Ya yaba musu cewa, sun yi kokari sosai wajen kashe wani babban kwamandan kungiyar ta’addanci ta ISWAP tare da wasu mutane biyu kwanaki kadan da suka gabata.

 

LEADERSHIP ta tuna cewa, babban kwamandan ISWAP da aka kashe, Abu Fatima na cikin jerin sunayen ‘yan ta’addan da sojojin Nijeriya ke nema ruwa a jallo tare da saka ladar Naira miliyan 100 kan duk wanda ya kawo mata shi.

 

An ce Abu Fatima shi ne ke da alhakin kai hare-hare a arewacin jihar Borno, musamman ma yankin Baga.

 

An fara kama dan ta’addar na ISWAP a raye amma daga baya ya mutu sakamakon zubar da jini mai yawa bayan Harbin da aka yi masa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin falasdinawan da su ka yi shahada saboda yunwa sun kai 10.

 Daga lokacin da HKI ta fara amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 111.

Wannan adadin yana nuni da yadda rashin abinci ya tsananta a cikin yankin na Gaza saboda yadda Isra’ila ta killace yankin ta hana a shigar da abinci a ciki.

A gefe daya, HKI tana ci gaba da kashe Falasdinawa ta hanyar yi musu kisan kiyashi, da a yau kadai fiye da mutane 80 ne su ka yi shahada. Mafi yawancin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’oin nan na baya suna a unguwannin Tallul-Hawa, da Deir-Balah. Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a sansanin ‘yan hijira dake Mukhayyam-Shadhi.

 Kungiyoyin kasa da kasa suna ta ci gaba da yin kira da a bude iyakokin Gaza domin a shigar da kayan abinci, sai dai babu faruwar hakan.

A cikin zirin Gaza dai, mutane suna faduwa suna  somewa, wani lokaci mutuwa saboda yunwa, ba kuma babba babu yaro.

Mafi yawancin mutanen da suke mutuwa dai kananan yara ne, jarirai da matasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ruwa da iska sun kashe mutum 5, sun raba sama da 5,000 da muhallansu a Yobe
  • Ruwa da iska sun kashe mutum, sun raba sama da 5,000 da muhallansu a Yobe
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace
  • Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid A Borno
  • A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
  • Har Yanzu Yaƙi Da Ta’addanci Ne Babban Muradin Gwamnatina — Tinubu
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin
  • Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne