Kungiyar RSF da kawayenta na shirin kafa gwamnatin ‘yan tawaye a Sudan
Published: 24th, February 2025 GMT
Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba.
Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga kowane al’adu, kabila, addini, ko yanki ba.
Gwamnatin da aka gabatar na shirin magance gibin ayyuka a yankunan RSF a cewar Alaa El-Din Nuqd, wanda ya jaddada cewa “An katse al’ummar wadannan yankuna daga muhimman ayyuka kamar sabbin takardun kudi da sojoji suka fitar, sarrafa fasfo, da sabunta takardu,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto.
Mai magana da yawun rundunar RSF Najm al-Din Drisa ya ce za a iya kafa sabuwar gwamnati nan da wata guda.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Baje Kolin Kayakin Da Ake Kerawa A Iran Tare Da Taron Iran Da Afirka Karo Na Uku
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar.
EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan daga nan take samun kasuwa a kasashen duniya. Kuma yan kasuwa daga kasahe fiya da 100 ne suka shigo kasar don halattan kasuwar.
Esma’il Bakaee, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce ya na fatan a wannan kasuwar, kasashen Afirka da Iran za su amfani juna a harkokin kasuwancin da ake bunkasa a tsakaninsu.