Miliyoyim Musulmi A Nan Iran Da Sauran kasashen Duniya Ne Suka Yi Sallar Idin Layyah
Published: 6th, June 2025 GMT
Miliyoyin musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya suka gudanar da sallar Layyah, wanda yake daga cikin manya-manya bukukuwa a cikin addinin musulunci.
Tashar talabijin na Press tv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan sallar wanda maniyya da kuma sauran musulni suke yi ya hada da yanka dabba gwagwadon hali, da kuma raba namansa a tsakanin mabukata musulmi.
Ana son duk musulmi baligi wanda ya ke da lafiya da ikon zuwa Hajja to yayi shi akalla sau
Guda a rayuwarsa.
A Bana dai musulmi kimani 1600,000 suka sauke farali. Mafi yawa daga kasashen waje.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Birgediya Janar Sabahi Fard Ya Jaddada Cewa: Duk Wani Sabon Hari Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Gauni
Kwamandan rundunar hadin gwiwar hedikwatar tsaron saman Iran ya jaddada cewa: Duk wani sabon kuskure da ‘yan sahayoniyya suka aikata zai haifar da mummunan sakamako
Kwamandan rundunar hadin gwiwar hedikwatar tsaron saman Iran kuma kwamandan bataliyar Khatam al-Anbiya (s.a.w) Birgediya Janar Alireza Sabahi Fard, ya jaddada cewa: Duk wani sabon kuskure da yahudawan sahayoniyya za su sake yi, zai haifar da mummunan sakamako.
Birgediya Janar Seyyed Majid Mousavi, kwamandan rundunar sararin samaniyar Iran na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ya ziyarci hedikwatar hadakar tsaron sojojin saman na Khatam al-Anbiya, inda ya tattauna da Birgediya Janar Sabahi Fard, kan sakamakon arangamar da sojoji suka yi a baya-bayan nan da kuma hanyoyin inganta hadin kan tsaro.
A zaman taron, Sabahi Fard ya ce, “Tsarin tsaron saman kasar Iran ya shiga cikin yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan da jajircewa da himma, tare da yin nasara ta hanyar hadin gwiwa da daukar matakin jihadi wajen dakile manufofin makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta musu ja da baya. Ya bayyana karara cewa ci gaba da ta’addancin yana kara ta’azzara halin da ake ciki a cikin yankunan da aka mamaye, musamman a Tel Aviv da Haifa.”
Ya kara da cewa, “Suna dogara da karfin kasa wajen bunkasa na’urar tsaronsu, kuma jinin shahidansu ko daga sojoji ne ko farar hula, ba zai zuba a banza ba. Zai haifar da mummunan tasiri kan ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya. Kisan gillar da aka yi wa masana kimiyyar nukiliya da shugabannin tsaron Iran ba zai hana kasar cimma nasarorin fasaha, soja, da tsaro ba. Maimakon haka, za su yi aiki a matsayin wani gagarumin shiri na yaki da makiya.”