Wang Yi Ya Gana Da Sabon Jakadan Amurka A Sin
Published: 4th, June 2025 GMT
A nasa bangare kuma, David Perdue ya ce, shugaba Donald Trump yana matukar girmama shugaba Xi Jinping, kuma yana da muhimmanci a ci gaba da karfafa mu’amala dake tsakanin shugabannin biyu. A matsayin jakadan kasar Amurka a kasar Sin, yana fatan yin mu’amala da bangaren Sin yadda ya kamata, bisa ka’idar girmama juna, da sauraron ra’ayoyin juna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Manoma A Kaduna Sun Yabawa Irin Masara Na TELA Saboda Juriyarshi Ga Kwari
Manoma a Jihar Kaduna sun bayyana gamsuwarsu da yadda iri na TELA Hybrid Maize daga kamfanin EcoBasic Seeds ke samar da amfanin gona ba tare da amfani da maganin kwari ba.
Sun bayyana hakan ne a Jaji, Jihar Kaduna, lokacin da ‘yan jarida suka kai ziyara gonakin gwaji da kamfanin EcoBasic Seeds ya kafa.
Wani daga cikin manoman, Mallam Sabitu Abdullahi, ya bayyana Irin Masara na TELA Hybrid a matsayin masara mai ban mamaki, yana cewa tana bada amfanin gona mai yawa da kuma girbi cikin kwanaki 70 kacal.
“Idan duka manoman Najeriya suka rungumi wannan iri, zai taimaka wajen tabbatar da wadatar abinci a kasa,” inji shi.
Ya ce ya shafe shekaru uku yana amfani da irin Masara TELA a gonakin gwaji, kuma ba su yi nadama ba.
“Ina noma don cin abinci ne da siyarwa. Mun yi tuwo da ita kuma lafiyayya ce,” ya kara da cewa.
Sabitu ya bayyana cewa ya dasa irin SAMMAZ 75 T a gonarsa, wanda kuma za a iya sake dasa shi. Ya shawarci sauran manoma su rungumi irin Masara na TELA, tare da bukatar su sayi iri tun kafin damina mai zuwa.
Ya koka da cewa kafin zuwan irin Masara na TELA, manoma a Najeriya na fama da asarar amfanin gona saboda fari, kwari irinsu stemborer da sauran su, amma yanzu sun fara cin gajiyar karin amfanin da ya kai kashi 30 cikin 100.
Haka zalika, matarsa, Aminat Sabitu, wata manomiya, ta ce ta shiga harkar noma tare da mijinta bayan ganin irin yawan amfanin da irin Masara na TELA Maize ke bayarwa.
“Tun da muka fara amfani da irin Masara na TELA, muna samun buhuna 22 daga filin da muke samun buhuna 10,” inji ta, tana mai cewa irin na da juriya ga fari kuma yana karɓar taki sosai.
Ta bukaci kungiyoyin mata su fito su fara shuka irin Masara na TELA, tana tabbatar musu ba za su yi nadama ba.
Isma’il Shaibu, matashi mai shekara 27 da haihuwa, ya bayyana cewa irin Masara na TELA Maize ita ce masarar da ta fi dacewa.
“Da can ina samun buhuna 7, amma yanzu ina samun 13 daga fili ɗaya. Ba sai mun feshi da maganin kwari ba, saboda wannan iri yana da juriya,” inji shi.
Ya kara da cewa kafin su gwada TELA suna da ra’ayi mara kyau a kanta, amma tun da suka fara amfani da ita, suka cigaba da nomanta.
A wani bangare, Saleh Ahmadu da aka hangosu yana shara a gonarsa, ya ce ya shafe fiye da shekaru 20 yana noma amma bai taba ganin irin TELA Maize ba.
“Kwari ba su cika cin ganyenta ba, kuma tana bada yawan amfanin gona. Idan wani iri zai baka buhuna 5, wannan zai baka sau biyu daga fili ɗaya,” ya bayyana.
Cov: Adamu Yusuf