Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Amurka Da Isra’ila Suna Da Mugun Nufi Kan Iran Da Kasashen Musulmi
Published: 4th, June 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suna da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi.
A yayin wani jawabi da ta gabatar a wajen juyayin tunawa da rasuwar Imam Khumaini {r.
Pezeshkian ya kara da cewa: Wadanda ke da’awar kare hakkin bil’adama suna kare “haramtacciyar kasar Isra’ila” mai laifi, kuma suna ci gaba da adawa da shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Ya ci gaba da cewa: “Babu mutum mai ‘yanci da zai yarda da zalunci da girman kai, kuma Iran ba zata yarda da shi ba.”
Pezeshkian ya bayyana cewa: “Za su dakile duk wani makirce-makircen abokan gaba kuma ba za su taba yin watsi da ‘yancinsu na nukiliya da na kimiyya ba.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Isra ila Pezeshkian ya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana cewa aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, a karshen kogin Yarlung Zangbo, aiki ne dake bisa ikon mallakar kasar Sin, kuma Sin din tana raya aikin don gaggauta samar da makamashi mai tsabta, da kyautata zaman rayuwar jama’ar wurin, da kuma tinkarar sauyin yanayi.
Guo ya ce, kasar Sin ta mai da hankali, da sauke nauyin dake wuyanta na amfani da albarkatun kogin da ya ratsa bangarenta da ma kasashen waje, kana tana da fasahohin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa. An tsara aikin ne a kan karshen kogin Yarlung Zangbo bisa ma’aunin Sin mai nasaba da aiki, da gudanar da aikin tare da kiyaye muhalli, da magance aikin a muhimman wuraren halittu don tabbatar da tsarin yanayin wanzuwar halittu. An gina tashar don magance bala’i a kan kogin, ta yadda aikin ba zai yi wata illa ga yankin karshen kogin ba.
Guo Jiakun ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yi hadin gwiwa tare da kasashen dake kan karshen kogin a fannonin sanar da yanayin kogin, da magance bala’i, da yaki da bala’i da sauransu, da kuma yin mu’amala da kasashen don ci gaba da yin hadin gwiwa da su, da kuma kawo moriya ga jama’arsu baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp