HausaTv:
2025-07-23@23:51:56 GMT

Maniyyata na hawan Arfa a kasar Saudiyya

Published: 5th, June 2025 GMT

Yau Alhamis 9 ga watan Zul Hijja, ita ce ranar da miliyoyin Musulmi da ke aikin Hajji a kasar Saudiyya ke hawan Arfa, wato daya daga cikin shika- shikan aikin Hajji.

Maniyyata kusan miliyan biyu daga fadin duniya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin, wanda ya kunshi dawafi da zaman Mina da tsayuwar ta Arfa da kuma jifar shaidan.

A washegarin ranar ne kuma sauran Musulmai a duk fadin duniya su ke shagulgulan Sallar layya.

Hukumar lura da aikin hajji ta Saudiyya ta ce yanayin zafi zai kai maki 45 a kwanakin da ake tsaka da aikin na hajji.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar

Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen inganta ci gaban zamantakewar al’umma da kuma tallafawa aiwatar da Muradun Cigaba mai Dorewa (SDGs).

Hajiya Amina Mohammed ta kai ziyara Jihar Kano ne domin yin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar fitattun dattawan nan  biyu, wato Alhaji Aminu Alhassan Dantata da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A yayin ziyarar tata, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna gamsuwa da wasu daga cikin shirye-shiryen Gwamna Yusuf na cigaban al’umma, musamman wadanda suka yi daidai da muradun ci gaban duniya.

Daga cikin wadannan shirye-shirye akwai sanya fitilu masu amfani da hasken rana a titunan Kano, kafa cibiyar kula da cututtuka ta Kano (Kano Centre for Disease Control), wadda ita ce irinta ta farko da wata gwamnati ta jiha ta kafa a Najeriya, da kuma kokarin fadada tsarin inshorar lafiya domin al’ummar jihar su amfana.

Ta kuma yaba da kirkirar Ma’aikatar Wutar Lantarki da Makamashi, tare da sake tsara Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, wanda dukkansu ke nuni da jajircewar gwamnati wajen daukar matakan kare muhalli da dorewar ci gaba.

Hajiya Mohammed ta bayyana cewa ziyarar tata ba wai kawai domin ta’aziyya ba ce, har da zurfafa wayar da kai kan Muradun Ci Gaba Mai Dorewa, da kuma karfafa hadin gwiwa da jihar Kano.

Ta sanar da gwamnan game da babban taron Kasuwanci da Zuba Jari na Majalisar Dinkin Duniya da ke tafe, tare da nuna godiya bisa dagewarsa wajen karfafa mata, samar da ayyukan yi, da kare muhalli.

A nasa jawabin , Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa a shirye jiharsa take ta hada gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya musamman a fannonin ilimi, lafiya, sauyin yanayi, samar da makamashi, kare muhalli da kuma zuba jari mai dorewa.

Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaba da za su inganta rayuwar al’ummar Kano da kuma bada gudunmawa ga kokarin ci gaban duniya.

 

 

Abdullahi Jalaluddeen

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
  •  Fiye Da  Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki
  • Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma’a – Gwamnati
  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
  • Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana
  • Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa
  • Asibitin ATBUTH za ta fara gwajin rigakafin zazzaɓin Lassa
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
  • Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin
  • Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar