Iran Zata Wallafa Tsokacinta Kan Rahoton Babban Daraktan Hukumar IAEA Kan Kasarta
Published: 7th, June 2025 GMT
Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta wallafa tsokacinta kan rahoton babban darartan Hukumar IAEA ga kwamitin gwamnonin hukumar
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da ra’ayoyinta da tsokacinta kan sabon rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnonin hukumar ta IAEA a ranar 24- wannan shekara ta 2025.
A cewar cibiyar diflomasiyya da ta yada labarai ta hukumar makamashin nukiliya ta Iran, an fitar da bayanin mai taken “Sa ido da Tabbatarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 (2015)” a ranar 31 ga Mayu, 2025.
Bayanin ya fayyace cewa: Rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnoni mai taken: “Sabbin da tabbatarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa ga kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2231 (2015)”.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana son bayyana ra’ayoyinta da tsakacinta kan rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnonin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Jamhuriyar Musulunci ta Iran makamashin nukiliya ta ga kwamitin
এছাড়াও পড়ুন:
Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa.
Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Laraba, ya ce yayin da ake fama da yanayi mai sarkakiya, da sauye-sauye masu maimaituwa daga ketare, cinikayyar waje ta Sin na gudana lami lafiya, cike da karfin juriya da babban karsashi.
Hakan a cewarsa, ya shaida gazawar yakin haraji da cinikayya wajen girgiza fifikon da Sin ke da shi, a fannin raya masana’antun sarrafa hajoji da kasar ta gina a tsawon lokaci. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp