Ma’aunin Farashin Kayan Masarufi Na Watan Mayu A Kasar Sin Ya Ragu Da Kaso 0.1 Bisa Dari
Published: 9th, June 2025 GMT
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 9 ga wata sun nuna cewa, a watan Mayun bana, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, watau CPI na kasar, ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma farashin makamashi ya zama babban dalilin da ya haifar da raguwar.
Duk da cewa ma’aunin CPI na watan Mayu ya ragu kadan, amma farashin kayayyaki a wasu bangarori ya canza, al’amarin da ya shaida rawar da manufofin ingiza harkokin saye da sayarwa ke takawa.
Kazalika, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, a farkon watanni biyar na shekarar da muke ciki, jimillar darajar hajojin da aka yi shige da ficensu a kasar Sin ta kai Yuan tiriliyan 17.94, adadin da ya karu da kaso 2.5 cikin dari, bisa na makamancin lokacin bara, wanda ya ci gaba da karuwa. Kana, jimillar cinikayyar da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta kai matsayin koli a tarihi, inda jimillar hajojin da kasar Sin ta yi shige da ficensu a tsakaninta da kasashen Afirka, ta kai Yuan biliyan 963.21, adadin da ya karu da kaso 12.4 cikin dari, wanda ya dauki kaso 5.4 cikin dari na jimillar darajar hajojin da kasar Sin ta yi shige da ficensu. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ya ragu da kaso a kasar Sin ta
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa
Kasar Sin ta bukaci Japan da ta daina yi wa masu fafutukar neman “‘Yancin kan Taiwan”, ingiza mai kantu ruwa, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun ya bayyana a yau Laraba.
An ruwaito cewa, gwamnatin Japan a ranar Talata ta ba da wata lambar girmamawa ga tsohon “wakilin Taiwan a Japan” Hsieh Chang-ting.
A martanin da ya mayar game da hakan a wani taron manema labarai, mai magana da yawun ma’aikatar Guo Jiakun ya ce, kasar Sin tana matukar adawa da matakin gwamnatin Japan na ba da lambar girmamawa ga wadanda ke fafutukar “‘yancin kai na Taiwan” kuma yin hakan wani babban kuskure ne da bangaren Japan ke yunkurin tafkawa kan batun da ya shafi yankin Taiwan na kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA