Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Hakkin Iran Na Tace Sinadarin Uranium
Published: 4th, June 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium shi ne mabuɗin batun nukiliya, don haka Iran ba zata taba yin watsi da shi ba
A jawabin da ya gabatar a safiyar yau Laraba, a daidai lokacin da ake cika shekaru 36 da wafatin jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khumaini (Allah ya jikansa), Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a matsayin martani ga shawarar Amurka, ya jaddada cewa inganta sinadarin Uranium shi ne mabudin batun nukiliya, kuma ba za su taba yin watsi da shi ba.
A wajen wannan juyayi, bayan karatun kur’ani mai tsarki da yabon Ahlul-baiti (a.s) jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da jawabinsa inda ya ce: Kafin ya ce komai, yana mika jinjinarsa ga ruhin Imam mai girma da kuma rokon Allah Madaukakin Sarki da ya daukaka darajarsa.
Jagoran ya kara da cewa: Gobe ne ranar Arafah, kuma mabudin Sallah, don haka yana nasiha ga matasa da yin sallah, su bayyana bukatunsu da manufofinsu ga Allah Madaukakin Sarki, tare da neman taimakonsa.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tsarin siyasarsu wanda alhamdulillahi ya samu ci gaba da karfafa shi ne sakamakon juyin juya hali mai girma, kuma jagoransu mutum ne mai girma wanda har yanzu ake jin kasancewarsa a duniya sama da shekaru talatin bayan wafatinsa, kuma har yanzu tasirin juyin juya halinsa a bayyane yake ga al’ummar duniya, kuma irin koma bayan da Amurka take da samu a duniya yana da nasaba da samuwarsa da kuma kiyayya da juyin juya halinsa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Jagoran juyin juya halin Musulunci
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Kira Ga “FIFA” Da Ta Kori “Isra’ila” Daga Cikinta
Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta aike da sako zuwa ga hukumar kwallon kafa ta duniya da ta kori HKI daga cikinta
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Iran Mahdi Taj, ya bayyana cewa: Mun yi kira ga Sheikh Salman akan daukar kwakkwaran mataki akan ‘Yan Sahayoniya. Mun kuma rubuta wasika zuwa ga Fifa akan cewa ya zama wajibi a dagawa HKI jan kati.
Bugu da kari, ya kuma ce; “Yan sahayoniya sun kai wa hukumar kwallon kafa ta Iran hari, ta kuma kashe mana alkalai, ‘yan wasa, don haka ya zama wajibi a kore su daga Fifa.
Taj ya kuma ce; Mun sami ci gaba sosai a wannan fagen, muna fatan kungiyar Fifa ta yi la’akari da wadannan laifukan na Isra’ila.