A cikin sanarwar da dukkan bangarorin da suka halarci taron suka sanya wa hannu, an amince da cewa, kungiyar za ta ba da wata guda domin tattauna bukatun JUSUN.

 

Wani bangare na yarjejeniyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta saki kudaden da suka wajaba ga bangaren ma’aikatan shari’a a cikin wannan watan.

 

Sanarwar ta jaddada cewa, da zarar an fitar da kudaden, dole ne a aiwatar da duk wasu bukatu da kungiyar ta JUSUN ta gabatar ba tare da bata lokaci ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare

Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).

A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.

Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.

A cewarsa, an zabo daliban 12 ne  sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.

Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.

“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.

Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.

A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.

Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja
  • Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250  a Jami’ar Ilorin