Jami’an tsaro a kasar Amurka sun cilla tear gas da albarusan roba kan masu zanga-zangar kin amincewa da shirin shugaba Trump na korar wasu Amurkawa wadanda ya kira bakin haure.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa, rikicin wanda aka fara tun kwanaki uku da suka gabata ya tashi ne bayan da jami’an shege da fice na Amurka suka kama wasu yan Latino da nufin korarsu daga kasar.

Sun kama mutane da dama a birnin Los Angeles a cikin rana kowa na gani. Gwamnan jihar Calfonia Gavin Newson ya rubuta a shafinsa na X kan cewa basu da wata matsa sai bayan da shugaba Trump ya aiko da ‘Sojojin Tarayya ko “National guard”, kuma wannan keta hurumin jihar ne, kuma shiga Trump tare da National Gurd shi ne rikita al-amura a jihar. Amma duk da haka zuwa safiyar yau Litinin kome ya lafa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100

Wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, sun yi zanga-zangar lumana tare da neman gwamnati ta ɗauki kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a yankin.

Zanga-zangar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Laraba.

Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno

Jama’a da dama sun halarci zanga-zangar; wasu a kan babura, wasu a cikin motoci, wasu kuma a ƙafa.

Kuma sun taru a ƙofar gidan gwamnatin Jihar da ke Gusau domin nuna damuwarsu.

Ƙauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka, da Fegin Mahe.

Mazauna yankunan sun ce sama da mutum 100 ’yan bindiga suka kashe a baya-bayan nan.

Wani daga cikin masu zanga-zangar, Malam Abubakar Abdullahi daga ƙauyen Fegin Mahe, ya ce ’yan bindiga sun kashe ’yan uwansa da dama, sannan kuma sun sace musu kaya da darajarsu ta haura Naira miliyan ɗaya, ciki har da buhun taki guda 500.

Hare-haren sun hana manoma yin aiki a gonakinsu, saboda rashin tsaro a yankin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Gusau, Abubakar Iman, ta bakin wakilinsa Aminu Wakili Mada, ya ce ya fahimci ƙorafin jama’ar yankunan.

Ya tabbatar da cewa gwamnati tare da jami’an tsaro suna aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya, kuma za a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa wuraren da suka fi fama da matsala nan ba da jimawa ba.

Yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ci tura domin bai amsa waya ba.

A wani labarin kuma, jami’an tsaro sun ceto mutum 11 da aka sace a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

An sace mutanen ne a ƙauyen Kaibaba da ke gundumar Turba a Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato.

An miƙa su ga Gwamnatin Jihar Sakkwato a ranar Laraba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
  • Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan sama da mutum 100
  • Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno
  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  • Iran: Sojojin Ruwan Iran Sun Kori Jirigin Yakin Amurka Daga Tekun Oman
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
  • Trump ya fitar da Amurka daga UNESCO saboda amincewa da  Falasdinu a matsayin Mamba
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh