Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Halarci Taron Ministocin Kula Da Matakan Taron FOCAC Da Bikin Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Afirka Karo Na 4
Published: 6th, June 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar a yau Jumma’a cewa, daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Yuni, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, zai halarci taron ministoci masu bibiyar aiwatar da matakan da aka dauka na taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), gami da bikin bude baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da Afirka karo na hudu a birnin Changsha na lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp