Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Fursunoni 59,786 Rijistar NIN A Faɗin Nijeriya
Published: 8th, June 2025 GMT
Jimillar fursunoni: 80,879
Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256
Kashi na rijista da aka kammala: 74%
Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki.
Hukumar ta bayyana wannan aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin dijital, da sake gyaran rayuwa, da shigar da fursunoni cikin tsarin ƙasa.
Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanansu daga hukumomin da suka dace kafin wallafawa domin kaucewa yaɗa bayanan da za su iya dagula fahimtar jama’a ko rage ƙwarin gwuiwar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An wajabta wa ɗaliban firamare mallakar lambar NIN a Bauchi
An wajabta wa ɗaliban makarantun firamare da Ƙaramar Sakandare mallakar lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) a Jihar Bauchi.
Hukumar Kula da Ilimin Bai-ɗaya a Matakin Farko ta jihar (SUBEB) ce ta bayar da umarnin ta hannun shugabanta, Alhaji Adamu Mohammed Duguri.
Ya bayyana cewa mallakar lambar NIN ta zama tilas lura da duk hukumomin shirya jarabawa da manyan makarantu suna amfani da ita kafin yi wa ɗalibai rajista.
Ya umarci shugabannin makarantun firamare da sakandare da su umarci ɗalibansu da su tabbata sun yi rajistar katin shaidar ɗan ƙasa sun mallaki lambar NIN kafin shekarar da za su zana jarabawar kammala makarantar da suke.
NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa A tsananta hukunci kan masu dukan mata — Sarki SanusiHaka zalika ya buƙaci da su tabbatar ’ya’yansu sun mallaki lambar NIN kafin su kai aji 6 na firamare zuwa aji 3 na Ƙaramar Sakandare domin guje wa makara.
Haka kuma ya umarci Sakatarorin Ilimi na ƙananan hukumomin jihar su tabbatar an bi wannan umarni sau da ƙafa domin guje wa fafar hira a ranar tafiya.