UNICEF ya yi gargadi game da tabarbarewar matsalar jin kai a Gaza
Published: 8th, June 2025 GMT
Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadi game da tabarbarewar matsalar jin kai a zirin Gaza da Isra’ila ke ci gaba da yi wa kawanya.
Kakakin hukumar James Elder ya yi gargadin cewa, yara da dama da ke kwance a asibiti masu fama da matsananciyar yunwa ba za su iya rayuwa a mako mai zuwa ba idan har Isra’ila ta ci gaba da kafar ungulu da ayyukan jin kai a yankin.
A wata hira da yayi da gidan talabijin na Sky News, James Elder ya bayyana mummunan halin da ake ciki a Gaza da kuma sadaukarwar da iyaye mata suke yi don ciyar da ‘ya’yansu.
Wannan lokaci shi ne mafi wahala da mata da yara suka taba fuskanta a Gaza inji shi.
Ya ba da shaida ga yadda ya gamu da yaran da ke kwance a asibiti, wadanda rayuwarsu ke fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki.
Rahotanni daga kungiyoyin da ke da alaka da Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomin jin kai sun bayyana lamarin da mai ban tsoro.
Kungiyoyin ba da agaji sun yi gargadin cewa, idan ba a dage shingen da Isra’ila ta yi ba nan ba da jimawa ba, al’ummar kasar na cikin hadarin fadawa cikin wani bala’in jin kai da ba a taba gani ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara
Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya.
A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai dubban ƙananan yara da gwamnati ta rufe su ba kuma tare da cikakken bayani ga iyalansu ba, wasu ma a yanzu babu cikakken bayani kan inda suke ko kuma halin da suke ciki.
Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar MajalisaAsusun ya ce a Nijeriya rufe ƙananan yara tare da yi musu shari’a ta zalunci ba bisa ƙa’ida ba na ƙara zama ruwan dare matakin da ke jefa yara cikin fargaba.
Rahoton ya ce wannan matsala ta nuna ƙarara yadda rayuwar yara ƙanana ke cikin haɗari da kuma yadda ake da ƙarancin kotuna da kuma gidajen tsare ƙananan yara.
UNICEF ɗin ya ƙara da cewa ana gwamutsa yaran a gidajen yari da manyan masu laifi sakamakon ƙananan laifuka da suka aikata abinda ke gurɓata tunaninsu a lokuta da dama kuma suke koyon wasu laifukan masu girma.
Rahoton ya ci gaba da cewa a bayanan da ya tattara a tsakanin shekarar 2018 da 2022 sama da mutane 87 ne ake tsare da su a gidajen yari haka siddan ba tare da sanin makomarsu ba, sai kuma ƙananan yara 1,279 da ake tsare da su wasu ma ba’a san inda suke ba.
Asusun ya gano cewa mafi yawan waɗannan mutane sun shafe sama da shekaru 5 a gidajen yarin, ba tare da an yanke musu hukunci ba.