2025-07-23@07:40:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4754
«Zaman lafiya»:
Amurka ta yanke shawarar ficewa daga hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a karo na biyu saboda matakin da ta dauka na shigar da Falasdinu a matsayin mamba. Mataimakiyar sakatariyar yada labaran fadar White House Anna Kelly ta sanar da matakin a cikin wata sanarwa a ranar Talata....
Wata sabuwar tashin-tashina ta sake kunno kai a yankin kahon Afirka a daidai lokacin da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya yi gargadi kai tsaye ga firaministan Habasha Abiy Ahmed, inda ya yi kashedin sake kaddamar da wani yaki. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Habasha ke kokarin shiga bangaren ruwa...
A cewar Ringim, idan ana so a sami cigaban da ya shafi kowa da kowa a Arewacin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, to ana buƙatar siyasa irin ta Kwankwaso wadda ke mayar da hankali kan talakawa da gaskiya a mulki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa. Sanarwar ta bayyana cewa bikin...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya...
Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi ta yanke hukunci a kan gwamnatin jihar Bauchi da ta biya tsohon Akanta-Janar na jihar, Dakta Sa’idu Abubakar, Naira miliyan 100 a matsayin diyyar take masa haƙƙi da kuma tsare shi ba bisa ƙa’ida ba. Kotun ta kuma umarci gwamnati ta wallafa ban haƙuri a manyan jaridu guda biyu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen killace yankin Gaza da aka yi, da kuma wajabcin kai musu abinci da magunguna. Kungiyar malaman musulmin ta kuma bayyana abinda HKI take yi na killace mutanen Gaza fiye da...
Yar wasan gaba ta Nijeriya, Chinwendu Alozie, ce ta tabbatar da nasara da kwallon da ta jefa kafin tashi daga wasan. Wannan nasara ta ba wa tawagar ta Justin Madugu damar kaiwa wasan ƙarshe na gasar. Yanzu haka, Super Falcons za su kara da ƙasar da za ta yi nasara tsakanin Moroko, wacce ke...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Batun kare hakkin bil’adama da ake yi a duniya ba komai ba ne sai karya. Shugaba Fizishkiyan ya yi ishara da yadda masu ikirarin kare hakkin bil’adama suke sa kafafunsu suna take hakkin mutanen Gaza da cikin kasashen yammacin Asiya da kuma tafka manyan laifuka. A yau...
Fira ministan HKI wanda kotun duniya ta manyan laifuka take nem ruwa a jallo ya bayyana cewa; Babu yadda za su tsayar da yakin Gaza, matukar kungiyar Hamas ba ta mika wuya baki day aba. Benjemine Netanyahu ya kuma ce; A lokacin da Hamas za ta mika makamanta ne, shi ne za mu yi tunanin...
Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai...
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani...
Yuro biliyan 4 Yen biliyan 15 (na Japan) Tallafin dala miliyan 65 Kuma aron cikin gida ta hanyar sayar da hannun jarin gwamnati (bond) na kusan Naira biliyan 757. Har ila yau, akwai shirin tara kuɗi har dala biliyan 2 ta hanyar takardun lamuni da za a fitar cikin ƙasa amma a kuɗin ƙetare. Shugaban...
Su kuwa mahalarta taron, sun yaba da kyautatuwar dangantakar kasashen biyu da rawar da SCO ke takawa. Sun kuma bayyana fatan Masar da Sin za su yi amfani da damarmakin ci gaba da SCO ta samar domin su hada hannu tare, su inganta tsarin jagorantar harkokin duniya da farfadowar kasashe masu tasowa. (Mai fassara: Fa’iza...
Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga...
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar. Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100...
Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati. Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan...
Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati. Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan...
Gwamnatin ƙasar Guinea ta rufe wasu sassan kamfanoni guda 1,724 sakamakon kama su da laifin ƙin bin dokokin hukuma, yayin da aka janye kayayyakin da suke sarrafawa daga kasuwa. Sanarwar na zuwa ne ƙarƙashin ma’aikatar kasuwanci a ƙasar, tana mai cewa an ɗauki matakin ne don kare lafiyar masu sayen kayayyakin da kuma tabbatar da...
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tashin farashin takin zamani yana hana manoma da dama noman wasu nau’ukan abinci. Manoma da dama sun ƙaurace wa noman masara da shinkafa da aka fi amfani da su a Najeriya sakamakon tsadar takin zamani, abin da masana ke ganin in ba a ɗauki mataki ba, hakan zai...
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a tsananta hukunci kan masu cin zarafin ’ya’ya mata, yana mai cewa babu wani musulmi nagari da zai yi wa matarsa dukan da har zai yi mata lahani. A yayin da yake tunatar da malamai da limamai kan muhimmiyar gudunmawar da za su bayar a wannan...
Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa yunwa na ƙara tsananta a Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe. A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa. Mutum 16...
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta sanar da cewa a ’yan kwanakin nan za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a wasu jihohi da ke sassa daban-daban na ƙasar. Hakan na kunshe cikin hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025 da hukumar ta fitar....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce PDP ce kaɗai ke da ƙarfin gina ƙasa. “Wannan gwamnati ce da ke cewa mutane su yi azumi alhali su suna cin abinci sannan suna jin daɗi. Babu ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa ko wata jam’iyya mai jin zafin halin da mutane ke ciki da za ta goyi bayan Tinubu a 2027. Gwamnatinsa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.” “Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!” A ranar 20 ga wata, an rufe...
Manoma a Jihar Kaduna sun bayyana gamsuwarsu da yadda iri na TELA Hybrid Maize daga kamfanin EcoBasic Seeds ke samar da amfanin gona ba tare da amfani da maganin kwari ba. Sun bayyana hakan ne a Jaji, Jihar Kaduna, lokacin da ‘yan jarida suka kai ziyara gonakin gwaji da kamfanin EcoBasic Seeds ya...
An shawarci mata da su daina amfani da tsumma ko soson katifa, da takarda a lokacin al’adar su don inganta tsafta da rigakafin matsalolin lafiya. Jami’ar tallafawa masu kula da tsaftar jinin haila a jihar Kano (MH-NoW) Amina Sabiu Musa ta yi wannan kiran ne a lokacin wani taron karawa juna sani na tsaftar...
Jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman a cire su daga shirin bayar da gudunmawar fansho (CPS). An ga jami’an ‘yan sandan da suka yi ritaya a jihar karkashin kungiyar ‘yan sandan Najeriya mai ritaya (ARPON), dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar su...
Gwamnatin Libya ta tasa keya daruruwan baƙin haure ‘yan ƙasar Sudan 700 zuwa ƙasarsu da yaƙi ya ɗaiɗaita, A cewar mahukuntan, waɗannan mutanen sun yi hijira zuwa Libya ne domin gujewa yaƙi da talauci, inda suke neman hanyar tsallakawa zuwa Turai. A cewar huƙumar kula da baƙin haure, an kori mutane 700 daga Libya da...
Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen inganta ci gaban zamantakewar al’umma da kuma tallafawa aiwatar da Muradun Cigaba mai Dorewa (SDGs). Hajiya Amina Mohammed ta kai ziyara Jihar Kano ne domin yin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar...
Jami’in harkar shari’ar kasa da kasa ya bayyana cewa: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhu Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya ce: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne, kuma jarrabawa ce...

Birgediya Janar Sabahi Fard Ya Jaddada Cewa: Duk Wani Sabon Hari Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Gauni
Kwamandan rundunar hadin gwiwar hedikwatar tsaron saman Iran ya jaddada cewa: Duk wani sabon kuskure da ‘yan sahayoniyya suka aikata zai haifar da mummunan sakamako Kwamandan rundunar hadin gwiwar hedikwatar tsaron saman Iran kuma kwamandan bataliyar Khatam al-Anbiya (s.a.w) Birgediya Janar Alireza Sabahi Fard, ya jaddada cewa: Duk wani sabon kuskure da yahudawan sahayoniyya za...
Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da...

Mataimakin Shugaban Kasar Iran Na Farko Ya Jaddada Wajabcin Damawa Da Kowane Bangare A Fagen Jagorantar Kasar Iran
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya jaddada cewa; Ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa akan fagen yadda al’amura zasu karfafa Mataimakin shugaban kasar na farko na kasar Iran Mohammed Reza Aref ya bayyana cewa: Babu wani bambanci tsakanin diflomasiyya da fannin, inda ya ce har yanzu ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa kan hanyoyi kyautata gudanar...

Mamba A Kwamitin Tsaron Kasar Iran Ya Ce; Nan Gaba Iran Zata Zama Cikin Sahun Manyan Kasashen Duniya
Mamba a kwamitin tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata zama daya daga cikin manyan kasashen duniya Ala’uddin Boroujerdi mamba a kwamitin tsaron kasa da manufofin kasashen waje na majalisar shawarar Musulunci ya bayyana cewa: Kisan gillar da aka yi wa fitattun malamai irin su Shaheed Tehranji ba zai kawo cikas...
Ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana alfahari da rusa Gaza da tarwatsa mazauna yankin! Isra’ila Katz, ministan yakin gwamnatin mamayar Isra’ila, ya wallafa wani hoto da ya nuna yadda aka lalata garin Beit Hanoun a arewacin zirin Gaza, yana mai alfahari da yadda aka rusa gine-ginen garin”. Kuma ta hanyar dandalin “X”, Kats yayi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanata Yemi Adaramodu, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, ya ce matsalar tsaro a Najeriya na raguwa, kuma tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa. Ya yaba da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda. Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila WFP ya dakatar da tallafin abinci...
Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ’yan siyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Nijeriya. Ya bayyana cewar haɗaka ’yan adawar za ta taimaka wajen hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal. WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka Za a sa zare tsakanin...
Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea...
Benyamin Natanyahu firai ministan HKI ya amince da cewa gwamnatinsa ta kashe masana fasahar Nukliya na kasar Iran da dama, don haka kasar ci gaba a wannan bangaren. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Amurka mai sun a FOX NEWS....
A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, Usman Dako ya bayyana yadda aka kori iyalinsa, aka rusa gidansu, aka kuma tsorata matarsa da ‘ya’yansa. Ya ce gida ne da aka ware wa mahaifinsa tun zamanin marigayi Sarki Ado Bayero, amma yanzu an rusa shi ba tare da haƙƙi ba. Dako ya dage da...
Kakakin ma’aikatar sharia a nan Iran ya bayyana cewa shi bai da wata masaniya dangeneda cewa HKI ta kai hare-hare kan gidan yarin Evin na Tehran ne don kashe ma’aikatanta da aka kama aka kuma tsare a gidan yarin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin na ma’aikatar sharia yana fadar haka...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana hukumar kula da shige da fice ta Najeriya a matsayin matakin farko na tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi a kasar. Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin daliban jami’ar Immigration da ma’aikatan kwalejin Sokoto a ziyarar ban...
Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea...
A cikin wannan mako dai an yi ta murna da farin ciki a fadin jihar Kano inda dubban ‘yan fansho suka fara karbar kudaden fansho da garatuti da aka dade ba su yi ba. Kudaden da aka fitar na ‘yan fansho na jihar Kano, sun kasance wani babban ci gaba a kokarin da...