Aminiya:
2025-11-02@19:46:05 GMT

Abin da ya sa na yi wa Buhari juyin mulki —Babangida

Published: 24th, February 2025 GMT

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (murabus) ya bayyana dalilin da ya hambarar da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a 1985.

Janar Babangida ya bayyana dalilin da gwamnatinsa ta karya darajar Naira da sauran sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta yi bayan kifar da Buhari.

Babangida, wanda shi ne babban hafsan sojin kasa a lokacin Buhari, ya taka rawar gani a juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Shehu Usman Shagari a 1983 da kuma na 1985 da ya kawo shi kan karagar mulki.

Ya ba da cikakken bayani game da abubuwan da suka faru a cikin littafin tarihin rayuwarsa da ya ƙaddamar a makon jiya.

Har yanzu Najeriya na buƙatar shugabanni nagari – Sheikh Gumi NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri

Littafin na Babangida ya haifar da cece-kuce, game da muhimman batutuwan da suka dabaibaye mulkinsa na shekaru takwas, musamman soke zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni; kashe babban dan jarida, Dele Giwa; da kuma kashe Manjo Janar Mamman Vatsa bisa zargin yunkurin juyin mulki.

 “Juyin mulkin 1985 ya zama dole.”

A babi na shida, Babangida ya ba da hujjar juyin mulkin da aka yi wa Janar Buhari a 1985. Ya bayyana cewa juyin mulkin martani ga korafe-korafen ’yan Najeriya da kuma tabarbarewar al’amurana kasar.

Ya ce, “A farkon shekarar 1985, ’yan Najeriya sun fara fargaba game da makomar kasarmu. Al’amarin ya kasance mai hadari kuma yana cike da munanan alamun a fili da hatsarin da ke yanzu.

“A bayyane yake ga shugabancin sojojin cewa aikin da muka yi da nufin ceto ƙasarmu a shekarar 1983 ya watse,” kamar yadda Janar Babangida ya rubuta.

Ya ce rashin daukar mataki zai kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin sojoji, wanda a ganinsa hakan zai haifar da mummunar illa ga kasar.

“Idan sojojin suka yi samu rabuwar kai, al’ummar za su bi sahu, kuma abin da zai biyo baya zai zama mai ban tsoro ne da ba za a iya tunani ba,” in ji shi.

A cewarsa, a shekarar 1983 sojoji sun hambarar da Shugaba Shagari ne cikin haɗin kai, amma sai aka fara samun rarrabuwar kawuna tsakaninsu.

“Sojoji, a matsayinsu na waɗanda aka sani da hadin kai, sai ga shi an fara samun guna-guni; down haka ya zama dole a yi wani abu don kada mu rasa kasar.

“Babban abin da na ji tsoro shi ne, rarrabuwar kawuna da ra’ayi a tsakanin sojoji na iya haifar da bangaranci a tsakaninsu. Idan kuma aka bari a ci gaba da samun gindin zama, to akwai hatsarin gaske.”

Ya zargi Buhari da mataimakinsa Birgediya Janar Tunde Idiagbon da mayar da mayar da sojoji saniyar ware, tare da daukar tsauraran matakan kama-karya wajen tafiyar da mulki.

“Sun dauki kansu kamar wasu waliyyai, inda suka kawo wa sojoji bakin jini a wurin al’ummar kasa. Suna take hakkin al’umma tare da cin zarafi babu kakkautawa,” in ji Babangida.

A cewarsa gwmanatin sojin Buhari ta yi mulki ne ta hanyar tsoratarwa maimakon sanya ’yan kyakkyawan fata a zukatan al’umma.

“Kamata ya yi mu Inganta rayuwarsu mu sa musu kyakkyawan fata cewa rayuwarsu za ta inganta. Amma maimakon haka sai aka yi ta kafa musu dokokin kama-karya.

“Sai aka wayi gari gwamnatin da aka kafa da niyyar cimma muradun bai-ɗaya na sojoji, ta koma ta wasu ’yan tsirarun mutane masu taurin kai,” in ji Babangida.

Taɓarɓarewar tattalin arziki

Ya bayyana cewa tsarin musayar kaya na gargajiya da Buhari ya koma amfani da shi ya kara kassara tattalin arzikin Najeriya.

Ya ƙara da cewa lalacewar tattalin arziki da guna-gunin ’yan kasa kan matsin rayuwa na daga cikin abin da suka sa su hambarar da Buhari.

Ya ce, “Kamar yawancin juyin mulkin soja, mun yi ne sakamakon yawan korafe-korafen jama’a. Talakawa sun shiga matsanancin matsin rayuwa, ga shi yanayin tattalin arziki sai kara  ta’azzara suke yi a kulla-yaumin.

“Kayayyakin masarufi da sauran bukatun yau da kullum sai karanci suke kara yi.

“Sannan ku a komawa amfani da  tsohuwar hanyar yin ciniki ta hanyar musayar kaya a kasuwancin kasa da kasa yana nufin cewa ba a kama hanyar kawo karshen matsalolin tattalin arziki a tsakanin al’umma ba.

Dokokin kama-karya, sun tauye ’yancin walwalar jama’a, ga kuma hukunci mai tsauri, in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Buhari tattalin arziki Babangida ya

এছাড়াও পড়ুন:

Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

“Ana kiransa da suna dokar binciken tntanet ta tsoratarwa, wadda kasashen da suka ci gaba da dama suka dade da yin watsi da ita. A karni na 21, ba za a iya tunanin cewa gwamnatin Nijeriya za ta tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda shi ne ginshikin mulkin dimokuradiyya.”

Atiku ya ce duk wata doka da ke take ‘yancin ‘yan kasa na yin tsokaci mai muhimmanci game da shugabanninsu ko a hanyoyin sadarwar zamani ko ta hanyar magana ba dimokuradiyya ba ce kuma kai tsaye take hakkokin Dan’adam ne.

“A cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara daukan matakan da ke janyo kuncin tattalin arziki da yunwa da bakin ciki ga mutanen Nijeriya, mun shaida zanga-zanga da koke-koke daga ‘yan kasa da ba za su iya daukar mulkin rashin gaskiya ba. Duk da haka, maimakon sauraron ‘yan kasa sai gwamnatin ta zabi hanyar amfani da karfin hukumo da tsoratarwa wadda ta juya lamarin zuwa wani abu daban.

“Lallai abin bakin ciki ne na ganin ana take hakkin ‘yan kasa da kundin tsarin mulki ya tabbatar a lokacin da ya kamata dimokuradiyyarmu ta kasance mai bin tsari. Dole ne mu tunatar da gwamnatin Tinubu cewa babu gwamnati a lokacin da ta kasa kare ‘yancin ‘yan kasarta, komai karfinta kuwa. Yin haka abun ta da hankali ne kuma hakan yana nuna gazawar gwamnati a fili.”

Atiku ya ce tabbas gwamnati na da alhakin kula da doka da oda, babu ingantacciyar gwamnati da za ta harbi masu zanga-zangar lumana da harsashi mai rai ko ta boye a bayan dokoki tana musguna wa ‘yan kasa.

Ya ce rashin kulawar gwamnati Tinubu ga dokar kasa da kuma ci gaba da kin bin umarnin kotu sun zama shahararrun siffofinta mafiya suna a kasar nan a halin yanzu.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kara da cewa tun farkon wannan gwamnati, kungiyar kare hakkin Dan’ada ta Amnesty ta soke wannan gwamnatin da take hakkin Dan’adam.

Ya ce haka ma wasu kungiyoyi masu muhimmanci kamar irinsu kungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya da kungiyar kare ajandar kafafen yada labarai sun yi korafi kan cin zarafin ‘yan jarida da ‘yan kasa ta hannun jami’an gwamnati.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025 Siyasa Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta October 24, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma