HKI Ta Kaiwa Jirgin Ruwan Masu Rajin Kare Hakkin Mutanen Gaza Na Jinkai
Published: 9th, June 2025 GMT
Wadanda suka shirya jirgin agaji zuwa Gaza mai suna Madleen sun bada sanarwan cewa HKI kai farmaki kan jirgin a safiyar yau Litinin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jami’an tsaron HKI sun kaiwa jirgin Madleen hare-hare a safiyar yau Litinin kafin iasar Jirgin agajin zuwa gabar tekun Medeterania a gaza.
Labarin ya kara da cewa Thiago Avila, dan rajin kare hakkin bil’adama daga kasar Brazil a cikin Jirgin ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun yiwa jirgin kofar rago . Y ace sojojin ruwa na HKI sun kaiwa jirgin agaji ” Madleen farmakai. Jirgi wanda yake kokarin keta kofar ragon da HKI ta yi wa Gaza tun shekara 2006.
Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun kama masu rajen kare hakkin mutanen Gaza, dake cikin jirgin ruwa na Madleen saboda an daina jinn duriyarsu.
Daga cikin wadanda suke cikin wannan jirgin dai, wadanda kuma suke tsare a hannun jami’an tsaron HKI sun hada da Greta Thunberg mai rajin kare yanayi, sannan mutane 12 wadanda suke rajin kare mutanen Gaza ta hanyar Jirgin Madleen, da kuma
Sai kuma Liam Cunningham da Rima Hassan, yan majalisar dokokin Taarayyar Turai daga kasar faransa kuma yan asalin kasar Falasdinu. Labarin yace LIMA ta yada sautin da karar jiniyar da sojojin yahudawan suka kunna a lokacin kai masu hari.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Mahmood Abu-Odeh dan jarida wanda yake bin jirin ceton na Madleen daga kasar Jamus ya bayyana cewa an kama wadanda suke jirgin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gamayyar Ƙungiyoyin Tinubu/Shettima Za Su Ƙaddamar Da Gangamin Yaƙi Da Masu Yi Wa Tafiyar Shetttima Zagon Ƙasa – Aminu Boyi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp