Wang Yi Ya Nanata Matsayin Taiwan Yayin Tattaunawa Da Takwaransa Na Faransa
Published: 8th, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya nanata matsayin Taiwan da jaddada manufar Sin daya tak a duniya yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a jiya Jumma’a. Ya kuma bayyana adawar Sin da shigar kungiyar tsaro ta NATO cikin harkokin yankin Asiya da Pasifik.
Wang Yi wanda mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya nanata cewa, batun da ya shafi Taiwan, batu ne na cikin gidan Sin da ya shafi ’yancin kasar da iko kan yankunanta, wanda ya bambanta da batun kasar Ukraine.
Bugu da kari, ministan ya bayyana fatan Sin na ganin Faransa ta rike matsayin da ya dace da adawa da shigar NATO cikin harkokin Asiya da Pasifik tare da jaddada cewa, ya kamata kasashen biyu su inganta cudanyar bangarori daban daban da kare tsarin ciniki cikin ’yanci da adawa da ayyukan cin zali.
A nasa bangare, Jean-Noel Barrot ya ce Faransa za ta ci gaba da daukar Sin a matsayin kawa kuma abokiyar hulda, da nace wa manufar Sin daya tak tare da sa ran ci gaba da aiwatar da musaya tsakanin manyan jami’ansu da tuntuba ta kut da kut bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da Sin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Manchester City Ta Kammala Daukar Rayan Cherki Daga Lyon
Cherki ya buga wasansa na farko a Lyon yana da shekara 16 a watan Oktoban 2019 kuma ya bar kungiyar inda ya ci kwallaye 29 sannan ya taimaka aka jefa 45 a wasanni 185 da ya bugawa kungiyar ta Faransa. Cherki ya wakilci kasar Faransa kuma ya lashe lambar azurfa a gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa a bara.
Daraktan kwallon kafa na Manchester City, Hugo Viana ya ce, “Babu shakka a yanzu Cherki yazo inda ya dace kuma zai cigaba a karkashin jagorancin Guardiola, kuma na yi imani zai iya zama babban dan wasa a duniya tare da goyon bayan abokan wasa da masu horarwa”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp