Aikin Ba Da Ilmi Ba Makamin Takarar Jam’iyyu Ba Ne
Published: 7th, June 2025 GMT
Ran 4 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan sanarwar hana baiwa daliban ketare dake neman gurbin karatu a jami’ar Harvard bizar shiga kasar da dakatar da shigar daliban ketare dake karatu a jami’ar da ‘yan ketare masu shirin mu’ammalar ilmi a cikin kasar. Sanawar ta ce, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bisa la’akari da batun tsaron kasar.
Gwamnatin Amurkta ta matsa lamba kan jami’o’in kasar ciki hadda Harvard ta hanyar katse ayyukansu dake da nasaba da kasashen ketare da hana baiwa dalibai Sinawa bizar shiga kasar ba gaira ba dalili, matakin da ya bullo da ainihin burinta na amfani da sunan wadannan jami’o’i don cimma nasarar matakanta na siyasa. Ba za a dakatar da irin wannan ja-in-ja a tsakanin jam’iyyun siyasa biyu na kasar game da jami’o’in kasar ba, matukar jam’iyyun suna ci gaba da takara da juna babu iyaka.
Harvard jami’a ce dake da tsawon tarihin kusan shekaru 400, wadda ke da babbar ma’ana da gagarumin tasiri ga bangaren ba da ilmi a duniya. Siyasantar da batun ba da ilmi da sanya jami’o’i cikin rikicin takarar jami’yyu, ba keta halastaciyyar moriyar dalibai a duniya kadai yake yi ba, har da cin fuskar aikin ba da ilmi, kuma duniya ba za ta yarda da hakan ba. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki.
Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata a ce ana ware wa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya.
NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba BuhariShirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin hutun makaranta.
Domin sauke shirin, latsa nan