Aminiya:
2025-07-23@22:46:38 GMT

Kwamishina ya yi murabus saboda sauya sheƙar Gwamnan Akwa Ibom

Published: 6th, June 2025 GMT

Kwamishinan Harkoki na Musamman a Jihar Akwa Ibom, Mista Ini Ememobong, ya yi murabus daga muƙaminsa biyo bayan sauya sheƙar Gwamna Umo Eno daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Sallah: Gwamna Inuwa ya yi kiran sadaukarwa da haɗin kai Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC

Gwamna Eno ya faɗa wa kwamishinoninsa cewa duk wanda ba ya son bin sa zuwa APC ya ajiye aikinsa.

Ememobong, ya ce yana girmama ra’ayin gwamnan, amma ba zai iya binsa APC ba.

“Ba zan iya yin wannan tafiya ba,” in ji Ememobong.

“Na yarda da siyasar aƙida. Na gode wa gwamna bisa ƙauna da ya nuna min, amma dole na tsaya kan abin da nake da yaƙini a kai.”

A ranar Juma’a ne, Gwamna Eno, ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC, inda ya ce ya yanke hukuncin ne bayan dogon nazari.

“Na tuntuɓi mutane daga ko ina a cikin jihar,” in ji Eno.

“Wannan shawara ce da ta dace da lokacin da muke ciki. Mun shiga APC ba don mu samu rauni ba, sai don mu ƙara ƙarfi.”

Da wannan sauyin, APC na da iko a jihohi huɗu cikin shida da ke yankin Kudu Maso Gabas, sai Jihohin Ribas da Bayelsa kawai suka rage a hannun PDP.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Akwa Ibom Kwamishina Sauya Sheƙa Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar

Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen inganta ci gaban zamantakewar al’umma da kuma tallafawa aiwatar da Muradun Cigaba mai Dorewa (SDGs).

Hajiya Amina Mohammed ta kai ziyara Jihar Kano ne domin yin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar fitattun dattawan nan  biyu, wato Alhaji Aminu Alhassan Dantata da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A yayin ziyarar tata, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna gamsuwa da wasu daga cikin shirye-shiryen Gwamna Yusuf na cigaban al’umma, musamman wadanda suka yi daidai da muradun ci gaban duniya.

Daga cikin wadannan shirye-shirye akwai sanya fitilu masu amfani da hasken rana a titunan Kano, kafa cibiyar kula da cututtuka ta Kano (Kano Centre for Disease Control), wadda ita ce irinta ta farko da wata gwamnati ta jiha ta kafa a Najeriya, da kuma kokarin fadada tsarin inshorar lafiya domin al’ummar jihar su amfana.

Ta kuma yaba da kirkirar Ma’aikatar Wutar Lantarki da Makamashi, tare da sake tsara Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, wanda dukkansu ke nuni da jajircewar gwamnati wajen daukar matakan kare muhalli da dorewar ci gaba.

Hajiya Mohammed ta bayyana cewa ziyarar tata ba wai kawai domin ta’aziyya ba ce, har da zurfafa wayar da kai kan Muradun Ci Gaba Mai Dorewa, da kuma karfafa hadin gwiwa da jihar Kano.

Ta sanar da gwamnan game da babban taron Kasuwanci da Zuba Jari na Majalisar Dinkin Duniya da ke tafe, tare da nuna godiya bisa dagewarsa wajen karfafa mata, samar da ayyukan yi, da kare muhalli.

A nasa jawabin , Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa a shirye jiharsa take ta hada gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya musamman a fannonin ilimi, lafiya, sauyin yanayi, samar da makamashi, kare muhalli da kuma zuba jari mai dorewa.

Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaba da za su inganta rayuwar al’ummar Kano da kuma bada gudunmawa ga kokarin ci gaban duniya.

 

 

Abdullahi Jalaluddeen

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
  • Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa
  • Trump ya fitar da Amurka daga UNESCO saboda amincewa da  Falasdinu a matsayin Mamba
  • Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
  • PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
  • Manoma A Kaduna Sun Yabawa Irin Masara Na TELA Saboda Juriyarshi Ga Kwari
  • Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
  • Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar