Iran Tace Amurka Tana Ci Gaba Da Amfani Da Karfi Inda Bai Dace Ba A Duniya
Published: 9th, June 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghae ya bayyana cewa gwamnatin kasar amurka tana amfani da karfi inda bai dace ba a duniya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Baghae yana fadar haka a jiya Lahadi. Ya kuma kara da cewa gwamnatin Amurka tana amfani da kujerar VETO a kwamitin tsaro na MDD don hana tsagaita wuta da kuma dakatar da kissan kiyashi a gaza, sannan ta yi amgani da takunkuman tattalin arziki kan alkalai da Jami;an kotun ICC wadanda suke aikinsu na tabbatar da adalci a duniya.
Kakakin ma’aikatar ya kara da cewa lokaci yayi wanda kasashen duniya zasu tashi don kawo karshen wadannan mummunan halayen gwamnatin Amurka wadanda suke girgiza asasin dokokin kasa da kasa don hana ci gaba da zaman lafiya a duniya.
Sannan daga wannan zamu fahinci cewa gwamnatin kasar Amurka tana da hannu dumu-dumi a kissan kiyashin da ke faruwa a gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Kama Wata Mata Da Take Shirin Kashe Benjemin Netanyahu
Kafafen watsa labarun HKI sun ambato hukumar leken asiri ta “Shabak’ tana sanar da kame wata mace, dake zaune a tsakiyar wannan haramtacciyar kasa bayan da aka tuhumeta da Shirin kashe Fira minister Benjamin Netanyahu.
‘Yan sandan HKI sun ce, matar da aka kama ta so yin amfani da abubuwa masu fashewa da ake kerawa da hannu ( IDE), kuma a halin yanzu Shabak tana gudanar da bincike.