Kasar Faransa Ta Jaddada Aniyarta Ta Amincewa Da Yantacciyar Kasar Falasdinu
Published: 6th, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Faransa ya jaddada aniyar birnin Paris na amincewa da kasar Falasdinu
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya tabbatar da aniyar Faransa na amincewa da kasar Falasdinu, yana mai jaddada cewa wannan amincewa ba zai kasance na bai daya ba, sai dai a matsayin wani bangare na kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe.
Hakan ya zo ne a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo kasa makonni biyu gabanin taron hadin gwiwa tsakanin Faransa da Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya.
Barrot ya bayyana cewa, makasudin taron shi ne hada kasashe da masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da hukumar Falasdinawa da kasashen Larabawa don ciyar da shirin zaman lafiya gaba. Ya bayyana cewa, Faransa a matsayinta na mamba ta dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, tana da wani nauyi na musamman a wannan fanni, kuma amincewar da ake sa ran na da nufin kara tabbatar da martabar kasar Falasdinu da samar mata da damammaki.
Barrot ya kuma jaddada muhimmancin tattaunawa kan batun kwance damarar kungiyar Hamas a matsayin wani bangare na duk wani hangen nesa na makomar zirin Gaza bayan yakin. Ya bayyana damuwarsa game da tsarin raba kayan agaji a yankin, wanda ya bayyana a matsayin “tsarin soja”, lura da hargitsi da tashe-tashen hankula da ya haifar, musamman bayan killace yankin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi tun tsawon watan Maris din da ya gabata.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Falasdinu
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin
“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.”
“Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!”
A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar Sin, tare da hada kai da kasar Sin da ma sauran baki ’yan kasuwa wajen kyautata tsarin samar da kayayyaki na duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp