HKI Ta Kashe Wani Babban A Cikin Shuwagabannin Falasdinawa
Published: 8th, June 2025 GMT
Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Asa’d Abu Sharia shi ne baban sakataren kungiyar ‘Dakarun Palastinewa”. Wacce aka kafa a shekara ta 2001 M.
Kungiyar kanta ta tabbatar da wannan labarin ta kuma bayyana cewa ya dade yana shugabantar wannan kungiyar sannan a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya shiga cikin yakin da aka fara kan HKI kuma dakarunsa sun kama yahudawa da dama suka shigo da su su gaza.
A wani labarin kuma kungiyar ta kara da cewa tare da shi akwai dan uwansa Ahmed Abu Sharia, ko wanda akewa Lakabi da Abu Falasteen, sun yi shahada tare. Banda haka kafin shahadarsa Abu Sharia ya rasa danginsa na kusa kimani 150 a yankin tufanul Aksa ya zuwa yanzu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fiye Da Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki
Kungiyoyin agaji da kuma na hakkokin bil’adama sun yi gargadi akan yunwar da ake fama da ita a Gaza, tare da yin kira ga gwamnatoci da su yin matsin lamba domin kawo karshe killace Gaza da aka yi, da kuma shigar da kayan agaji a cikin yanki.
Kungiyoyin sun kuma dorawa HKI alhakin halin da mutanen Gaza suke ciki na yunwa.
Daga cikin kungiyoyin da su ka fitar da bayani da akwai Majalisar ‘yan gudun hijira ta kasar Norway” da “Refugee International” da wasu da adadinsu ya kai 111, sun yi gargadi akan yadda yunwa take yaduwa a cikin Gaza.
Bayanin ya kunshi cewa; Mazauna yankin Gaza suna fama da yunwa saboda killace su da Isra’ila ta yi, kuma a duk lokacin da mutanen su ka nunfi wurin da aka ware domin raba abinci sai a bude musu wuta.
Wuararen raba abincin da suke a cikin yankin Gaza dai, HKI da Amurka su ka shriya su a matsayin tarkon kashe Falasdinawa da suke zuwa wurin.
Bayanin ya kuma ce, da akwai kayan abinci, ruwa da magunguna masu yawan gaske da aka ajiye da su a wajen yankin Gaza, amma kuma Isra’ila ta hana a shiga da su.
Haka nan kuma sun bayyana cewa; Dukkanin kayan agajin da ake da su, sun kare baki daya, kuma kungiyoyin agaji suna Kallon yadda ‘yan’uwansu suke ramewa da kama hanyar mutuwa saboda rashin abinci.
Har ila yau sun yi ishara da cewa: Dokoki da Isra’ila ta kafa ne, da su ka jawo jinki, da kuma yadda take karkatsa yankin na Gaza wanda yake a killace, su ne su ka haddasa yunwa da mutuwa.”
Haka nan kuma wadannan kungiyoyin sun yi kira ga gwamnatoci da su kawo karshen bin matakai na cike-ciken takardu akan dukkanin hanyoyi, saboda share fagen shigar da kayan abinci cikin yankin Gaza.