Sojoji sun kashe manyan Kwamandojin ISWAP 3 a Borno
Published: 6th, June 2025 GMT
Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da ke samun goyon bayan sojojin sama Air Component sun kashe wasu manyan kwamandojin Kungiyar ISWAP guda uku.
Rundunar ta kashe kwamandojin ne a harin ta’addanci da ba a yi nasara ba a kan Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam a Jihar Borno.
Sallah: Gwamna Inuwa ya yi kiran sadaukarwa da haɗin kai Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APCWata majiya mai tushe daga jami’an rundunar ta OPHK ta tabbatar a ranar Alhamis din nan cewa, kwamandojin da aka bayyana sunayensu: Amir Abu Ali Weldone da Amir Ibunu da Amir Abu Waldume, na daga cikin wadanda aka kashe a harin da aka kwashe sa’o’i hudu ana yi a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Mallam Fatori.
A cewar majiyoyin, kwamandojin da aka kashe sun taka rawar gani wajen gudanar da ayyukan Kungiyar ISWAP, inda ake kyautata zaton Abu Ali Wadume ne ke jagorantar ayyukan ta’addanci a yankin Kerenoa kusa da kan iyakar Najeriya da Nijar.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa, ‘yan ta’addan sun kaddamar da harin hadin gwiwa ne daga yankin Kaniram da sanyin safiyar Laraba, inda suka afkawa sojoji.
Mayakan ISWAP sun yi amfani da manyan makaman yaki hade da jirage marasa matuki ciki har da makamin (AGLs), amma sun gamu da turjiya daga sojojin kasa na rundunar ta OPHK da goyan bayan manyan makaman yaki da suka hada da tankokin yaki da suka rika amfani da su babu kakkautawa.
Majiyar na cewar sojojin sun samu nasarar dakile harin bayan kazamin fadan da ya tilastawa maharan ja da baya cikin rudani a gaggauce.
Rahoton na cewar, akalla ‘yan tada kayar baya 12 ne aka tabbatar da mutuwarsu, tare da kwato bindigogin AK-47 guda bakwai, manyan bindigogi guda uku samfurin (GPMGs), da makaman roka guda biyu (RPGs), da wasu bama-bamai.
“Har yanzu ana ci gaba kididdige barnar da aka yi wa ‘yan ta’addan, amma an tabbatar da kashe wadannan manyan kwamandojin guda uku da aka ambata sunayensu wanda kuwa hakan babbar nasara ce tga kokarin da mayakan sojojin Najeriya ke samu akan ‘yan ta’addan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kungiyar ISWAP
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin
Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuradiyya a kasar.
Majalisar ta kuma ce tana goyon bayan matakin da shugaban ya ɗauka kwanaki kafin haka domin hana yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya a makwabciyar kasar.
Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashentaBukatar dai na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisa yayin zamanta.
Tinubu ya umarci tura sojojin makon da ya gabata domin dakile yunƙurin karɓar mulki ba bisa ka’ida ba a Jamhuriyar Benin da kuma kaucewa rikicewar tsaro a yankin yammacin Afirka.
Sai dai Tinubu bai nemi amincewar majalisa ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Bayan karanta wasiƙar, majalisar ta koma zaman kwamiti domin tantance bukatar. A yayin zaman, ’yan majalisa sun tattauna kan tasirin tsaro, jin‑ƙai da diflomasiyya da ke tattare da wannan mataki.
Babbar damuwar a cewarsu ta haɗa da yiwuwar kwararar ’yan gudun hijira zuwa Najeriya, tsaron iyaka da kuma tasirin matakin ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
Bayan doguwar muhawara, majalisar ta koma zama a zaurenta, inda ta kada kuri’ar amincewa da matakin shugaban ƙasa cikin rinjaye.
Shugaban Majalisar, Akpabio, ya gabatar da rahoton kwamitin domin tabbatarwa, inda ’yan majalisa suka amince ba tare da wata adawa ba kafin su amince da tura sojojin ta hanyar kada kuri’ar murya karo na biyu.
A jawabin sa, Akpabio ya yabawa Shugaba Tinubu bisa ɗaukar matakan da suka tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma bin ka’idojin kundin tsarin mulki ta hanyar neman amincewar majalisa, ko da bayan tura sojojin cikin gaggawa.
“Wannan mataki ne da ya zama dole. Shugaban Ƙasa ya yi aiki ne domin kare tsaron ƙasa da kuma kare dimokuraɗiyya a yammacin Afirka. Barazana ga kasa ɗaya barazana ce ga kowa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa za a isar da kudurin majalisar ga Shugaban Ƙasa nan take.