Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano
Published: 6th, June 2025 GMT
“Yawancinmu ba mu je kasuwa ba yau saboda Sallah. Bidiyon da aka ɗora ne ya sa muka samu labarin wutar. Abin takaici, wasu shaguna da ke kusa da nawa sun ƙone,” in ji shi.
Ƙoƙarin da wakilinmu ya na tuntuɓar mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, bai yi nasara ba domin wayarsa ba ta shiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Farm Centre Gobara
এছাড়াও পড়ুন:
An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
’Yan sanda a jihar Legas sun kama wani tsohon fursuna tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a jerin laifukan fashi da yankan aljihu a jihar kwana biyar da fitowa daga kurkuku.
Tsohon fursunan mai shekaru 25 da haihuwa, Segun Kolawole, an kama shi ne bayan kwana biyar da aka sako shi daga cibiyar gyaran hali ta Kirikiri, a jihar Legas.
Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano SpalletiSauran wadanda aka kama tare da shi sun haɗa da Sodiq Isa mai shekaru 27 da Adekanmbi Ganiu mai shekaru 21.
Rahotanni sun nuna cewa an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifukan yankan aljihun mutane da sauran laifukan sata a sassa daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da cafke Kolawole, inda ta ce an kama shi da misalin ƙarfe 8 na safiyar Talata a kasuwar Oshodi, bayan jami’ai sun lura da motsinsa da ya zama abin zargi.
Adebisi ta ce an same shi da tsabar kuɗi ₦80,000 da wayar Infinix Note 40 Pro, waɗanda aka gano daga wani fashi da ya aikata a Opebi, inda ake zargin ya saci ₦200,000 da wayar daga hannun wani ɗan kasuwa da ke barci.
“Bincike ya ƙara tabbatar da cewa ya riga ya sayi sabbin kaya da takalma da wani ɓangare na kuɗin da ya sata, waɗanda suma aka kwato su daga hannunsa,” in ji ta.
Haka kuma, a wani samame daban da aka gudanar da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Juma’a, jami’an RRS sun kama Sodiq Isa da Adekanmbi Ganiu bisa zargin yunkurin satar wayoyin hannu daga hannun fasinjoji a sassa daban-daban na Legas.