2025-07-25@15:57:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5736
«na gwamnati»:
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, ya karɓi ’yan APC zuwa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano. Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta shafinsa na X, inda ya ce waɗanda suka sauya sheƙar ’yan jam’iyyar APC ne. An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo An kashe mata da yara a sabon harin Filato “Jiya rana ce mai muhimmanci,” in ji shi. “Na karɓi dubban mutane da suka bar jam’iyyar APC suka dawo NNPP.” Ya ce taron ya gudana ne a gidansa da ke Kano, inda ya yi wa sabbin mambobin maraba da kuma alƙawarin adalci da haɗin kai a cikin jam’iyyar. An wallafa hotunan taron a shafukan...
A ranar Juma’a wasu ’yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka uku na Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie a garin Arondizogu, a Ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a Jihar Imo, inda suka kashe aƙalla mutane bakwai. An samu rahoton cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sun yi ta harbin mutanen yankin a ƙauyukan Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama. An kashe mata da yara a sabon harin Filato Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Waɗanda harin ya rutsa da su, masu shaguna ne da kwastomominsu da kuma masu wucewa. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa majiyarr PUNCH cewa, waɗanda lamarin ya...
Sai dai Sanatoci sun yi watsi da bayanin, inda suka zargi Ojulari da yin watsi da Majalisar. Kwamitin yana binciken tambayoyin tantancewa daga shekarar 2017 zuwa 2023, wanda ya nuna sabanin da ya kai Naira tiriliyan 210, ciki har da bashin da ba a tabbatar da shi ba na Naira tiriliyan 103. ‘Yan majalisar sun firgita cewa Naira tiriliyan 3 zuwa 5 ne kawai aka rubuta a cikin asusun ribar da kamfanin ya samu a cikin shekaru shida. “Wannan gayyatar ba tilas bace,” in ji Wadada. Ya kara da cewa kwamitin ba yana zargin hukumar ta NNPC da laifin sata bane amma ya jaddada cewa girman sabanin ya bukaci a yi karin haske kai tsaye. Ya bayyana rashin bayyanar Ojulari...
Aƙalla mutum 14; ciki har da mata da ƙananan yara ƙanana ne, suka rasu a wani sabon hari da aka kai a Jihar Filato. Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a Gundumar Mangor da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos. Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu Waɗanda aka kashe suna kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako-mako da ke garin Bokkos, lokacin da wasu ’yan bindiga suka buɗe musu wuta. Wannan hari na zuwa ne wata guda bayan wani hari da aka kai wa wasu ‘yan ɗaurin aure daga Zariya a Jihar Filato, inda aka kashe su. Ƙungiyar Bokkos Cultural Development Forum (BCDF), ta tabbatar da faruwar...
Koda ya ke dai, a lokacin ‘yansanda sun yi nisa ban gudanar bincike, amma babu wanda suka iya kamawa, kuma ba a kara shigar da wata sabuwar kara a gaban kotu ba, duk tsawon wadannan shekarun. Wannan bukatar da Muyiwa ya biro da ita, tamkar bude wani sabon babi ne, kan batun hallaka manyan mutane a kasar, wadda za a iya cewa, tun daga 1999, har zuwa yau, amma shiru ake ji, kan daukar wani kwakwaran mataki. A wani taro a kwanan baya, babban Lauya SAN Cif Kanu Agabi, ya bijiro da zargin yadda ake gaza hukunta masu aikata manyan laifuka a kasar, inda kuma ake samun dogon jan kafa, kan shari’ar da ta shafi, marasa karfi a kasar. Wannan...
“Sauran su ne Lawan Haruna, Opurum Patrick, Agbo James da Georgewill Onwubiko da sauransu. “Shugaban PSC ya ce su tuna cewa su abokai ne ga kowa, kuma ya kamata a kowane lokaci su yi daidai da abin da ‘yan Nijeriya ke bukata. Ya kuma ba su tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yin iya kokarinta don ganin an inganta yanayin aikinsu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon hawa gwamnatin APC ake yinsa.” Kwankwaso ya kara da cewa ana gudanar da manyan ayyuka a Kudu cikin hanzari, amma an bar ayyuka masu mahimmanci a Arewa babu kulawa. “Muna jin ana gina titi daga Kudu zuwa Gabas. Muna maraba da ci gaba a ko’ina a Nijeriya. Amma gwamnati tana ɗaukar duk arzikin ƙasa ta zuba a ɓangare ɗaya kaɗai, ba ta yin aiki da...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Aref ya jaddada cewa: Dole ne a kawo karshen kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankin Zirin Gaza cikin gaggawa ta hanyar daukar matakai na zahiri da kuma dauri daga kasashen duniya. Aref ya rubuta a shafinsa na X a jiya Alhamis cewa: “Mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba saboda yunwa sakamakon hana isar da abinci ga al’ummar Gaza da aka zalunta ya kasance tare da yin shiru na kunya daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.” Ya kara da cewa: “Dole...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Babu shakka Iran za ta ci gaba da inganta sinadarn Uranium Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a jiya Alhamis dangane da tattaunawar da Iran za ta yi da kungiyar kasashen Turai da za a yi a yau Juma’a a birnin Istanbul na Turkiyya cewa; Za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a cikin kasar Iran, kuma kasar ba za ta yi watsi da wannan hakkin na al’ummar Iran ba. A cikin bayanin da ya yi a gefen ziyarar da ya kai ga iyalan shahidan Laftanar Janar Baqiri, Araqchi ya kara da cewa; Ko da yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da shirinta...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: Taro Tsakanin Iran Da Tawagar Kasashen Turai Dama Ce Ta Gyarar Tunanin Tarai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron Istanbul wata dama ce ta gyara matsayar Turai kan shirin makamashin nukiliyar Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, ya yi la’akari da taron na yau tsakanin Iran da kasashe uku mambobin kungiyar hadin gwiwa ta JCPOA a matsayin wata muhimmiyar dama ta gyara ra’ayoyinsu da gwada hakikaninsu kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. A cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labaran IRNA, Isma’il Baqa’i ya bayyana fatansa na cewa wadannan kasashe uku za su yi amfani da wannan damar wajen gyara tsarin da suka bi a baya wanda bai dace ba, wanda ya lalata martabar Turai da matsayin tattaunawa, tare da mayar da ita a matsayin...

Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza
Hukumar ba da agaji da kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta “UNRWA” tana karkashin wuta sakamakon ma’aikatan 330 da suka yi shahada kuma aka lalata cibiyoyinta 300 a Gaza! Inas Hamdan, mai magana da yawun hukumar ta UNRWA a birnin Alkahira, ta tabbatar da cewa; Yunwar da ke faruwa a zirin Gaza, wani bala’i ne da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya shafi mutane sama da miliyan biyu, ciki har da akalla yara miliyan daya. Wannan ya saba wa duk dokokin jin kai da ka’idoji, kuma abin takaici, lamarin yana da kara muni. Hamdan ta yi nuni da cewa, a lokacin da suke magana kan matsalar agajin jin kai ko shigar da kayan abinci zuwa zirin Gaza,...

‘Yan Tawayen Sudan Ta Kungiyar Rapid Support Forces Sun Kashe Mutane 27 A Yammacin Jihar Kordofan Ta Kasar Sudan
Mutane akalla 27 ne aka kashe a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai a yammacin Kordofan na kasar Sudan Kafofin yada labaran kasar Sudan sun rawaito cewa: Mutane 27 ne suka mutu kana wasu 43 suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan wasu kauyukan arewacin garin Nahud na jihar Kordofan ta yamma. Kungiyar likitocin Sudan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jaridar Sudan Tribune ta buga, inda ta bukaci daukar matakin kasa da kasa na dakatar da abin da ta bayyana a matsayin “cin zarafin fararen hula da bude hanyoyin jin kai don ceto wadanda aka tilastawa gudun hijira daga yankunansu.” A cewar jaridar,...
Aisha Muhammad Abdullahi ’yar shekaru 7 ba ta da masaniyar irin hadarin da ke gaba yayin da mahaifiyarta ta aike ta ta sayo sinadarin hada lemon zoborodo amma ta manta ba ta sayo kankara ba wanda hakan ya sa ta juya. A daidai wannan lokacin ne wata mace wacce ke bin ta a baya ta kirayi Aisha ta kuma ba ta alewa sannan ta bukaci ta bi ta. Abin da Aisha za ta iya tunawa kawai shi ne ta farka daga barci ta ganta a garin Onitsha na Jihar Anambra a hannun wata mace mai suna Ebere. Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Aisha na...
“Rasuwar Sarkin Zamfara babban rashi ne ga al’ummar jihar Zamfara, Arewa da ma ƙasar nan baki ɗaya. “Sarkin ya sadaukar da rayuwar sa a shekarun nan 10 da ya ya yi hana mulki a matsayin Sarkin Gusau na 15, wanda ya hau a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015. Ya yi mulki cikin jajircewa da sadaukarwa. “Marigayin, kafin ya zama Sarki, ƙwararren ma’aikacin gwamnati ne, wanda har sai da ya kai matsayin Babban Sakatare a gwamnatin tsohuwar jihar Sakkwato da ta Zamfara. “Na rasa murshidin Uba mai basira, wanda ke nuna mani hanya, tare da sauran shugabanni a jiha. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuran sa, ya sa aljanna ce ce makoma. Daga kanmu,...

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)
Hikimar Rashin Hade Farkon Shekarar Musulunci Da Tarihin Manzancin Annabi (SAW) Masu karatu har yanzu dai muna kan bayani game da abubuwan da suka sa Sahabbai ba su kafa tarihin kirgen shekarar musulunci ba da wasu manyan alherai na Musulunci, sai suka zabi Muharram ta zama farkon shekarar tare da lakaba mata shekarar Hijirah. A makon da ya gabata mun yi bayani kan hikimar ware farkon shekarar daga watan Rabi’ul Auwal zuwa watan Muharram saboda girman haihuwar Manzon Allah (SAW). A yau kuma, za mu ci gaba da bayani a kan ware kirgen farkon shekarar daban da ranar da aka fara aiken Manzanci ga Annabi (SAW). Tun ana sauran shekara uku Manzon Allah (SAW) ya cika shekara 40 da...
Ya ce, nan da shekarar 2030 za a bukaci hekta miliyan 300 domin samar da bukatar abinci. Don haka ne ya ce taken taron ranar yaki da kwararowar hamada na 2025 na da matukar tasiri domin tabbatar da daukan matakan da suka dace wajen kiyaye hamada da gurbacewar muhalli. A cewarsa, yunkurin zai tunkari manyan kalubale kamar matsalar tattalin arziki da karancin abinci, karancin ruwa, da sauyin yanayi. Lawal ya jaddada cewa cimma muradun ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya ba zai yuwu ba idan ba tare da kare muhalli da kuma kula da filaye da albarkatun kasa ba. Ya kara da cewa gwamnati na ba da fifiko ga al’amuran muhalli kuma ta samar da cibiyoyi, manufofi, tsare-tsaren ayyuka,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati. Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala. NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan irin damar da masu yi wa kasa hidima suke da ita a garuruwan...
Kashe- Kashen 2025 Ya Fi Na 2024 Alkaluman bincike sun bayyana cewar ‘yan ta’adda sun dauki rayukan mutane a rabin wannan shekarar fiye da na shekarar 2024 da ta gabata kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yancin Dan- Adam ta kasa ta bayyana a wannan watan. Kamar yadda alkaluman suka nuna, akalla mutane 2, 266 ne suka bakunci lahira a hannun ‘yan ta’adda a rabin shekarar 2025, idan aka kwatanta da mutane 1, 083 a rabin farko na shekarar 2024 da kuma mutane 2, 194 a bakidaya shekarar. Rundunar sojojin Nijeriya na fafatawar yaki da mayakan Boko- Haram da sauran ‘yan ta’adda a Arewa Maso- Gabas, ta’addanci da garkuwa da mutane a Arewa Maso- Yamma, hare- haren makiyaya da manoma...
Tsohon wakilin Amurka na musamman a kan lamurran Iran Robert Malley, ya caccaki gwamnatin Donald Trump game da kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, lamarin da ya ce babban kure ne wanda kuma zai haifar da mummunan sakamako. Robert Malley ya ce; ina tsammanin zabi na soja ba daidai ba ne bisa kowane irin dalili. Ba ya kula da matsalar da ke tattare da hakan sosai. Lamarin da zai haifar da rashin tabbas da sakamakon da ba za a iya tsammaninsa ba, ba kawai a cikin kwanaki masu zuwa, ko makonni ba, har ma watanni ko shekaru masu zuwa. Don haka ina tsammanin cewa wannan shi ne zabi na kuskure da Trump ya dauka, in ji Robert Malley a wata...
‘Yan majalisar dokokin Amurka sun gabatar da wani kudirin doka da ke ba da shawarar sake duba alakar Amurka da Afirka ta Kudu da kuma kakaba takunkumi a kan wasu jami’ai da suka ki amincewa da manufofin Amurka na ketare. Kwamitin harkokin wajen Amurka ya kada kuri’a don aikewa da daftarin kudiri a kan yin nazarin dangantakar Amurka da Afirka ta Kudu” zuwa ga babban zauren majalisar wakilai, inda za a kada kuri’a a kansa. Wannan matakin na bukatar amincewa daga majalisun wakilai da na dattawa kafin ya zama doka, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters. ‘Yar majalisar wakilai Ronny Jackson ce ta gabatar da kudirin dokar a watan Afrilun da ya gabata. Tana zargin Afirka ta Kudu da...
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fada a wannan alhamis cewa yana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Senegal a cikin watan Augusta domin tattauna yadda aza magance matsalar basussukan da ke kan kasar da kuma fara tattaunawa kan tsarin sabon shirin lamuni. Kasar Senegal na fama da bashin biliyoyin daloli da gwamnatin da ta shude ta karba, lamarin da ya sanya asusun lamuni na duniya IMF ya dakatar da shirin ba da lamuni ga kasar. A nasa bangaren kuma, wani mai magana da yawun IMF ya ce, “Asusun na bukatar karin bayanai kafin ya karfafa kimanta halin da ake ciki na basussukan kasar Senegal, sannan yana bukatar yarjejeniya kan muhimman matakan gyara.” Ya kara da cewa, “Da...
Olumekun ya ƙara da cewa, katunan zaɓe na rijistar da ta gabata ma za su kasance a shirye don karɓa. Ya ce da saura kwanaki 105 zuwa zaɓe, INEC ta san lokaci ya matse, amma tana tabbatar da cewa sabbin masu rijista a jihar Anambra za su samu damar karɓar katunansu kafin zaɓen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba bayan nadin sabon shugaban karamar hukumar Gumel. A wajen bikin da aka gudanar a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa rayuwa na da kurarran lokaci, don haka ya kamata shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma sanin nauyin da ke kansu. “Rayuwa ba ta da tabbas, hakazalika shugabanci ba wasa ba ne”....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar. Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa da tsaki a Jihar Kano. Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71 A cewarsam Tinubu ya yi watsi da halin da yankin arewacin ƙasar ke ciki wajen gina Kudancin Najeriya da kuma samar musu da kayan more rayuwa. “Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ana shirin sayar da makarantar firamare ta Yusuf Dantsoho da ke Unguwar Rimi GRA. Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Maman Lagos, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki makarantar. Makarantar Yusuf Dantsoho, wacce aka kafa a shekarar 1920, tana tsakiyar Unguwar Rimi GRA, kuma ta samar da fitattun ‘yan Najeriya da dama da suka yi aiki a matakai daban-daban na gwamnati da kuma masu zaman kansu. Alhaji Maman Lagos ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da niyyar sayar da wata cibiyar gwamnati, kama daga makarantu zuwa asibitoci. Yace maimakon haka,...
Gwamnatin Jihar Yobe ta raba tallafin kuɗi ga iyalan ’yan banga da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka a bakin aiki. Kuɗaɗen wanda Daraktan ayyuka na musamman, Muhammad Alhaji Baba ya miƙa a madadin sakataren gwamnatin jihar sakamakon umarnin da Gwamna Mai Mala Buni ya bayar na a yi hakan. Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71 An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Wannan shiri dai wani ɓangare ne na shirin jin daɗin jama’a na jaha ga jami’an tsaro domin tabbatar da cewa, iyalan ’yan banga da abin ya shafa sun samu tallafi. A ƙarƙashin shirin, kowane dangin ɗan banga da ya rasu ya karɓi Naira dubu ɗari ₦500, yayin da waɗanda suka jikkata...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam. Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba. Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin ‘yan sahayoniyar da su ka jikkata sojoji ne. Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; Wanda ya take sojojin ya iya gudu daga wurin, ba tare da an tsayar da shi ba. Ita kuwa jaridar ‘ Yasrael Home” ta bayyana cewa; An baza ‘yan sanda a wurin da aka kai hari, domin gano inda maharin yake. Kungiyoyin Falasdinawa sun yi maraba da wannan harin,...
Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen dabbobi. Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono ta hanyar kyautata da kula da lafiyarsu, domin rage dogaro da waje samar da nama da kuma nono.” Haka nan kuma ministan na noma ya kara da cewa; Kara yawan dabbobin da ake samarwa a cikin gida,wata lalura ce ta tattalin arziki, da kuma kishin kasa. Ministan Noma na Iran ya kuma kara da cewa, ma’aikatar tasu tana kokarin ganin mayar da Iran zama cibiyar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin. Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin suna dauke da kayan abinci, ruwa da magani a cikin kasashen Jordan da Masar. A wani bayani da ofishin gwamnatin Gaza ya fitar a yau Alhamis, a cikin yankin Gaza duk wani abinci, ruwa da magani duk sun kare, don haka a halin yankin yankin yana da bukatuwa da buhunan filawa 500,000 a kowane mako. An shiga kwanaki 145 da HKI ta rufe dukkanin mashigar...
Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana cewa gudanar da ayyukan raya kasa sosai a yankunan karkara zai kara daga martabar jihar a idon sauran jihohin kasar nan. Ya yi wannan tsokaci ne yayin ziyarar aiki a sakatariyar karamar hukumar Dutse, inda ya ja hankalin shugaban karamar hukumar game da bukatar bada fifiko ga bangaren ayyukan raya kasa fiye da harkokin yau da kullum domin karfafa matakin cigaban karamar hukumar. A cewar sa, kwamatin na rangadin kananan hukumomin jihar 27 ne domin bibiyar yadda ake aiwatar da tanade tanaden kasafin kudi domin tabbatar da kashe kudaden gwamnati ta hanyar da ta dace, Inda Kwamatin ke duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin...
Shahararren ɗan kokawa ɗan ƙasar Amurka mai ritaya Terry Gene Bollea wanda aka fi sani da Hulk Hogan ya rasu yana da shekara 71 a duniya. A cewar TMZ da sauran rahotanni, likitoci sun mayar da martani a gidansa na Clearwater, da ke Florida da sanyin safiyar Alhamis kan Hulk Hogan ya kamu da bugun zuciya da ya yi ajalinsa. An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Daga nan an ɗauki Hogan da wuri aka saka shi cikin motar ɗaukar marasa lafiya. Duk da damuwa na kwanan da aka bayyana game da lafiyarsa – ciki har da larurar wuyansa a farkon wannan shekara, matarsa Sky ta...

Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya. Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali da Sin ta samu yayin kyautata kauyuka zuwa matsayin birane da garuruwa, Rossbach ta bayyana cewa, Sin ta cimma nasarar kawar da talauci ga mutane miliyan 800, da kuma tafiya a kan hanyar kyautata kauyuka zuwa birane da garuruwa, kuma wannan darasi ne da ya cancanci kasashen Afirka wadanda suke fuskantar kalubalen kyautata kauyuka zuwa birane su yi koyi da shi. Ta ce, nan da...
A cewar ministan, shi da sauran abokan aikin sa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a Jihar Katsina. Cibiyoyin da aka ƙaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sababbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan Asibitocin Koyarwa na Tarayya a ƙasar nan. Wannan cigaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani. Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da suka rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alƙawarin samar da ingantaccen tsarin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aikin gina tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin ya samu gagarumin ci gaba sosai, inda gwamnatin kasar Sin ta sanar a jiya cewa, a ranar 18 ga watan Disamban bana, za a kaddamar da manufar kafa “kwastam mai zaman kansa a duk faɗin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan” a hukumance, wadda ke nufin saukaka bincike da ragewa ko soke haraji. “Ana iya cin moriyar manufofin ba da fifikon harajin kudi a tsibirin Hainan”, sannan “mu’amalar Hainan da kasashen duniya za ta kasance cikin ’yanci da lumana”. A ra’ayin jama’a na kasa da kasa, wannan wani muhimmin mataki ne ga kasar Sin na kara fadada bude kofa ga ketare, wanda ba bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar...
Kwamitin zartaswa na Jam’iyyar APC na ƙasa ya naɗa Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. Nan take aka rantsar da Nentawe Yilwatda a wajen taron. Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Nentawe ya yi rantsuwar ne da misalin ƙarfe 02:50 na rana a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar yayin taron NEC karo na 14 da ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, ranar Alhamis. Nentawe, wanda ya fito daga Jihar Filato, shiyyar Arewa ta Tsakiya, shi ne ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin...
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin...
An cimma matsaya kan zaɓensa bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC. Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar za su tabbatar da naɗinsa a yau Alhamis. Farfesa Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da suke da alhakin riƙe kujerar shugabancin jam’iyyar. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sun ce kasancewarsa Kirista zai taimaka wajen daidaita shugabanci, duba da cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa Musulmai ne. Shugabannin jam’iyyar na fatan Farfesa Yilwatda zai kawo sabon salo, tare da haɗa kan jam’iyyar kafin tunkarar zaɓe mai zuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar China. Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa jirgin wanda ke dauke da fasinjoji, ciki har da kananan yara biyar da kuma ma’aikatan jirgi su shida, ya fadi ne ranar Alhamis ba tare da ko mutum daya ya rayu ba. “Ma’aikatan ceto sun gano wasu sassan jirgin na ci da wuta,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito jami’an ceton na cewa. Reuters ya kuma ce jirgin wanda mallakin kamfanin Angara Airlines ne, ya fadi ne a kusa da Tyndra, wani gari da ke yankin na Amur, bayan hanyar da yake...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu. Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a fadin kananan hukumomin da lamarin ya faru. Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Dr Goje yan kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu. Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu. Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a fadin kananan hukumomin da lamarin ya faru. Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Dr Goje yan kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu. Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi...

Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
Ayatullah Makarem Shirazi ya jaddada cewa: An kara samun karfafan hadin kan al’umma Iran bayan wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya da Amurka kan kasarsu Ayatullah Nasser Makarem Shirazi, babban malamin addinin Musulunci a birnin Qum mai tsarki na kasar Iran ya jaddada cewa: An kara samun hadin kan kasa bayan yakin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ganawarsa da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a jiya Laraba a birnin Qom mai alfarma Ayatullah Makarem Shirazi ya yi ishara da yakin tunani da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya da Amurka suka yi kan Iran yana mai cewa: Wadannan makiya sun yi zaton za su haifar da rudani ta hanyar kai...
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza. Mataimakin babban...

Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan jin kai da dama da suka yi balaguro zuwa yankunan da ake fama da rikici, da bala’o’i, da wuraren yaki a duniya, kuma dukkansu, ba tare da togiya ba, sun amince cewa, ba su taba ganin wani yanayi mai kama da abin da ke faruwa a Gaza ba. Abu Khalaf ya yi nuni da cewa: Mutanen yankin Zirin Gaza sun fara fama da yunwa, sannan...

Ministan Lafiya Na Kamaru: Hadin-Gwiwa Ta Fuskar Kiwon Lafiya Ta Shaida Zumunci Mai Karfi Tsakanin Kamaru Da Sin
Ministan lafiya na kasar Kamaru, Manaouda Malachie ya bayyana jiya Talata 22 ga wata a Yaounde cewa, hadin-gwiwar Kamaru da Sin a bangaren kiwon lafiya ta haifar da babban alfanu ga jama’ar Kamaru, kana alama ce dake shaida dangantakar kut da kut gami da dadadden zumunci tsakanin jama’ar kasashen biyu. A wajen bikin cika shekaru 50 da kaddamar da hadin-gwiwar Sin da Kamaru ta fuskar kiwon lafiya wanda aka yi a jiya Talata a birnin Yaounde, minista Malachie ya gabatar da jawabi yana mai cewa, hadin-gwiwar kasashen biyu ta fuskar kiwon lafiya ta shaida cewa, kwalliya za ta iya biyan kudin sabulu, idan aka raya hulda mai aminci, da sahihanci kuma bisa muradu iri daya tsakanin kasa da kasa. Gwamna...
Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da karya dokokin kasa da kasa, inda ta fara mamaye yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan da kwarin Jordan! Majalisar Dokokin yahudawan sahayoniyya ta Knesset ta kada kuri’a kan wani kudirin doka da ba shi da tushe don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila cikakken ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma kwarin Jordan. Kuri’ar dai ta samu amincewar ‘yan majalisu 71, yayin da 13 suka nuna adawa da shi. Kungiyar Hamas ta dauki matakin a matsayin maras halacci a doka. A wani mataki da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida da na waje, Majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta kada kuri’ar amincewa da wani kudirin doka da bai taka kara ya karya ba na...
Wani mummunan al’amari ya faru a Ƙaramar Hukumar Fika da ke Jihar Yobe, inda wata mata mai shekara 35, ta kashe mijinta da itace bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu a kan abinci. Rahotanni sun nuna cewa matar wacce ’yar garin Abba ce, ta ɗauki katon itacen girki ta rafka wa mijinta bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan sama da mutum 100 Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Dungus Abdulsalam, ya ce bayan faruwar lamarin, an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka kama wacce ake zargi. Marigayin ya rasu nan take, kuma ya bar mata biyu da...

Gwamantin Kasar Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga BirninSiweida Na Kasar Saboda Ci Gaba Da Bullar Rikici
Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun rufe hanyoyin zuwa birnin Sweida bayan sake bullar wani tashin hankali Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin Sweida da ke kudancin kasar tun daga wayewar garin ranar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin. A halin da ake ciki, ana ci gaba da kokarin da ake yi na cikin gida da waje na wanzar da tsagaita bude wuta da kare fararen hula. Ana zaman dar dar a lardin Suwayda da ke kudu maso yammacin kasar Siriya, inda dakarun gwamnati ke ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin tun da safiyar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza...
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Ƙananan Hukumomin Rijau da Mariga a Jihar Neja. ’Yan ta’addan sun fito ne daga Jihar Zamfara, yayin da suke tafiya a kan babura ɗauke da muggan makamai. Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100 Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa Sojoji tare da taimakon jiragen yaƙi na sama sun kai farmaki bayan samun bayanan sirri. Aƙalla ’yan ta’adda 95 aka kashe a yayin artabun. Sojojin sun kuma lalata babura 18 tare da ƙwato bindigogi kirar AK-47. Sai dai an yi rashin sa’a soja guda ɗaya ya rasa ransa a yayin fafatawar. Dakarun sun sake kai wani farmaki na biyu inda suka ƙwato makamai da...
Gobir ya bayyana cewa kowanne daga cikin waɗanda aka ceto zai samu Naira 100,000, buhun gero ɗaya da buhun masara ɗaya a matsayin tallafi. Shi ma da yake magana, Shugaban ƙaramar hukumar Isa, Alhaji Sherifu Abubakar Kamarawa, ya gode wa gwamnatin jihar bisa taimakon da ta bayar, yana mai cewa hakan ya nuna damuwar gwamnati kan tsaron rayuka da jin daɗin al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Matukar ba a sami sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan Jinkai da Yaki da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa a yau Alhamis. Majiyoyi da dama a daren jiya sun shaida wa Aminiya cewa Nentawe ne ke kan gaba a cikin mutanen da ake so su dare shugabancin jam’iyyar mai mulki. Sai dai a cewar wasu majiyoyin, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Almakura shi ma na daga cikin wadanda ake duba yiwuwar ba kujerar. Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno NAFDAC ta gano dakin ajiye kayayyaki makare da sinadaran hada bam a Kano A daidai lokacin da ya rage ’yan sa’o’i gabanin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar, majiyoyi...
Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da daewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka. Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin kasar Iran kan yadda mu’amalar hukumar zata kasance da Iran. Gharibabadi ya bayyana cewa idan kasashen yamma sun yi kokarin amfani da shrin SnapBack na yarjeniyar JCPOA zasu gamu da maida martani mai tsanani, sannan ya kara da cewa mu’amala da hukumar IAEA da kasar Iran zata sauka saboda amfani da karfi kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran wanda Amurka da HKI suka yi a kallafeffen...
Yan majalisar dokokin kasar Iran sun bukaci majalisar dokokin kasar Iraki su kori sojojin Amurka daga kasar ta Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yana cewa, yan majalisar dokokin kasar Iran sun bayyana haka ne a lokacin ganawasu da wani dan majalisar dokokin kasar Iraki mai wakiltan lardin Karbalar Imam Hussain (a) a majalisar dokokin kasar. Labarin ya nakalto wakilin lardin Karbala a majalisar dokokin kasar Iraki yana cewa kasashen Iran da Iraki da gwamnatin kasar Iraki sun gamu a wannan ra’ayin kuma nan gaba abinda za’a yi Kenan. Yace dole ne sojojin Amurka su fice daga kasar Iraki, su kuma fice daga dukkan kasasjen larabawa a yankin. Ya ce da haka ne kasashen yankin zasu tabbatar da...
Wani babban Jami’in diblomasiyyar kasar Iran ya zargi Amurka da kuam HKI da laifin Zagon kasa ga dokokin kasa da kasa da kuma sabawa yarjeniyoyi da dokokin MDD. Kazen Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran sharia na kasa da kasa yana fadar haka a jiya Laraba a majalisar dinkin duniya a birnin NewYork na kasar Amurka, a lokacinda yake jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD dangane da kasar Falasdinu. Gharibabadi ya bayyana cewa, Amurka da HKI sune manya-manyan masu haddasa rashin tsaro a kasashen yankin Asiya ta yamma. Jami’in diblomasiyyar ya bayyana cewa Amurka da HKI ne suke haddasa halin da ake ciki a Gaza, na yuwan da kuma kisan kiyashi a Gaza da kashesu...
Gwamnatin kasar Brazil tana shirin bayyana goyon bayanta ga Afirka ta kudu a karar da ta shigar a gaban kotun ICJ dangane da tuhumar jami’an gwamnatin HKI da aikaya kisan kiyashi a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wata jaridar kasar Brazil Folha De S tana fadar haka. Sannan kamfanin dillancin labaran reuters ya tabbatar da labarin a jiya Laraba. A shekara ta 2023 ne gwamnatin Afirka ta kudu ta shigar da karar don tabbatar da cewa gwamnatin HKI ta na aikata kissan kare dangi kan kasar Amurka. Wanda ya sabawa dokar hana kissan kare dangi ta MDD ta shekara 1948. Sannan a cikin watan Octoban da ya gabata ne, Pretoria ta gabatar da shaidu da...
Dakarun Sojin Operation Hadin Kai, sun daƙile hare-haren Boko Haram a garuruwan Monguno da Bitta da ke Jihar Borno, tare da wani kashe babban Kwamandan Boko Haram mai suna Ibn Khalid. Sun kuma kashe ’yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan ƙungiyar. NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Kapten Reuben Kovangiya, ya ce sojojin sun yi jarumta wajen hana ’yan ta’addan shiga Monguno. Ya ce sojojin sun yi amfani da manyan makamai wajen mayar da martani, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan Boko Haram mai...
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a ranar Laraba ta ce ta gano wani dakin ajiye kayayyaki da aka makare da lita 88,560 na sinadaran hada bama-bamai a Kano. Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan lokacin da take yi wa manema labarai jawabi a kofar rumbun da ke unguwar Kwakwaci a karamar hukumar Fagge da ke jihar. Mojisola, wacce Daraktan Bincike da Tabbatar da Bin Doka na hukumar, Dokta Martins Iluyumade ya wakilta, ta ce dakin na dauke ne da lita 60,000 na sinadarin sulphuric acid, sai kuma lita 28,560 na nitric acid da kuma wasu jarkoki 330 da aka riga aka rabar wa mutanen da ba a san ko su...
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na ci gaba da hadin gwiwa da Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria – FMBN) domin shawo kan matsalar karancin gidaje a jihar. Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da Babban Daraktan bankin Alhaji Shehu Usman Osidi a ofishinsa. Gwamna Yusuf ya bayyana muhimmancin wannan hadin gwiwa, yana mai jaddada Kano a matsayin jiha ta biyu mafi yawan jama’a a Najeriya, inda adadin mutanenta ke kara karuwa cikin sauri. “Kano tana daga sahun gaba wajen ci gaba, kuma samar da gidaje na daga cikin muhimman ginshikai na wannan ci gaba. Akwai bukatar samar da gidaje masu araha domin inganta rayuwar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya bayyana cewa Gwamnonin APC sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar gwamnati da ke Abuja. Da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron, Gwamna Uzodimma ya bayyana ganawar da cewa “tattaunawa ce mai muhimmanci da Shugaban Ƙasa domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma inganta ikon ta na samar da nagartaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya”. Ya ƙara da cewa, a matsayin su na gwamnoni, sun haɗu da Shugaban Ƙasa domin daidaita matsayin al’amuran jam’iyya da kuma muhimman abubuwan da suka shafi shugabanci. Da aka tambaye shi ko ana sa ran yanke wasu manyan shawarwari ko takaddama a...
Yau Laraba, aka kaddamar da bikin nune-nunen harkokin rediyo da fina-finai da talabijin na kasa da kasa na Beijing karo na 32 ko kuma BIRTV2025 a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wanda kamfanin CBIC na kasar Sin ya dauki nauyin shiryawa, bisa jagorancin babbar hukumar kula da harkokin rediyo da talabijin ta kasa gami da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasa wato CMG. Bikin na BIRTV2025 yana kokarin kafa wata gada don inganta mu’amala tsakanin kasa da kasa ta hanyar gudanar da harkokin kasa da kasa, ciki har da taron sanin makamar aiki don inganta kwarewar kafafen yada labaran Sin da Afirka, wanda zai mayar da hankali kan irin labaran da suka kamata a watsa, gami da hanyoyin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dokokin Tarayya buƙatar ƙara ranto bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare, ƙarƙashin shirin ciyo bashin na gwamnatin tarayyar na 2025 zuwa 2026. Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Tinubu ya aikewa majalisar, wadda Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanto a zamansu na yau Laraba. Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya Takartar ta ambato shugaban ƙasar na cewa karɓar rancen ya zama tilas saboda buƙatar ƙarin kuɗi da aka yi a aikin babbar hanyar Lagos zuwa Calabar, wanda ya tashi daga Dala miliyan 700 zuwa Dala miliyan 747 — ƙarin Dala miliyan 47 ke...
Gwamnatin Borno ta bayyana yawan ma’aikata a matsayin dalilin da ya sanya ƙananan hukumomin jihar ba za su iya biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata na Naira dubu 70,000 ba. Gwamnatin ta ce ta umarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su samar da tsari mai ɗorewa domin ƙaddamar da fara aikin mafi ƙarancin albashin. WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi Babban sakataren ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masana’antu, Modu Alhaji cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce yawan ma’aikatan ne ya haifar da jinkiri wajen fara biyan mafi ƙarancin albashin. Modu ya yi bayanin cewa a wasu lokutan gwamnatin tarayya na turo ƙasa da Naira...

Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana cewa aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, a karshen kogin Yarlung Zangbo, aiki ne dake bisa ikon mallakar kasar Sin, kuma Sin din tana raya aikin don gaggauta samar da makamashi mai tsabta, da kyautata zaman rayuwar jama’ar wurin, da kuma tinkarar sauyin yanayi. Guo ya ce, kasar Sin ta mai da hankali, da sauke nauyin dake wuyanta na amfani da albarkatun kogin da ya ratsa bangarenta da ma kasashen waje, kana tana da fasahohin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa. An tsara aikin ne a kan karshen kogin Yarlung Zangbo bisa ma’aunin Sin mai nasaba da aiki, da gudanar...
Sojojin ruwan Iran sun sanar da cewa, wani jirgin ruwan Amurka na yaki da ya yi kokarin shiga tekun Oman, ya fuskanci gargadi daga sojojin ruwan Iran tare da tilasta masa janyewa. Da saiyar yau Laraba ne dai jirgin sama mai saukar angulu mallakin sojojin ruwa, ya yi gargadi ga jirgin ruwan na Amurka da a karshe ya tilasta masa janyewa. Da fari, jirgin ruwan yakin na Amurka ya yi wa jirgin sama mai saukar angulu na Iran barazanar kai masa hari, said ai duk da haka sojojin ruwan na Iran sun ci gaba da yin gargadi ga Amurkawan da su kar su shiga cikin ruwan tekun Oman. Bayan wannan barazana ne aka aikewa jirgin ruwan Amurkan sako daga dakarun...
Kungiyoyin agaji da kuma na hakkokin bil’adama sun yi gargadi akan yunwar da ake fama da ita a Gaza, tare da yin kira ga gwamnatoci da su yin matsin lamba domin kawo karshe killace Gaza da aka yi, da kuma shigar da kayan agaji a cikin yanki. Kungiyoyin sun kuma dorawa HKI alhakin halin da mutanen Gaza suke ciki na yunwa. Daga cikin kungiyoyin da su ka fitar da bayani da akwai Majalisar ‘yan gudun hijira ta kasar Norway” da “Refugee International” da wasu da adadinsu ya kai 111, sun yi gargadi akan yadda yunwa take yaduwa a cikin Gaza. Bayanin ya kunshi cewa; Mazauna yankin Gaza suna fama da yunwa saboda killace su da Isra’ila ta yi, kuma a...
Ofishin Fira ministan kasar Iraki ya fitar da bayani a yau Laraba akan abinda ya gudana a tsakanin Muhammad Shiya al-Sudani da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a tattaunawar wayar tarho. Sakataren harkokin wajen Marco Rubio ne ya kira yi fira ministan Iraki inda su ka tattauna alakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma halin da ake ciki a wannan yankin. Sudani ya yi ishara da hare-haren bayan nan da aka kai wa cibiyoyin man fetur dake yankin Kurdistan na Iraki da kuma yankin Salahuddin a Karkuk. Haka nan kuma ya ce a halin yanzu jami’an tsaro suna gudanar da bincike domin gano wadanda su ka kai harin.” Haka nan kuma Fira ministan na kasar Iraki ya bayyana mamakinsa...
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin falasdinawan da su ka yi shahada saboda yunwa sun kai 10. Daga lokacin da HKI ta fara amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 111. Wannan adadin yana nuni da yadda rashin abinci ya tsananta a cikin yankin na Gaza saboda yadda Isra’ila ta killace yankin ta hana a shigar da abinci a ciki. A gefe daya, HKI tana ci gaba da kashe Falasdinawa ta hanyar yi musu kisan kiyashi, da a yau kadai fiye da mutane 80 ne su ka yi shahada. Mafi yawancin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’oin nan...
Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa daga ƙarshen watan Yuli, zai dakatar da tallafin gaggawa na abinci da kiwon lafiya ga mutum miliyan 1.3 a Arewa maso Gabashin Nijeriya saboda ƙarancin kuɗi. Darektan WFP a Nijeriya, David Stevenson, ya ce kayan abinci da na kiwon lafiya sun ƙare gaba ɗaya, kuma rabon da ake yi yanzu shi ne na ƙarshe. Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi 2027: Obi zai iya takara ba tare da ni ba — Datti Baba-Ahmed Ya ce tallafin zai tsaya ne daga ƙarshen watan Yuli, lokacin da aka ƙiyasta kayan abinci da na kiwon lafiyar za su ƙare gaba ɗaya. Idan ba a samu tallafi cikin gaggawa ba,...
“Mun kasance muna jiran a ba mu garin alkama, saboda muna jin yunwa sosai, muna neman abin sha da abinci, kwatsam tankokin sojan Isra’ila suka zo suka kewaye mu, suka fara harba bindiga a kanmu, ba mu iya motsawa ba. Ba mu samu gari ba, an kuma kewaye mu na tsawon sa’a daya da rabi zuwa biyu, wasu sun gudu, wasu an kashe su, wasu kuma sun ji raunuka.” In ji wani dan Gaza game da abin da ya faru gare shi a ranar 21 ga wata. Tsawon kwanaki 140 ke nan da Isra’ila ta rufe hanyoyin shiga Gaza. A halin yanzu, kashi 93% na iyalai a Gaza ba su da ruwan sha, kuma fiye da kashi 87% na yankunan...
Wasu matasa uku daga ƙauyen Durum sun rasu yayin da suke wanka a wani rafi a ƙauyen Jinkiri, cikin gundumar Tirwun a Ƙaramar Hukumar Bauchi. Matasan su ne; Habibu Mohammed mai shekaru 16, Abubakar Mohammed mai shekaru 16, da kuma Zailani Sule mai shekaru 14. 2027: Obi zai iya takara ba tare da ni ba — Datti Baba-Ahmed NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana wa manema labarai faruwar lamarin. Duk da ƙoƙarin da aka yi na ceto su, matasan sun rasu kafin a kai su asibiti. Wakil, ya ce bincike ya nuna cewa matasan sun yi aikin haƙar ma’adinai, wanda daga bisani...
Babban abin dubawa a nan shi ne ko mene ne hikimar tura irin wadannan bakin haure zuwa kasashen Afirka? Misali kamar bakin hauren da Amerika take son turawa Nijeria, ’yan asalin kasar Venezuela, ko kuma bakin hauren da Sudan ta kudu ta karba ’yan asalin Myammar, da Cuba da Vietnam, al’adunsu da harshensu sun sha banban da na ’yan Afirka. Sabo da haka babu wata alaka tsakanin juna. To idan ba domin isgilanci da gadara ba, ta yaya Mr. Trump zai nemi tursasawa kasashen Afirka karbar irin wadannan bakin haure maimakon ya tasa keyarsu zuwa kasashensu na asali?(Lawal Mamuda) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ta kasar Sin ta fidda bayani a jiya Talata cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, yawan zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ya kai ton-kilomita biliyan 78.35, adadin da ya karu da kaso 11.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Kana, yawan zirga-zirgar fasinjoji ya kai miliyan 370, wanda ya karu da kaso 6 bisa dari. A sa’i daya kuma, yawan zirga-zirgar hajoji da kunshin kayayyaki ya kai ton miliyan 4 da dubu 784, wanda ya karu da kaso 14.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Cikin taron aiki da hukumar zirga-zirgar jigaren sama ta fasinja ta kira a jiyan, shugaban hukumar Song Zhiyong...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe, sun fara rabon kayayyakin gini ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙananan hukumomi 13 na jihar. Wannan taimako na da nufin tallafa wa mutanen da ambaliya ta rushe musu gidaje. Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano A lokacin da aka fara rabon kayayyakin a Damaturu, wakilin babban daraktan NEDC, Farfesa Ibrahim Ali Abbas, ya ce hukumar ta kawo kayayyakin rufin gida da sauran kayan gini don taimaka wa mutane su gyara ko sake gina gidajensu. Baya ga wannan, hukumar ta kuma bai wa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda takwas, da kuma mayar da wasu hudu zuwa wasu ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati daban-daban. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya fitar a Dutse, inda ya bayyana cewa daga cikin sabbin sauye-sauyen akwai Sagir Muhammad Sani daga Ma’aikatar Ilimin Firamare zuwa Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki, da kuma Muhammad Yusha’u daga Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki zuwa Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi. Sai Lawan Muhammad Haruna daga Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi zuwa Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi, da kuma Injiniya Musa Alhassan Arobade daga Ma’aikatar Wuta da Makamashi zuwa Hukumar Bunƙasa Ma’aikata da Horaswa,...
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano. Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Lamido, ya ce hukumomi irin su EFCC ana amfani da su ne wajen matsa wa ’yan adawa lamba. Ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin aikata almundahana. A cewarsa bayan Okowa ya koma jam’iyyar APC, an daina tuhumarsa. Ya kafa misali da wata magana da Sanata Adams Oshiomhole ya taɓa yi. Ya ce: “Da zarar ka shiga APC, an yafe...
Ana zargin wata uwa a jihar Enugu da kashe ’ya’yanta biyu saboda tsananin kuncin rayuwa. Lamarin ya faru a unguwar Trans Ekulu da ke yankin birnin na Enugu. An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa An ga gawarwakin yara biyu a gidan lokacin da jami’an tsaro sukashiga ciki, lamarin da ya tayar da hankulan jama’ar unguwar. Yaran da ake zargin uwar tasu da kashewa sun hada da yarinya mai suna Esther Arinze mai shekara hudu da haihuwa da kuma kaninta mai suna Chibusoma. Ana zargin an yi amfani da makami mai kaifin gaske wajen ji wa yaran raunuka a jikunansu kafin su rasu. Majiyar labarinmu da rundunar...
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci. Ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya makara wajen dawowa makaranta zai iya fuskantar hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa; Ba zai yiwu Iran ta iya yin watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Har yanzu ba a daina sarrafa sinadarin Uranium ba a Iran, duk da irin barnar da hare-haren Amurka ya yi wa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran. A wata hirarsa da Fox News, Araqchi ya amsa tambayoyi kan cewa: “Shin shirin inganta sinadarin Uranium a Iran ya dawo? Shin har yanzu yana ci gaba, ko kuma barnar da aka yi wa Iran ya yi tsanani har ta kai ga dakatar da shi gaba daya?” Araqchi ya amsa da cewa; “Ba a daina bainganta sinadarin ba, duk da cewa barnar ta yi...
Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai taɓa, a kowace hanya ko salo, tauye ko hana ci gaban aikace-aikacen kafafen yaɗa labarai a wannan ƙasa ba. Amma dole ne mu duka ‘yan jarida da masu aikin yaɗa labarai mu haɗa kai, mu bi wannan hanya mai sarƙaƙiya, mu tabbatar da cewa al’umma tana ci gaba da zama cikin haɗin kai, yayin da muke riƙe shugabanni da gwamnati da alhakin aikin su.” Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen kula da tsarin dimokiraɗiyya, inda ya shawarci ’yan jarida da su kula da rawar da suke takawa domin kada su zama abin da zai jawo ruɗani ko rikici a cikin al’umma. “A yayin da kuke...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar Barack Obama da cin amanar kasa tare da yin kira da a yi masa shari’a Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi magabacinsa, Barack Obama da cin amanar kasa, inda ya bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya kan wani rahoton sirri da ya nuna cewa; Jami’an gwamnatin Obama sun murguda bayanai game da katsalandan din Rasha a zaben Amurka na shekara ta 2016. Kalaman na Trump sun zo ne yayin wani taron manema labarai a ofishin Oval, wanda shugaban kasar Philippines Ferdinand Marcos ya halarta. Yana cewa:”Bisa ga abin da ya karanta…tsohon shugaba Obama ne ya fara wannan badakalar,” ya kara da cewa Obama shi ne “shugaba” na...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata a ce ana ware wa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya. NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin...
“Farfaɗowa na samuwa, kuma a bayyane yake cewa sabon yanayi na sauyi yana faruwa a Kaduna,” in ji shi. Ya jaddada cewa kyakkyawar gwamnati na nufin kula da buƙatun al’umma, musamman waɗanda rikici ya shafa. “Muna share hawayen waɗanda rikice-rikice suka shafa. Muna haɗa kan al’umma. Muna tabbatar da cewa kowa yana da wajen zama da jin cewa yana da muhimmanci,” in ji Tinubu. Shugaban ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna, ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, da kuma hafsan hafsoshin tsaro bisa matakan soja da na lumana da suke ɗauka don shawo kan matsalar tsaro. “Zaman lafiya na gaskiya sai an gina shi, ba zai zo da ƙarfi ko tsoratarwa ba,” in ji shi. Ya...
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin masani a harkar hulɗa da jama’a kuma ma’aikacin gwamnati na gari da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga jihar. Ya ce aikin wayar da kai da ya yi ba za a manta da shi ba. Gwamna Bala Muhammad, ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa, abokansa da masarautar Bauchi. Ya bayyana Ilelah a matsayin mutum mai kishin ƙasa da jajircewa a bakin aiki. Ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya jiƙansa kuma ya sanya shi a Aljanna Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran. Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a kasar Iran nan gaba bisa tsarin dokokin kasa da kasa. Wannan yunkuri yasa an ga bangarorin biyu na Amurka da Isra’ila suna matsa lamba a kan sauran bangarori na duniya, tare da bayyana Shirin na Iran a matsayin mai matukar hadari ga duniya, da nufin samun goyon bayan kasashen duniya kan bakaken manufofisu a kan kasar ta Iran. Dangane da zargin da...
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka. “Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem. Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen...
Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata. Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata 22 ga watan Yuli 2025, aka gudanar da taron tawagogin kasashen uku. Mahalarta taron a karkashin inuwar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, sun tabbatar da aniyar kasashensu na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da yin musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar. Sun kuma jaddada muhimmancin ci gaba...
Amurka ta yanke shawarar ficewa daga hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a karo na biyu saboda matakin da ta dauka na shigar da Falasdinu a matsayin mamba. Mataimakiyar sakatariyar yada labaran fadar White House Anna Kelly ta sanar da matakin a cikin wata sanarwa a ranar Talata. Kelly ta ce dalilin da ya suka dauki wannan kan hukumar UNESCO, shi ne ta tallafa wa shirye-shiryen da Amurka ke kallonsu a matsayin wadanda ba su dace da muradunta ba. “Shugaba Trump ya yanke shawarar janye Amurka daga UNESCO, wadda ke kula da ayyuka a bangaren raya al’adu da ilimi da zamantakewar al’umma, saboda daukar wau matakai wadanda ba su dace da manufofin Amurka...
Wata sabuwar tashin-tashina ta sake kunno kai a yankin kahon Afirka a daidai lokacin da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya yi gargadi kai tsaye ga firaministan Habasha Abiy Ahmed, inda ya yi kashedin sake kaddamar da wani yaki. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Habasha ke kokarin shiga bangaren ruwa Eritra da kuma tabarbarewar dangantakar bangarorin biyu tun bayan rikicin Tigray. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan telebijin, shugaba Afwerki ya yi gargadin cewa adadin yawan jama’ar Habasha ba zai tabbatar da nasarar soji ba, yana mai nuni da dabarun yakin da Habasha ta yi amfani da su a yakin da ya gabata, yana mai cewa duk da yawan sojojinta amma bata...
Dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta lashi takobin sake maka shugabancin Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a gaban kotun daukaka kara bayan an hana ta shiga harabar majalisar a ranar Talata. Cikin bacin rai, Natasha ta shaida wa ’yan jarida cewa za ta tattauna da lauyoyinta cikin gaggawa domin fara shigar da karar, tana mai cewa matakin ya saba da hukuncin kotun da ta bayar da umarnin a mayar da ita kan kujerarta. Lamarin dai ya biyo bayan yadda jami’an tsaron da ke gadin majalisar suka tare hanya suka hana tawagar motocinta shiga majalisar, duk kuwa da umarnin kotu na mayar da ita. HOTUNA: An ƙaddamar da aikin sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu...
A cewar Ringim, idan ana so a sami cigaban da ya shafi kowa da kowa a Arewacin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, to ana buƙatar siyasa irin ta Kwankwaso wadda ke mayar da hankali kan talakawa da gaskiya a mulki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa. Sanarwar ta bayyana cewa bikin sanya hannun ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnati dake Dutse, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta, ciki har da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Sani Isyaku. Ta ce Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, bayan kai-komo na sama...
Kwamatin kananan hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya duba ayyukan raya kasa da karamar hukumar Kirikasamma ta samu nasarar gudanarwa daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya kafa kananan kwamitoci guda biyu domin samun nasarar tantance ayyukan a cikin garin Kirikasamma da kauyuka. Karamin Kwamati na daya bisa jagorancin wakilin mazabar Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashimu Kanya, ya duba aikin sanya soma da tona riniyar tuka tuka a mayanka da magudanin ruwa a garin Marma da aikin gina rumfunan kasuwa a garuruwan Tasheguwa, Marma, Dilmari da Madaci. Alhaji Ibrahim Hashim Kanya ya bayyana wa shugaban kamsilolin karamar hukumar wanda ke yiwa tawagar rakiya, Malam Isyaku Abdullahi, muhimmancin ziyarar duba ayyukan Gwamnati dan tabbatar da...