Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai
Published: 5th, June 2025 GMT
Kasar Sin ta ci gaba da yin tsayin daka kan matsayinta na guje wa yin katsalandan musamman a Afirka. Ba kamar kasashen yammacin duniya da suka tsunduma cikin harkokin soji da makamai ba, kasar ta mai da hankali kan hadin gwiwar tattalin arziki, kamar zuba jari mai yawa a kasashen Afirka da dama ba tare da gindaya sharuddan siyasa ba.
Kazalika, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sulhunta rikici a yankin Asiya, inda ta samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici da juna maimakon samar da mafita ta hanyar karfin soja. Sulhunta tsakanin Saudiya da Iran a shekarar 2023, tare da daidaita harkokin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu babban misali ne. Wannan nasarar ta nuna hikimar da kasar Sin ke da ita ta sasanta rikice-rikice masu sarkakiya a matakin yanki ba tare da tilastawa ko kuma matsin lamba ta fuskar soja ba. Sabanin Amurka wacce ake suka bisa dama lissafi da kara zaman dar-dar, musamman a yankin Asiya da tekun Pasifik, ta hanyar kawancen soji da sayar da makamai.
Kasar Sin da gaske take yi kan batun zaman lafiya a duniya, domin yayin da Amurka kullum ke tunanin fadada sansanoninta na soji, ita kuwa ta fi mayar da hankali ne wajen sabuntawa da karfafa rundunonin sojinta don kiyaye tsaron kanta da ikon mallakar yankunanta. Ba kamar Amurka ba, wacce ke daukar dawainiyar sansanonin soji birjik a duniya da a ko yaushe ake zarginsu da haddasa husuma a yankuna.
Ba wai kawai a doron kasa ba, hatta ci gaban da ake samu na bincike a sararin samaniya Amurka ta mayar da shi ta fuskar soji, duk kuwa da gargadin da ake ta yi cewa hakan zai haifar da gasar makamai da kara tabarbarewar tsaro a duniya. A nata bangaren, kasar Sin jaddada hadin gwiwar kimiyya ta yi, kamar samar da tashar binciken sararin samaniya ta Tiangong, wadda ke maraba da hadin gwiwar kasa da kasa. Wannan ma ya bambanta da kafa rundunar sararin samaniyar da Amurka ta yi, wadda ke nuni da mayar da lamarin ta fuskar soji.
Akidar Sin ta yin hadin gwiwar tattalin arziki, da sulhuntawa a fannin diflomasiyya, sun ba ta damar ci gaba da yin suna a matsayin mai tabbatar da zaman lafiya a harkokin duniya. Yayin da Amurka kuma ke ci gaba da yin tasiri ta hanyar kawancen soja da yin katsalandan ga sauran kasashe. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: hadin gwiwar
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata.
Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata 22 ga watan Yuli 2025, aka gudanar da taron tawagogin kasashen uku.
Mahalarta taron a karkashin inuwar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, sun tabbatar da aniyar kasashensu na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da yin musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar.
Sun kuma jaddada muhimmancin ci gaba da wannan shawarwari domin biyan muradun kasashen uku wajen tinkarar manufofin kasashen yamma, musamman takunkuman Amurka.
Tawagogin sun amince su ci gaba da bude hanyoyin karfafa alakokinsu da kuma ci gaba da gudanar da taruka a nan gaba a matakai daban-daban a cikin makonni masu zuwa, a wani bangare na abin da suka bayyana da “kokarin hadin gwiwa na tallafawa zaman lafiyar yankin da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.”