Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja
Published: 4th, June 2025 GMT
Jami’an hukumar tsaro ta DSS da na rundunar sojojin Najeriya sun ce sun hallaka ’yan bindiga akalla 45 a kusa da garin Kuchi da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.
An dai sami nasarar ce sakamakon wani harin da dakarun suka kai cikin sirri a ci gaba da yakin da suke yi da ’yan bindiga a yankin.
Majiyoyi daga cikin jami’an tsaro sun bayyana cewa jami’an DSS sun bi sahun wasu ’yan bindiga ne inda suka dakile yunkurinsu na kai munanan hare-hare, wanda kasurgumin dan bindigar nan, Dogo Gide da yaransa suka shirya kai wa.
Majiyar ta ce bayanan sirrin da hukumar ta tattara sun nuna yadda ’yan bindigar wadanda suka yi sansani a dajin Bilbis da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara da ma wasu sassan jihar Kaduna, Dogo Giden ne ya gayyace su domin su kai hari yankin na Kuchi.
A cewar amjiyar, “Da sanyin safiyar Litinin, biyu ga watan Yunin 2025, ’yan bindiga wajen su 100 daga kauyukan Kaduna da Zamfara da ke dauke da muggan makamai suka tunkari garin Kuchi na karamar hukumar Munya a jihar Neja.
“To sai dai jami’an tsaro sun yi musu kwanton bauna a wajen garin na Kuchi. Lamarin dai ya kai ga musayar wuta, inda aka kasha da dama daga cikin maharan sannan aka raunata wasu, aka kwace Babura da makamansu. Sai dai rahotanni sun nuna cewa wasu jami’an DSS su biyar sun ji rauni kuma yanzu haka suna asibiti.”
Majiyar ta ce harin wanda ya biyo bayan wani kisa da aka yi wa ’yan bindigar su 50 ya yi wa Dogo Giden mummunar barna.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Buni ya bai wa manoma 1,000 tallafin aikin gona
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya raba kayayyakin noma ga magidanta 1,000 da suka hada da ‘yan gudun hijira daga Mandunari da ke karamar hukumar Gujba da sauran al’ummomin da suke zaune a yankin.
Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke Damaturu, Buni ya bayyana cewa, duk da cewa al’ummomin Mandunari ya kasance su ne yankin al’umma guda daya tilo a jihar Yobe da har yanzu ba a sake tsugunar da su ba, al’ummarta sun nuna jajircewarsu na komawa gidajen kakanninsu.
Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ilaYa kuma jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da dawowar duk ‘yan gudun hijira lafiya, tare da tallafa musu ta hanyar saka hannun jari a ayyukan more rayuwa, tsaro, gidaje, kiwon lafiya, da ilimi.
Kayayyakin da aka bada tallafi ga manoman sun hada da ingantattun kayayyakin yin noma da irin masara, kubewa, gyada, gero, da irin shinkafa, taki, maganin kashe kwari da na ciyawa da makamantansu.
“A lokacin rani, manoma za su sami famfunan ruwa da ingantattun irin albasa, tumatir, kabeji, latas, da barkono.
“Gwamnatin jihar Yobe ta riga ta zuba jarin sama da dala biliyan 4 a ayyukan noma a fadin al’ummomi 178 na mazabun Jihar, inda ta samar da taraktoci, takin zamani, da sauran kayan masarufi don bunkasa samar da abinci,” inji gwamnan.
Ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar hukumar raya kasa da hadin gwiwar kasar Switzerland za ta tallafa wa karin magidanta 2,000 da kayan noma da kiwo a Gaidam, Tarmuwa, da Damaturu.
Buni ya kara da cewa, kananan manoma za su kuma samu horo kan noma da kiwo da sauyin yanayi, yayin da a karkashin shirin samar da mafita mai dorewa manoma 1,000 da ma’aikatar kula da kiwon lafiya ta horas da su za su samu kananan tallafi don ci gaba da rayuwarsu.
“Muna ci gaba da jajircewa wajen ganin ba a bar wata al’umma a baya ba, duk wanda ya rasa matsugunai ya cancanci a ba shi dama mai kyau don sake gina rayuwarsu cikin aminci da mutunci,” in ji gwamnan.