin binciken hadarin na cewa, dukkanin mutanen dake cikin jirgin saman mai lamba An-24 da ya yi hadari a yau Alhamis a yankin Amur na kasar Rasha sun rasu. An ce, jirgin na dauke da fasinjoji 43, da kuma matuka da masu bayar da hidima 6. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Idan har aka samu nasarar karɓar wannan gasa, za ta buɗe sabon babi a harkar wasanni da kasuwanci a Nijeriya, tare da samar da damammaki ga matasa da masu sana’o’i, da kuma ƙara haskaka ƙasar a idon duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta yi kira ga gwamnatin sojan jamhuriyar Nijar da ta saki tsohon shugaban kasar Muhamad Bazum, wanda ake tsare da shi tun lokacin juyin mulkin watan Yuli na 2023. Kungiyar ta kuma ce, ci gaba da tsare Muhammad Bazum da ake yi ba tare da yi masa shari’a ba, ya sabawa doka da kuma take dokokin kasa da kasa na sharia. Bayan juyin mulkin na 2023, shugabannin soja sun yi alkawalin gabatar da Bazum a gaban kotu domin yi masa shari’a bisa zargin cin amanar aksa. A 2024, kotun musamman da aka kafa ta cirewa tsohon shugaban kasar rigar kariya, da hakan ya zama tamkar share fage domin yi masa sharia,sai dai...
Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam. Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba. Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin ‘yan sahayoniyar da su ka jikkata sojoji ne. Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; Wanda ya take sojojin ya iya gudu daga wurin, ba tare da an tsayar da shi ba. Ita kuwa jaridar ‘ Yasrael Home” ta bayyana cewa; An baza ‘yan sanda a wurin da aka kai hari, domin gano inda maharin yake. Kungiyoyin Falasdinawa sun yi maraba da wannan harin,...
Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen dabbobi. Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono ta hanyar kyautata da kula da lafiyarsu, domin rage dogaro da waje samar da nama da kuma nono.” Haka nan kuma ministan na noma ya kara da cewa; Kara yawan dabbobin da ake samarwa a cikin gida,wata lalura ce ta tattalin arziki, da kuma kishin kasa. Ministan Noma na Iran ya kuma kara da cewa, ma’aikatar tasu tana kokarin ganin mayar da Iran zama cibiyar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin. Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin suna dauke da kayan abinci, ruwa da magani a cikin kasashen Jordan da Masar. A wani bayani da ofishin gwamnatin Gaza ya fitar a yau Alhamis, a cikin yankin Gaza duk wani abinci, ruwa da magani duk sun kare, don haka a halin yankin yankin yana da bukatuwa da buhunan filawa 500,000 a kowane mako. An shiga kwanaki 145 da HKI ta rufe dukkanin mashigar...
Shahararren ɗan kokawa ɗan ƙasar Amurka mai ritaya Terry Gene Bollea wanda aka fi sani da Hulk Hogan ya rasu yana da shekara 71 a duniya. A cewar TMZ da sauran rahotanni, likitoci sun mayar da martani a gidansa na Clearwater, da ke Florida da sanyin safiyar Alhamis kan Hulk Hogan ya kamu da bugun zuciya da ya yi ajalinsa. An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Daga nan an ɗauki Hogan da wuri aka saka shi cikin motar ɗaukar marasa lafiya. Duk da damuwa na kwanan da aka bayyana game da lafiyarsa – ciki har da larurar wuyansa a farkon wannan shekara, matarsa Sky ta...

Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya. Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali da Sin ta samu yayin kyautata kauyuka zuwa matsayin birane da garuruwa, Rossbach ta bayyana cewa, Sin ta cimma nasarar kawar da talauci ga mutane miliyan 800, da kuma tafiya a kan hanyar kyautata kauyuka zuwa birane da garuruwa, kuma wannan darasi ne da ya cancanci kasashen Afirka wadanda suke fuskantar kalubalen kyautata kauyuka zuwa birane su yi koyi da shi. Ta ce, nan da...
A cewar ministan, shi da sauran abokan aikin sa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a Jihar Katsina. Cibiyoyin da aka ƙaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sababbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan Asibitocin Koyarwa na Tarayya a ƙasar nan. Wannan cigaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani. Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da suka rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alƙawarin samar da ingantaccen tsarin...
Aikin gina tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin ya samu gagarumin ci gaba sosai, inda gwamnatin kasar Sin ta sanar a jiya cewa, a ranar 18 ga watan Disamban bana, za a kaddamar da manufar kafa “kwastam mai zaman kansa a duk faɗin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan” a hukumance, wadda ke nufin saukaka bincike da ragewa ko soke haraji. “Ana iya cin moriyar manufofin ba da fifikon harajin kudi a tsibirin Hainan”, sannan “mu’amalar Hainan da kasashen duniya za ta kasance cikin ’yanci da lumana”. A ra’ayin jama’a na kasa da kasa, wannan wani muhimmin mataki ne ga kasar Sin na kara fadada bude kofa ga ketare, wanda ba bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar...
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin...
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin...
An cimma matsaya kan zaɓensa bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC. Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar za su tabbatar da naɗinsa a yau Alhamis. Farfesa Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da suke da alhakin riƙe kujerar shugabancin jam’iyyar. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sun ce kasancewarsa Kirista zai taimaka wajen daidaita shugabanci, duba da cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa Musulmai ne. Shugabannin jam’iyyar na fatan Farfesa Yilwatda zai kawo sabon salo, tare da haɗa kan jam’iyyar kafin tunkarar zaɓe mai zuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar China. Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa jirgin wanda ke dauke da fasinjoji, ciki har da kananan yara biyar da kuma ma’aikatan jirgi su shida, ya fadi ne ranar Alhamis ba tare da ko mutum daya ya rayu ba. “Ma’aikatan ceto sun gano wasu sassan jirgin na ci da wuta,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito jami’an ceton na cewa. Reuters ya kuma ce jirgin wanda mallakin kamfanin Angara Airlines ne, ya fadi ne a kusa da Tyndra, wani gari da ke yankin na Amur, bayan hanyar da yake...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu. Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a fadin kananan hukumomin da lamarin ya faru. Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Dr Goje yan kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu. Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu. Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a fadin kananan hukumomin da lamarin ya faru. Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Dr Goje yan kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu. Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi...
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza. Mataimakin babban...

Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan jin kai da dama da suka yi balaguro zuwa yankunan da ake fama da rikici, da bala’o’i, da wuraren yaki a duniya, kuma dukkansu, ba tare da togiya ba, sun amince cewa, ba su taba ganin wani yanayi mai kama da abin da ke faruwa a Gaza ba. Abu Khalaf ya yi nuni da cewa: Mutanen yankin Zirin Gaza sun fara fama da yunwa, sannan...

Ministan Lafiya Na Kamaru: Hadin-Gwiwa Ta Fuskar Kiwon Lafiya Ta Shaida Zumunci Mai Karfi Tsakanin Kamaru Da Sin
Ministan lafiya na kasar Kamaru, Manaouda Malachie ya bayyana jiya Talata 22 ga wata a Yaounde cewa, hadin-gwiwar Kamaru da Sin a bangaren kiwon lafiya ta haifar da babban alfanu ga jama’ar Kamaru, kana alama ce dake shaida dangantakar kut da kut gami da dadadden zumunci tsakanin jama’ar kasashen biyu. A wajen bikin cika shekaru 50 da kaddamar da hadin-gwiwar Sin da Kamaru ta fuskar kiwon lafiya wanda aka yi a jiya Talata a birnin Yaounde, minista Malachie ya gabatar da jawabi yana mai cewa, hadin-gwiwar kasashen biyu ta fuskar kiwon lafiya ta shaida cewa, kwalliya za ta iya biyan kudin sabulu, idan aka raya hulda mai aminci, da sahihanci kuma bisa muradu iri daya tsakanin kasa da kasa. Gwamna...
Wani mummunan al’amari ya faru a Ƙaramar Hukumar Fika da ke Jihar Yobe, inda wata mata mai shekara 35, ta kashe mijinta da itace bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu a kan abinci. Rahotanni sun nuna cewa matar wacce ’yar garin Abba ce, ta ɗauki katon itacen girki ta rafka wa mijinta bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan sama da mutum 100 Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Dungus Abdulsalam, ya ce bayan faruwar lamarin, an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka kama wacce ake zargi. Marigayin ya rasu nan take, kuma ya bar mata biyu da...

Gwamantin Kasar Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga BirninSiweida Na Kasar Saboda Ci Gaba Da Bullar Rikici
Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun rufe hanyoyin zuwa birnin Sweida bayan sake bullar wani tashin hankali Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin Sweida da ke kudancin kasar tun daga wayewar garin ranar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin. A halin da ake ciki, ana ci gaba da kokarin da ake yi na cikin gida da waje na wanzar da tsagaita bude wuta da kare fararen hula. Ana zaman dar dar a lardin Suwayda da ke kudu maso yammacin kasar Siriya, inda dakarun gwamnati ke ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin tun da safiyar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza...
Gwamnatin Borno na ci gaba da ƙoƙarin ganin ta samo mafita domin iya biyan sabon albashin ma’aikata kamar yadda aka tsara a matakin ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, sun yi zanga-zangar lumana tare da neman gwamnati ta ɗauki kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a yankin. Zanga-zangar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Laraba. Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno Jama’a da dama sun halarci zanga-zangar; wasu a kan babura, wasu a cikin motoci, wasu kuma a ƙafa. Kuma sun taru a ƙofar gidan gwamnatin Jihar da ke Gusau domin nuna damuwarsu. Ƙauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka, da Fegin Mahe. Mazauna yankunan sun ce sama da mutum 100 ’yan bindiga suka...
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Ƙananan Hukumomin Rijau da Mariga a Jihar Neja. ’Yan ta’addan sun fito ne daga Jihar Zamfara, yayin da suke tafiya a kan babura ɗauke da muggan makamai. Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100 Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa Sojoji tare da taimakon jiragen yaƙi na sama sun kai farmaki bayan samun bayanan sirri. Aƙalla ’yan ta’adda 95 aka kashe a yayin artabun. Sojojin sun kuma lalata babura 18 tare da ƙwato bindigogi kirar AK-47. Sai dai an yi rashin sa’a soja guda ɗaya ya rasa ransa a yayin fafatawar. Dakarun sun sake kai wani farmaki na biyu inda suka ƙwato makamai da...
Wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, sun yi zanga-zangar lumana tare da neman gwamnati ta ɗauki kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a yankin. Zanga-zangar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Laraba. Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno Jama’a da dama sun halarci zanga-zangar; wasu a kan babura, wasu a cikin motoci, wasu kuma a ƙafa. Kuma sun taru a ƙofar gidan gwamnatin Jihar da ke Gusau domin nuna damuwarsu. Ƙauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka, da Fegin Mahe. Mazauna yankunan sun ce sama da mutum 100 ’yan bindiga suka...
Sanatoci da dama sun goyi bayan wannan buƙata. Sun bayyana cewa hakan ya shafi dukkanin yankunan ƙasar nan kuma yana daidai da yadda sauran ƙasashe ke gudanar da ci gaban tattalin arziƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da daewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka. Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin kasar Iran kan yadda mu’amalar hukumar zata kasance da Iran. Gharibabadi ya bayyana cewa idan kasashen yamma sun yi kokarin amfani da shrin SnapBack na yarjeniyar JCPOA zasu gamu da maida martani mai tsanani, sannan ya kara da cewa mu’amala da hukumar IAEA da kasar Iran zata sauka saboda amfani da karfi kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran wanda Amurka da HKI suka yi a kallafeffen...
Dakarun Sojin Operation Hadin Kai, sun daƙile hare-haren Boko Haram a garuruwan Monguno da Bitta da ke Jihar Borno, tare da wani kashe babban Kwamandan Boko Haram mai suna Ibn Khalid. Sun kuma kashe ’yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan ƙungiyar. NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Kapten Reuben Kovangiya, ya ce sojojin sun yi jarumta wajen hana ’yan ta’addan shiga Monguno. Ya ce sojojin sun yi amfani da manyan makamai wajen mayar da martani, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan Boko Haram mai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masana kiwon lafiya sun bayyana yadda ruma ke yada matsalolin rashin lafiya ga lafiyar jikin mutum. Musamman a lokuta irin na damina, ruma kan dabaibaye gidajen mutane da dama na tsawon lokaci wanda ka iya jawo matsaloli daban-daban ga lafiya da kuma gidajenmu. NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin matsalolin da ruma ke haifarwa ga lafiyar jikin namu. Domin sauke shirin, latsa nan
Daruruwan mazauna kauyen Fegin Mahe da ke yankin Ruwan Bore a karamar hukumar Gusau ta Jihar Zamfara, sun gudanar da zanga-zanga a gaban Gidan Gwamnati da ke Gusau, inda suka bukaci gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa kan kisan gilla da ‘yan bindiga ke yi a yankinsu. Masu zanga-zangar sun rike takardu masu dauke da rubuce-rubuce kamar su: “Muna bukatar zaman lafiya a yankunanmu” da “Gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka”. A cewar mazauna kauyen, harin ya faru ne da safiyar ranar Laraba, lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka afka wa kauyen, inda suka rika harbin mai-kan-uwa-da-wabi. Al’ummar yankin sun bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafi muni da suka taba fuskanta a ‘yan...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dokokin Tarayya buƙatar ƙara ranto bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare, ƙarƙashin shirin ciyo bashin na gwamnatin tarayyar na 2025 zuwa 2026. Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Tinubu ya aikewa majalisar, wadda Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanto a zamansu na yau Laraba. Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya Takartar ta ambato shugaban ƙasar na cewa karɓar rancen ya zama tilas saboda buƙatar ƙarin kuɗi da aka yi a aikin babbar hanyar Lagos zuwa Calabar, wanda ya tashi daga Dala miliyan 700 zuwa Dala miliyan 747 — ƙarin Dala miliyan 47 ke...
Gwamnatin Borno ta bayyana yawan ma’aikata a matsayin dalilin da ya sanya ƙananan hukumomin jihar ba za su iya biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata na Naira dubu 70,000 ba. Gwamnatin ta ce ta umarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su samar da tsari mai ɗorewa domin ƙaddamar da fara aikin mafi ƙarancin albashin. WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi Babban sakataren ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masana’antu, Modu Alhaji cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce yawan ma’aikatan ne ya haifar da jinkiri wajen fara biyan mafi ƙarancin albashin. Modu ya yi bayanin cewa a wasu lokutan gwamnatin tarayya na turo ƙasa da Naira...
Kungiyoyin agaji da kuma na hakkokin bil’adama sun yi gargadi akan yunwar da ake fama da ita a Gaza, tare da yin kira ga gwamnatoci da su yin matsin lamba domin kawo karshe killace Gaza da aka yi, da kuma shigar da kayan agaji a cikin yanki. Kungiyoyin sun kuma dorawa HKI alhakin halin da mutanen Gaza suke ciki na yunwa. Daga cikin kungiyoyin da su ka fitar da bayani da akwai Majalisar ‘yan gudun hijira ta kasar Norway” da “Refugee International” da wasu da adadinsu ya kai 111, sun yi gargadi akan yadda yunwa take yaduwa a cikin Gaza. Bayanin ya kunshi cewa; Mazauna yankin Gaza suna fama da yunwa saboda killace su da Isra’ila ta yi, kuma a...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambato hukumar leken asiri ta “Shabak’ tana sanar da kame wata mace, dake zaune a tsakiyar wannan haramtacciyar kasa bayan da aka tuhumeta da Shirin kashe Fira minister Benjamin Netanyahu. ‘Yan sandan HKI sun ce, matar da aka kama ta so yin amfani da abubuwa masu fashewa da ake kerawa da hannu ( IDE), kuma a halin yanzu Shabak tana gudanar da bincike.
Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa daga ƙarshen watan Yuli, zai dakatar da tallafin gaggawa na abinci da kiwon lafiya ga mutum miliyan 1.3 a Arewa maso Gabashin Nijeriya saboda ƙarancin kuɗi. Darektan WFP a Nijeriya, David Stevenson, ya ce kayan abinci da na kiwon lafiya sun ƙare gaba ɗaya, kuma rabon da ake yi yanzu shi ne na ƙarshe. Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi 2027: Obi zai iya takara ba tare da ni ba — Datti Baba-Ahmed Ya ce tallafin zai tsaya ne daga ƙarshen watan Yuli, lokacin da aka ƙiyasta kayan abinci da na kiwon lafiyar za su ƙare gaba ɗaya. Idan ba a samu tallafi cikin gaggawa ba,...
Babban abin dubawa a nan shi ne ko mene ne hikimar tura irin wadannan bakin haure zuwa kasashen Afirka? Misali kamar bakin hauren da Amerika take son turawa Nijeria, ’yan asalin kasar Venezuela, ko kuma bakin hauren da Sudan ta kudu ta karba ’yan asalin Myammar, da Cuba da Vietnam, al’adunsu da harshensu sun sha banban da na ’yan Afirka. Sabo da haka babu wata alaka tsakanin juna. To idan ba domin isgilanci da gadara ba, ta yaya Mr. Trump zai nemi tursasawa kasashen Afirka karbar irin wadannan bakin haure maimakon ya tasa keyarsu zuwa kasashensu na asali?(Lawal Mamuda) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Datti Baba-Ahmed, wanda ya yi wa Peter Obi, takarar mataimaki a zaɓen 2023, ya ce yana goyon bayan Obi idan yana so ya sake yin takara a 2027, ko da ba tare da shi ba. Peter Obi da Datti sun tsaya takara tare a 2023 sai dai sun ƙare a na uku. NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido Shugaba Bola Tinubu ne ya lashe zaɓen. Datti, ya ce Obi yana da ’yancin sake tsayawa takara a ƙarƙashin LP. Ya kuma ce ba dole ne sai Obi ya yi haɗin gwiwa da shi ba. “Peter Obi mutum ne da nake...
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe, sun fara rabon kayayyakin gini ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙananan hukumomi 13 na jihar. Wannan taimako na da nufin tallafa wa mutanen da ambaliya ta rushe musu gidaje. Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano A lokacin da aka fara rabon kayayyakin a Damaturu, wakilin babban daraktan NEDC, Farfesa Ibrahim Ali Abbas, ya ce hukumar ta kawo kayayyakin rufin gida da sauran kayan gini don taimaka wa mutane su gyara ko sake gina gidajensu. Baya ga wannan, hukumar ta kuma bai wa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a jihar Kano, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara zuba jari a fannin lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki ta hanyar kasafin kuɗi da ya danganci makomar yara. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Muhammad Farah, ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida kan kasafin kuɗi mai la’akari da bukatun yara, inda ya gabatar da wasu alkalumma masu tayar da hankali dangane da rayuwar yara a jihar. Farah ya ce jihar Kano na da yara fiye da miliyan 6 da rabi da ke ƙasa da shekaru 18, wadanda da dama daga cikinsu na...
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano. Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Lamido, ya ce hukumomi irin su EFCC ana amfani da su ne wajen matsa wa ’yan adawa lamba. Ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin aikata almundahana. A cewarsa bayan Okowa ya koma jam’iyyar APC, an daina tuhumarsa. Ya kafa misali da wata magana da Sanata Adams Oshiomhole ya taɓa yi. Ya ce: “Da zarar ka shiga APC, an yafe...
Ana zargin wata uwa a jihar Enugu da kashe ’ya’yanta biyu saboda tsananin kuncin rayuwa. Lamarin ya faru a unguwar Trans Ekulu da ke yankin birnin na Enugu. An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa An ga gawarwakin yara biyu a gidan lokacin da jami’an tsaro sukashiga ciki, lamarin da ya tayar da hankulan jama’ar unguwar. Yaran da ake zargin uwar tasu da kashewa sun hada da yarinya mai suna Esther Arinze mai shekara hudu da haihuwa da kuma kaninta mai suna Chibusoma. Ana zargin an yi amfani da makami mai kaifin gaske wajen ji wa yaran raunuka a jikunansu kafin su rasu. Majiyar labarinmu da rundunar...
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci. Ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya makara wajen dawowa makaranta zai iya fuskantar hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Iran ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskure, za su fuskanci mayar da martani da karfi Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin wani kuskure, to za su fuskanci mayar da martani mai karfi da zai wurga su cikin nadama kuma martini mai gauni ne fiye da na baya. A yayin ganawarsa da gungun mayakan sojojin sama, Manjo Janar Mousavi ya mika sakon jinjina ga shahidan daukaka da karfin Jamhuriyar Musulunci musamman shahidi Major Janar Hajizadeh. Ya yaba da rawar da ya taka wajen ciyar da shirye-shiryen rundunar Sojan sararin samaniya da bunkasa karfin makamai masu linzami da jirage marasa matuki ciki na...
Wani sabon salon gwamnatin mamayar Isra’ila na neman kashe Falasdinawa ‘yan gudun hijira da tsananta yunwa kansu Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun rufe tekun ga masunta da ‘yan gudun hijira a zirin Gaza, matakin da ke kara dagula al’ummar Gaza da aka killace. Gabashin tekun kudancin Gaza shi ne mashigar da mazauna yankin da kuma ‘yan gudun hijira a dukkanin yankunan zirin Gaza, musamman a kudancin zirin Gaza, biyo bayan umarnin ficewa da sojojin mamayarr Isra’ila suka bayar ga mazauna yankin Al-Mawasi da ke yammacin yankin. Tekun ya zama mafaka daya tilo ga ‘yan gudun hijira da mazauna yankin saboda hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa kan Falastinawa. Sai dai rundunar sojin mamayar Isra’ila ta sanya sabbin takunkumi...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar Barack Obama da cin amanar kasa tare da yin kira da a yi masa shari’a Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi magabacinsa, Barack Obama da cin amanar kasa, inda ya bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya kan wani rahoton sirri da ya nuna cewa; Jami’an gwamnatin Obama sun murguda bayanai game da katsalandan din Rasha a zaben Amurka na shekara ta 2016. Kalaman na Trump sun zo ne yayin wani taron manema labarai a ofishin Oval, wanda shugaban kasar Philippines Ferdinand Marcos ya halarta. Yana cewa:”Bisa ga abin da ya karanta…tsohon shugaba Obama ne ya fara wannan badakalar,” ya kara da cewa Obama shi ne “shugaba” na...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata a ce ana ware wa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya. NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin...
“Farfaɗowa na samuwa, kuma a bayyane yake cewa sabon yanayi na sauyi yana faruwa a Kaduna,” in ji shi. Ya jaddada cewa kyakkyawar gwamnati na nufin kula da buƙatun al’umma, musamman waɗanda rikici ya shafa. “Muna share hawayen waɗanda rikice-rikice suka shafa. Muna haɗa kan al’umma. Muna tabbatar da cewa kowa yana da wajen zama da jin cewa yana da muhimmanci,” in ji Tinubu. Shugaban ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna, ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, da kuma hafsan hafsoshin tsaro bisa matakan soja da na lumana da suke ɗauka don shawo kan matsalar tsaro. “Zaman lafiya na gaskiya sai an gina shi, ba zai zo da ƙarfi ko tsoratarwa ba,” in ji shi. Ya...
Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran. Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a kasar Iran nan gaba bisa tsarin dokokin kasa da kasa. Wannan yunkuri yasa an ga bangarorin biyu na Amurka da Isra’ila suna matsa lamba a kan sauran bangarori na duniya, tare da bayyana Shirin na Iran a matsayin mai matukar hadari ga duniya, da nufin samun goyon bayan kasashen duniya kan bakaken manufofisu a kan kasar ta Iran. Dangane da zargin da...
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka. “Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem. Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen...
Amurka ta yanke shawarar ficewa daga hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a karo na biyu saboda matakin da ta dauka na shigar da Falasdinu a matsayin mamba. Mataimakiyar sakatariyar yada labaran fadar White House Anna Kelly ta sanar da matakin a cikin wata sanarwa a ranar Talata. Kelly ta ce dalilin da ya suka dauki wannan kan hukumar UNESCO, shi ne ta tallafa wa shirye-shiryen da Amurka ke kallonsu a matsayin wadanda ba su dace da muradunta ba. “Shugaba Trump ya yanke shawarar janye Amurka daga UNESCO, wadda ke kula da ayyuka a bangaren raya al’adu da ilimi da zamantakewar al’umma, saboda daukar wau matakai wadanda ba su dace da manufofin Amurka...
Wata sabuwar tashin-tashina ta sake kunno kai a yankin kahon Afirka a daidai lokacin da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya yi gargadi kai tsaye ga firaministan Habasha Abiy Ahmed, inda ya yi kashedin sake kaddamar da wani yaki. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Habasha ke kokarin shiga bangaren ruwa Eritra da kuma tabarbarewar dangantakar bangarorin biyu tun bayan rikicin Tigray. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan telebijin, shugaba Afwerki ya yi gargadin cewa adadin yawan jama’ar Habasha ba zai tabbatar da nasarar soji ba, yana mai nuni da dabarun yakin da Habasha ta yi amfani da su a yakin da ya gabata, yana mai cewa duk da yawan sojojinta amma bata...
A cewar Ringim, idan ana so a sami cigaban da ya shafi kowa da kowa a Arewacin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, to ana buƙatar siyasa irin ta Kwankwaso wadda ke mayar da hankali kan talakawa da gaskiya a mulki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa. Sanarwar ta bayyana cewa bikin sanya hannun ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnati dake Dutse, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta, ciki har da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Sani Isyaku. Ta ce Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, bayan kai-komo na sama...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya baki daya. Guo Jiakun, ya jaddada muhimmancin taron, kasancewar ya zo a gabar da harkokin cudanyar kasa da kasa ke fuskantar yanayi na tangal-tangal, da ma karuwar daukar matakan kashin kai daga bangare guda, da kariyar cinikayya. Ya ce, hadin gwiwar sassan biyu, ya haifar da manyan nasarori a baya, wanda hakan ya bunkasa ci gaba da daukakarsu, tare da samar da tarin alfanu ga...
Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi ta yanke hukunci a kan gwamnatin jihar Bauchi da ta biya tsohon Akanta-Janar na jihar, Dakta Sa’idu Abubakar, Naira miliyan 100 a matsayin diyyar take masa haƙƙi da kuma tsare shi ba bisa ƙa’ida ba. Kotun ta kuma umarci gwamnati ta wallafa ban haƙuri a manyan jaridu guda biyu cikin kwanaki 14. Mai Shari’a Aminu Garba ya yanke wannan hukunci ne a ƙarar da Dakta Abubakar ya shigar, yana zargin gwamnati da jami’anta da take masa haƙƙi, da kama shi ba tare da bin ƙa’ida ba, da musgunawa. Ya bayyana cewa hakan ya saɓawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar kare haƙƙin bil’adama ta Afrika. Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen killace yankin Gaza da aka yi, da kuma wajabcin kai musu abinci da magunguna. Kungiyar malaman musulmin ta kuma bayyana abinda HKI take yi na killace mutanen Gaza fiye da miliyan biyu da haka su abinci da magani,musamman mata, yara da manya,wani babban laifi ne da ba shi da tamka a cikin tarihi, tana mai yin kira ga al’ummu da gwamnatoci da su motsa saboda su taimaki raunana. Kwamitin fatawa da yake a karkashin wannan kungiyar ta malaman musulmi, ya dogara da ayoyin alkrur’ani da hadisan ma’aiki ( s.a.w) da manufofi na shari’a da ka’idoji...
Yar wasan gaba ta Nijeriya, Chinwendu Alozie, ce ta tabbatar da nasara da kwallon da ta jefa kafin tashi daga wasan. Wannan nasara ta ba wa tawagar ta Justin Madugu damar kaiwa wasan ƙarshe na gasar. Yanzu haka, Super Falcons za su kara da ƙasar da za ta yi nasara tsakanin Moroko, wacce ke masaukin baki, da Ghana, a wasan da za a buga daga baya a yau Talata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Batun kare hakkin bil’adama da ake yi a duniya ba komai ba ne sai karya. Shugaba Fizishkiyan ya yi ishara da yadda masu ikirarin kare hakkin bil’adama suke sa kafafunsu suna take hakkin mutanen Gaza da cikin kasashen yammacin Asiya da kuma tafka manyan laifuka. A yau Talata ne dai shugaban kasar ta Iran ya gabatar da jawabi a wurin bikin girmama shahidan kallafaffen yaki na kwanaki 12, ya bayyana cewa: “A cikin wannan duniyar wacce take riya ci gaba da wayewa, a gaba idon duniya, ake yanke wa mutanen Gaza ruwan sha da abinci, a hana mata da kananan yara. Haka nan kuma ake tafka laifukan da su ka kunshi kisan...
Fira ministan HKI wanda kotun duniya ta manyan laifuka take nem ruwa a jallo ya bayyana cewa; Babu yadda za su tsayar da yakin Gaza, matukar kungiyar Hamas ba ta mika wuya baki day aba. Benjemine Netanyahu ya kuma ce; A lokacin da Hamas za ta mika makamanta ne, shi ne za mu yi tunanin ko za mu bude mata hanyar ficewa daga Gaza, da kuma dakatar da yaki. A gefe daya tashar talabijin din CNN ta ambato wata majiya ta gwamnatin Amurka tana cewa; Amurka ta gargadi kungiyar Hamas akan cewa, hakurinta ya kusa karewa akan batun tsagaita wuta, tare da neman kungiyar ta gwagwarmaya ta bayar da jawabi a cikin gaggawa kafin makwanni biyu masu zuwa. Tashar talabijin...
Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai dubban ƙananan yara da gwamnati ta rufe su ba kuma tare da cikakken bayani ga iyalansu ba, wasu ma a yanzu babu cikakken bayani kan inda suke ko kuma halin da suke ciki. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Asusun ya ce a Nijeriya rufe ƙananan yara tare da...
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce a watan Yuni, yawan wadanda ba su da aiki a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, watau bai sauya ba daga yadda ya kasance shekara 1 da ya wuce. Kasar Sin na da burin adadin marasa aikin yi ya tsaya kan kaso 5.5 a bana, tare da burin samar da guraben aikin yi sama...
Yuro biliyan 4 Yen biliyan 15 (na Japan) Tallafin dala miliyan 65 Kuma aron cikin gida ta hanyar sayar da hannun jarin gwamnati (bond) na kusan Naira biliyan 757. Har ila yau, akwai shirin tara kuɗi har dala biliyan 2 ta hanyar takardun lamuni da za a fitar cikin ƙasa amma a kuɗin ƙetare. Shugaban kwamitin kasafi, Sanata Olamilekan Solomon, ya ce wannan amincewa tsarin doka ce kawai, domin an riga an haɗa bashin cikin tsare-tsaren kasafin kuɗi da MTEF tun da farko. Sanata Sani Musa (Niger Ta Gabas) ya bayyana cewa wannan shiri ba na shekara ɗaya ba ne, amma zai shafi rabon kuɗi na tsawon shekara shida, yana mai jaddada cewa Nijeriya ba ta taɓa gazawa wajen biyan...
Su kuwa mahalarta taron, sun yaba da kyautatuwar dangantakar kasashen biyu da rawar da SCO ke takawa. Sun kuma bayyana fatan Masar da Sin za su yi amfani da damarmakin ci gaba da SCO ta samar domin su hada hannu tare, su inganta tsarin jagorantar harkokin duniya da farfadowar kasashe masu tasowa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati Ya ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin shugaban hukumar da ke Kazaure, Mansur Dabuwa, inda aka lalata katan 400 na barasa da darajar kudinsu ya kai naira miliyan 5.8. Ya bayyana cewa an kama barasa da aka kona a lokacin samamen da aka kai a sassa daban-daban a...
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar. Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100 da aka samu a bara. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati Sanarwar ta ce an yi bitar alkaluman mamatan a bana ne bisa la’akari adadin waɗanda suka kamu kuma ta yi ajalinsu a shekarar 2024. Hukumumar ta ce alkaluman mamatan ya kai kashi 18.9 cikin 100 na...
Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati. Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan 2 daga 2024, da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 wanda ya kai Naira tiriliyan 1.9. Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki, Dakta Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun daɗe suna nuna kishin ƙasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji. Ta bayyana cewa kudin da ake kashewa wajen samar...
Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati. Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan 2 daga 2024, da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 wanda ya kai Naira tiriliyan 1.9. Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki, Dakta Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun daɗe suna nuna kishin ƙasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji. Ta bayyana cewa kudin da ake kashewa wajen samar...
Gwamnatin ƙasar Guinea ta rufe wasu sassan kamfanoni guda 1,724 sakamakon kama su da laifin ƙin bin dokokin hukuma, yayin da aka janye kayayyakin da suke sarrafawa daga kasuwa. Sanarwar na zuwa ne ƙarƙashin ma’aikatar kasuwanci a ƙasar, tana mai cewa an ɗauki matakin ne don kare lafiyar masu sayen kayayyakin da kuma tabbatar da kare muhalli, da kuma tilasta musu biyayya ga dokokin tafiyar da kamfanoni. Ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar ta ce ba shakka wannan mataki zai zama tamkar hannunka mai sanda ga sauran kamfanoni da ke tafiyar da ayyukansu ba dai-dai ba. Da yake magana shugaban ƙungiyar masu sayen kayayyaki na ƙasar, Ousmane Keita, ya ce tun shekaru sama da uku suke ta wannan kiraye-kiraye, amma ba a...
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya huɗu a Najeriya da aka zaɓa don wannan aikin na tsawon shekaru uku (tare da yiwuwar ƙarin shekaru biyu don sa ido). Sauran su ne Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (Owo) da Babban Asibitin Irrua da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin. Wannan shiri, wanda Gidauniyar Ƙasa da Ƙasa kan Cututtukan Masu Saurin Yaɗuwa a Najeriya (IFAIN) ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tashin farashin takin zamani yana hana manoma da dama noman wasu nau’ukan abinci. Manoma da dama sun ƙaurace wa noman masara da shinkafa da aka fi amfani da su a Najeriya sakamakon tsadar takin zamani, abin da masana ke ganin in ba a ɗauki mataki ba, hakan zai kawo ƙarancin abinci a ƙasar. NAJERIYA A YAU: Abin da ya sa muke yi wa PDP zagon ƙasa —Sule Lamiɗo DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa farashin takin zamani ya yi tashin gwauron zabo a ƙasar. Domin sauke shirin, latsa nan
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a tsananta hukunci kan masu cin zarafin ’ya’ya mata, yana mai cewa babu wani musulmi nagari da zai yi wa matarsa dukan da har zai yi mata lahani. A yayin da yake tunatar da malamai da limamai kan muhimmiyar gudunmawar da za su bayar a wannan fage domin yi wa tufkar hanci, Sarkin ya bayyana damuwa kan yadda matsalolin fyade da kuma samun magidantan da ke dukan matansu suka zama ruwan dare a Jihar Kano. Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh Sarki Sanusi na wannan furuci yayin da ya karbi bakuncin tawagar cibiyar bunkasa bincike (dRPC)...
Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa yunwa na ƙara tsananta a Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe. A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa. Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet ICRC ta bayyana cewa fiye da mutum miliyan 3.7, wadanda galibi manoma ne na fuskantar barazanar matsanancin rashin abinci a yankin da aka shafe shekaru ana rikici. Churi Ibrahim, wani tsohon manomi dan shekara 70 da ke ciyar da iyalinsa goma,...
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta sanar da cewa a ’yan kwanakin nan za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a wasu jihohi da ke sassa daban-daban na ƙasar. Hakan na kunshe cikin hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025 da hukumar ta fitar. Ƙalubalen da ke tattare da sauya sunan jami’a An nada ’yar Najeriya a Kwamitin Nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya NiMet ta shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa. A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce PDP ce kaɗai ke da ƙarfin gina ƙasa. “Wannan gwamnati ce da ke cewa mutane su yi azumi alhali su suna cin abinci sannan suna jin daɗi. Babu ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa ko wata jam’iyya mai jin zafin halin da mutane ke ciki da za ta goyi bayan Tinubu a 2027. Gwamnatinsa kasuwanci ne mara riba,” in ji Ologunagba. Kakakin PDP ya kuma nuna damuwa kan halin rashin tsaro, inda ya ambaci kisan gillar da aka yi wa mutane a Jihar Filato da kuma hari kan ɗan takarar PDP daga Anambra a Abuja, a matsayin alamu cewa rashin tsaro ya zama ruwan dare. Ya ce ƙarfin PDP yana hannun talakawa, ba sai da manyan ’yan siyasa ba....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.” “Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!” A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar...