Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus
Published: 5th, June 2025 GMT
Da safiyar yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Belarus Aleksandr Lukashenko a nan birnin Beijing. Yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya sake taya takwaran nasa na Belarus Aleksandr Lukashenko murnar nasarar yin tazarce.
Xi ya ce, Sin na daukar huldar sassan biyu da muhimmanci, kuma tana raya ta bisa hangen nesa kan manyan tsare-tsare, tare da fatan kara hadin gwiwa da Belarus, don gaggauta bunkasa huldarsu, da ma cimma moriya tare cikin hadin gwiwa.
A nasa bangare kuwa, mista Lukashenko ya ce, wannan ne karo na 15 da yake gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, kuma a ko wane karo yana kara fahimtar dankon zumunci dake tsakaninsu. Ya ce Belarus na matukar godiya bisa daddaden taimakon da Sin ke bayarwa gare ta, yana mai fatan raya huldar kasashen biyu ba tare da tangarda ba, da ma gaggauta hadin gwiwarsu a mabambantan bangarori. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.
“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA