Sallah: Gwamnatin Sakkwato ta bai wa kowane Alhaji kyautar N450,000
Published: 8th, June 2025 GMT
Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya bai wa alhazan jihar su 3,200 kyautar Riyal 1,000 na Saudiyya (kimanin Naira 450,000) a matsayin barka da sallah.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya kai wa alhazan ziyara a Minna.
Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Mutum 9 sun rasu a hatsarin mota a JigawaYa taya su murna bisa kammala aikin Hajji lafiya, inda ya ce wannan kyauta ce domin tallafa musu kafin su dawo gida Najeriya.
Gwamna Aliyu, ya yaba da yadda alhazan suka kiyaye doka da oda a ƙasa mai tsarki, inda ya ce sun wakilci Jihar Sakkwato cikin ƙwarewa da girmamawa.
Ya kuma gode musu bisa ladabi da haƙuri da suka nuna yayin gudanar da ibadar Hajji.
Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da jin daɗin al’ummar jihar, musamman mahajjata.
Haka kuma, ya jinjina wa ƙoƙarin Amirul Hajj na jihar, Alhaji Ummarun Kwabo, da kuma Hukumar Alhazai ta jihar bisa jajircewarsu wajen tsara Hajjin bana cikin nasara.
Gwamnan, ya kuma roƙi alhazan da su ƙara yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da tsaro a Najeriya.
Ya ce duk da irin ƙoƙarin da ake yi wajen magance matsalolin tsaro, addu’a ita ce mafi tasiri wajen kawo ƙarshen matsalar da ke hana ci gaban ƙasa.
A yayin ziyarar, Gwamna Aliyu, ya jajanta wa akhazai daga ƙananan hukumomin Gudu da Shagari bisa rasuwar Hajiya Hadiza da Bala Jangebe a lokacin aikin Hajji.
Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta musu kuma Ya bai wa iyalansu haƙuri rashinsu.
A nasa jawabin, Amirul Hajji, Alhaji Ummarun Kwabo, ya gode wa gwamnan bisa goyon bayansa, wanda ya ce shi ne ya taimaka wajen samun nasarar aikin Hajjin bana.
Ya ƙara da cewa dukkanin kwamitocin da aka kafa sun yi aiki tuƙuru don ganin komai ya tafi lafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barka Da Sallah Gwamna Ahmed kyauta Sakkwato Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.
Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.
A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.
Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp