He Lifeng Zai Ziyarci Birtaniya Tare Da Halartar Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka
Published: 9th, June 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ta sanar a jiya Asabar cewa bisa gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta yi masa, memba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, zai ziyarci Birtaniya tun daga yau Lahadi har zuwa Juma’a 13 ga watan nan na Yuni.
Ana sa ran yayin ziyarar tasa a Birtaniya, He Lifeng zai halarci taron farko na tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi
Ƙungiyar Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi a matsayin mai horas da ’yan wasanta bayan raba da gari da ƙungiyar Pisa wadda ya kafa tarihin jagorantar haurowarta gasar Serie A.
Cikin wata sanarwa da Palermo ta fitar ta ce Inzaghi ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru da dama wanda zai soma aiki daga watan gobe.
Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi Jirgin alhazai ya yi saukar gaggawa kan barazanar harin bomA cewar kafofin watsa labarai na Italiya, Palermo ta biya Pisa kusan dala miliyan 1.1 wajen ɗaukar Inzaghi.
Pisa dai ta ƙare gasar Serie B a mataki na biyu a ƙarƙashin jagorancin kociyan mai shekaru 51, lamarin da ya ba ta nasarar haurowa gasar Serie A karon farko a cikin shekaru 34.
Pisa ta samu gurbi a gasar Serie A bayan samun nasara a wasannin sharar fage da ta buga da Cremonese da kum Sassuolo.
Sabuwar ƙungiyar Inzaghi wato Palermo ta dai ƙare ne a mataki na takwas, kuma ta sha ƙasa a zagayen farko na wasannin sharar fage a hannun Juve Stabia.
AFP