Iran ta ce a shirye take ta shiga tsakani a kokarin samar da zaman lafiya tsakanin Pakistan da Indiya
Published: 8th, June 2025 GMT
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya bayyana shirin kasarsa na samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasaahen Pakistan da Indiya.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a ranar Asabar.
Shugaban na Iran ya ce manufar Iran ta mayar da hankali ne kan inganta samar da zaman lafiya a duniya musamman a cikin kasashen musulmi.
Ya kara da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana maraba da duk wani mataki da kokarin samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Pakistan da Indiya, kuma za ta iya taka rawar shiga tsakani ga wannan manufar.”
A nasa bangaren firaministan kasar Pakistan ya mika sakon gaisuwar babba salla da sakon fatan alheri ga al’ummar Iran da kuma jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
Sharif ya kuma bayyana fatan ganin an aiwatar da yarjejeniyoyin kasashen biyu da Pakistan da Iran suka kulla.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: samar da zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Ganyayyaki Ke Yi Wa ‘Yan Najeriya Wahala
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Karancin kayan ganyayyaki na cigaba da barazana ga lafiyar ‘yan Najeriya.
Masana sun bayyana cewa akwai gibi mai girma na rashin kayan ganyayyaki da ya kamata cike.
Sai dai hakan na fuskantar tasgaro sakamakon wasu dalilai.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan matsala da zummar nemo hanyoyin magance ta.
Domin sauke shirin, latsa nan