Kasar Rwanda Ta Fice Daga Cikin Kungiyar Tattalin Arziki Ta Tsakiyar Afirka
Published: 9th, June 2025 GMT
A daidai lokacin da kungiyar kasashen tsakiyar Afirka ta tattalin arziki ( ECCAS) take yin taro, kasar Rwanda ta sanar da ficewa daga cikinta.
Bayanin da gwamnatin kasar ta Rwanda ta fitar ya kunshi cewa; Kasar Rwanda tana nuna takaicinta akan yadda kasar DRC take amfani da kungiyar tattalin arziki ta tsakiyar Afirka a matsayin wani makamin a hannunta.
Bayanin gwamnatin ta Rwanda ya kara da cewa: Yadda DRC take amfani da wannan kungiyar ya sake fitowa fili a yayin taron kungiyar karo na 26 a Malabo, ta yadda aka kau da kai akan hakkin Rwanda na shugabancin karba-karba,kamar yadda yake a cikin doka ta shida ta kundin kungiyar. Hakan kuma ya faru ne sanadiyyar shiftar DRC ga kungiyar.”
A yayin da aka shirya cewa a shekara mai zuwa kasar ta Rwanda za ta karfi shugabancin kungiyar, jami’an kasar DRC sun ce, ba za su sami halartar taron da za a yi a kasar ta Rwanda ba.
Kasashen biyu dai suna zaman tsami bisa zargin da Kinshasa take yi wa Kigali na cewa tana goyon bayan kungiyar ‘yan tawaye ta M23.
Yanzu dai kungiyar ta ECCAS tana da mamabobi 11 bayan ficewar kasar Rwanda. Kasashen su ne: Angola, Burundi, Cameroon, Afirka Ta Tsakiya,c, Congo, Gabon, Equatorial Guinea, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Rwanda, Sao Tome, sai tsibirin Principe da Chad.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Rwanda
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Tace Tawagar Kwararru Daga Hukumar IAEA Zata Ziyarci Kasar Nan Ba Da Dadewa Ba
Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da daewa ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka.
Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin kasar Iran kan yadda mu’amalar hukumar zata kasance da Iran. Gharibabadi ya bayyana cewa idan kasashen yamma sun yi kokarin amfani da shrin SnapBack na yarjeniyar JCPOA zasu gamu da maida martani mai tsanani, sannan ya kara da cewa mu’amala da hukumar IAEA da kasar Iran zata sauka saboda amfani da karfi kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran wanda Amurka da HKI suka yi a kallafeffen yaki na kwanaki 12 a cikin watan yunin da ya gabata.
Mataimakin ministan ya bayyana cewa, Iran zata ci gaba da kasancewa cikin yarjeniyar NPT mai hana yaduwar makaman nukliya a duniya. Amma dokar da Majalisar dokokin kasar Iran ta kafa ta jingine hulda da hukumar IAEA ya sa Iran za ta sanya hulda da hukumar takaitacce shi dimma tare da wasu sharudda guda biyu. Gharib abada ya fadawa yan jaridu a birnin NewYork a ranar Laraban da ta gabata kan cewa tawagar ba zata kai ziyara cibiyoyin makamashin nukliya na kasar ba. Sannan ya kammala da cewa hukumar makamashin nukliya na kasar Iran na lissafin irin asarorin da hare-hare Amurka suka yiwa cibiyoyin Nuklkiyar nkasar A Esfahan, Natansa da kuma Fordo.