Araghchi : Babu wata tattaunawa idan ba zamu tace uranium ba
Published: 5th, June 2025 GMT
Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake tabbatar da cewa Iran ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba kan ‘yancinta na tace Uranium, yana mai cewa ci gaban da kasar ta samu a fannin makamashin nukiliya ya samo asali ne sakamakon sadaukarwa da kuma saka hannun jari na kasa.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya ce, ba batun inganta makamashin Uranium a duk wata yarjejeniyar nukiliya da za a yi nan gaba.
“Iran ta saka kudi da yawa domin kai wag a wannan mataki, sannan kuma ba zai sa mu yi watsi da sadaukarwar da ‘yan kishin kasa sukayi don tabbatar da burinmu.
Araghchi ya bayyana tace uranium a matsayin wani sakamako na ilimi da fasaha, mahimman abubuwan da suka ba Tehran damar habaka fasahar nukiliya cikin lumana duk da takunkumin shekaru da matsin lamba na kasa da kasa.
Yayin da yake bayyana matsayin Iran a tattaunawar da Amurka, ya kara da cewa: “Babu wata yarjejeniya idan ba zamu tace uranium ba, amma zamu iya cimma yarjejeniya wacce ta tanadi hana mallakar makamin nukiliya.”
Ya zuwa yanzu dai Iran da Amurka sun gudanar da jerin tattaunawa har sau biyar da nufin maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Za Ta Kara Yawan Sanadarin Urani’um Da Take Tacewa A Wuri Na Sirri
A wani bayani na hadin gwiwa da hukumar makamashin Nukiliya ta Iran da kuma ma’aikatar harkokin wajen Iran su ka fitar, sun bayar da umarnin a bude wani wuri na daban na sirri domin ci gaba da tace sanadarin Urani’um, sannan kuma a maye gurbin bututu tace sanadarin mai mataki na daya, da mai mataki na shida a cibiyar “Pardo.”
Bayanin dai ya zo ne a matsayin mayar da martani ga sanarwar da ta fito daga kwamitin alkalai na hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa akan Iran.
Bugu da kari, bayanin na Iran ya kuma ce; A kodayaushe jamhuriyar musulunci ta Iran tana aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta, kuma har ya zuwa yanzu babu wani rahoto na hukumar wanda ya bayyana cewa; Iran ba ta aiki da ka’idojin hana yaduwar makaman Nukiliya.”
Haka nan kuma bayanin ya ambaci cewa; Tare da cewa Iran tana daukar rahoton da cewa na siyasa ne, wanda Amurka da kasashen turai suke amfani da hukumar a matsayin makami, ba tare da dogaro da wani dalili na ilimi ba.
Har ila yau Iran din ta zargi Amurka da kasashen na turai da wuce gona da iri wajen tsara rahoton da yake cin karo da rahoton da shugaban hukumar ta makamashin Nukiliya ya fitar, wanda bai sami wani abu mai shiga duhu ba a cikin Shirin na Iran na zama lafiya.